← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 102

Sashe 9

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

iya ri e min amana,bayan haka sace-sace suke min." Duk maganganun da take yi ba ta ce mata komai ba,aranta ta na tunanin karta amince a za a sami matsala da Baba Sani duk da shi ma ya na da laifi,in da ace ya na taimaka musu da ba za ta yi aiki ba. 'Ki na ji Mama da ban so na gaya miki wani sirrina ba,amma nuna amincewar ki ya zama dole na sanar miki domin ki taimakeni ki ceci aurena.Mai aikina mijina ya kama ta da yarana tana basu kirjinta suna tsotsa ita kuma ta na saka musu hannu a gabansu.Hankalinsa ya tashi warai ba yan ya mi a ta ga hukuma ya kawo su asibitin da nake aiki,hankalina ya tashi warai na yi kuka kuma mun yi rikici da shi daga ba ya yace dole na bar aiki ko mu rabu.Ina son aikina saboda da shi nake taimaka iyayena,sannan ina son aurena na yi-na yi a dai na saka ni aikin kwana amma ba zai yiwu ba. Mijina ya bani za in na bar aiki na kula mishi da yaransa ko ya rabu da ni,domin ya i barin na ara aukar me aiki.Mun yi rikici da shi sosai daga baya ya ha ura na samu mai aiki amma daga wannan ya kama ta da wani matsala zai rabu da ni."Tace cikin hawaye ta ja numfashi sannan ta ora da cewa. "Mariya ita ta ja ra'ayina akan Juwairiya saboda ta gaya min ta na da hankali,da yar na ami nce da na ganta na yadda da maganar Mariya ki taimake ni Mama in har kika amince zan zama tamkar arki,zan taimaka ma rayuwar ku." Jikin Mama ya yi sanyi sosai har ba ta san sanda ta amince ba jin aure na shirin mutuwa,duk da watarana ita ma aure za ta yi."Na amince Allah ya kyuata amma ar nan ya kamata ku din ga kiyaye wa,ni ma matsalar ba daga gareni ba ne a kwai anin mahaifinta ba lai-lai ba ne ya amince amma ta fara mu gani." Sosai ta ji da i ta bu e jakarta ta ciro dubu ishirin da biyar tace."Ga ku in ta na wata biyu dubu ishirin sai ki fara koda sana'a ne,sannan dubu biyar na baki kyauta kuma gobe in Allah ya sa tazo za ta taho da tsa Mama ta ji da in ku in da ta bata ta na ta murna da saka mata albarka har ta yi mata sallama,ta kama hannun Juwairiya tace."Sis sai kin zo gobe ko?Don Allah ki zo da wuri anninki suna ta maganarki."Tace tare da shafa kanta. "Gaskiya ta na da kirki sosai."Mama tace ta na juya ku in da ta bata,sai kuma ta aje ku in ta kalleta tace "Kin san me ba zan ta a ku in nan ba sai mun ji me Baban ku Sani zai ce."Da sauri ta mi e kawai ta na fa in."Ki ba ni naje na yo miki sare-sare ki fara sana'a ni fa ko me zai yi sana yi aikin nan,tunna shi ba taimakon mu yake yi ba don haka ba shi hurumin da zai hana mu." Ta yi maza ta fice daga akin kafin Mama tace komai sam ba ta jin tsoron abin da zai ce in dai ba kasheta zai yi ba ta rantse sai ta yi aikin. Kamar yadda ta gaya mata mijinta ba mazauni bane haka kuwa ta gani,don tun da ta fara aiki ba ta gan shi ba sai tan amemen hoton su da yake manne a falon wanda tun da taje ranar da Mariya ta kaita ta gan shi a hoto,wannan dalilin ya sa hankalin ta ya kwanta ko da ta ga Baba me aiki aikin ta take yi ta tafi ba ta kwana. Ta na aikin ta cikin kwanciyar hankali ga abinci da take ci kullum taci mai kyau ta sha mai kyau,don Anty Naja ba ta da rowa ko nama taci sai ta rage mata saboda yadda Juwairiya take kula da yaranta ga ta da tsafta ko ina na gidanta tsaf ya na tashin amshi. Kusan sati biyu ta na aiki cikin jin da i kuma har zuwa wannan lokacin Baba Sani be dawo ba,kullum in dai za ta dawo Anty Naja na sawa a yi girki da su ta saka mata a kula kuma da yawa,don haka ba sa matsalar abinci ga anye da take badawa a kai ma Mama in dai za ta yi aikin kwana. Ranar Juma'a da safe bayan ta gama aikin ta ta shirya musu abincin karyawa ta ibi nasu kamar yadda ta yi mata umurni,kasancewar ta gama aikin kwana za ta yi hutu har ta bawa Juwairiya hutun kwana biyu. A hanya Juwariya ta na tafe ta na ta yi mata addu'a don tsakanin su Allah ne kawai zai biya ta,saboda irin kyautata mata da take yi fara aikin ta ta bata kaya masu kyau sosai da abin alheri ko hijabi kala biyar ta bata,sannan ko ba i ta yi bata ce mata me aiki sai dai tace ar'uwanta ta na da matu ar kirki sam bata nuna wani abu ko rashin mutunci. A dai-dai ofar gidan su ta tsaya cikin firgici ganin Baba Sani ya are kan motar sa ya na ri e da atuwar bulala,sai juya ta yake ya na zare ido ransa a ace da ga ganin yadda ya aure fuska alamun ba mutunci. Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu ha u a shafi na bakwai.Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. *FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE* *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_
Chapter 9 · 0% Book details