Sashe 2
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *SHAFI NA BIYU* Da sauri Juwairiya ta dawo ta rungumshi da hannunta aya, ayan kuma ta na shafa mishi ruwa, ajiyan zuciya ta sauke mai arfi ganin ya bu e ido,don hankalin su ya tashi ma ura gani suke kamar mutuwa zai yi ganin yadda idanunsa suka afe. Juwariya ta mi e ta na fa in."Tun da ya farfa o bari na je na naimo mishi magani."Mi ewa ta yi ba ta jira amsar da Mama zata ba ta ba ta fice da ga cikin gidan ta na sharar hawaye. A hankali ta arasa shiga cikin shagon na sa ganin yadda ya ha e rai tun da ya hangeta ta na tahowa,tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa ya ha e ransa babu wani walwala.Jikin ta ya yi sanyi sai ta tsaya a bakin ofar ta kasa mishi magana kuma ta i ta tafi duk da kallon kora da hali yake mata. "Lafiya ki ka yi min tsaye kofar shago kamar na saki ki?Ya fa a ransa a ace"Don Allah ka taimake ni Bala kasan mai ya kawo ni a karo na biyu,wallahi suna cikin wani hali na rantse maka wannan karon zan naimi ku in ka na baka."Ta fa a da muryar kuka fuskarta bayyane da damuwar halin da take ciki. "Ni ina ruwana na gaji da baki bashi kuma ba kawo min kike ba,sannan na nuna miki hanyar da zaki bi mafi ulluwa kin nuna a'a wai ke ustaziya,to sai kije can amma ko maganin biyar ba zan baki ba."Tamkar zai kai mata duka yake magana ganin haka sai kawai ta juya,dan ta saka a ranta yau bazai bata ba. "A'a Juwairiya tafiya zaki yi."Ya fa a da sanyin murya ganin ta kama hanyar fita,sai kuma ya ara matso da fuskarsa gurin ta yace."Kin cika kafiya ki yadda ki amince ko sau aya ne,Allah zan baki duk abinda kike so.Kin san ina son ki Juwairiya na san babu yadda za'ai na same ki,wannna dalilin ya sa nake so ki amince min kar soyayyata ta fa i a banza." arashe fita ta yi da ga shagon dan abin da yake so bazai samu ba.Mahaifiyarta kullum ta na mata nasihar ta tsare kanta da ga aikata zunubi mai girma wanda Allah yake fushi da wanda ya aikata,kuma ya yi hani ga bayinsa muminai na warai. Gidan awarta Mariya ta wuce ta same ta zaune akan tabarma a cikin falo ta na gugan kayan ta da dutsen guga na gawayi,sallama kawai ta yi ta zauna a kan tabarma ji take kamar zatai hauka."Juwairiya lafiya kike mai ya faru?"Mariya ta jera mata tambayoyin da ta kasa ba ta amsa ba,sai ta janye hannunta da Mariya ta kama tare da share hawayen da ya gangaro mata. Mariya ta arashe share mata sauran hawayen ji take ita ma kamar ta saka kuka,ta ago idanunta da suka ka a suka yi ja ganin awar ta ta na kuka tace."Ki yi min magana Juwariya!Kin san ba na jure ganin ki a cikin wannan hali,abin da ya sa na i dawowa kin san halin Baba Sani na rasa yadda akai ya takurawa rayuwar ki baya son kowa ya ra e ki,dan haushin koron da yake yi nake ji irin kullen da yake miki ko fa yaran sa baya yi mawa,lamarin sa akwai ayar tambaya ,dan ina tunanin akwai lauje cikin na i!"Ta ja fasali ta na kallon Juwairiya da kukan ta ya tsananta,tuna yadda ya tsane ta yake azabtar da rayuwarta.Mariya ta ci gaba da magana cikin acin rai ta na cewa. "Ina jin takaicin halin da kike ciki amma ki sani bawa bai isa ya canza ma wani rayuwar sa ba,kin ga da Baba Sani baya miki kulle sai na sama miki aikatau ni bashi nake yi ba hankalina kwance. Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya duk da ba in cikin da take ji na in barta ta yi aikatau,wanda mahaifinta ma ya amince amma ememe ya hana ta da ta na yi ila da basu shiga cikin u ubar rayuwa ba,gashi tun da ta gama sakandiri ya hana ta karatu amma yaran sa duk sun yi. Duk da lamarin na ci mata tuwo a warya amma ba ta ce ala ba,sai dai zuciyar ta cinkushe take da damuwa tare da tunani iri-iri. Mikewa Mariya ta yi ta shiga kicin ta zuba tuwo da miyar ku ewa ta kawo mata ta na fa in."Gashi tun azu na so na kawo muku amma ina tunanin wannan Baban naki,kuma Auwal tun da ya tafi islamiya bai dawo ba balle na bashi ya kawo miki."Ta mi a mata tare da kwance ullin zaninta ta ciro naira ari biyu ta mi a mata. Tsabar murna sai kawai ta rungumeta tare da fashewa da kukan murna,Mariya na taimakon ta warai ta na fatan Allah ya bata ta taimaka mata. Rako ta ta yi ta siya magani sannan ta kaita dai-dai kwanar lungun gidansu.Da sauri Mariya ta saki hannunta ta na fa in."Na shiga uku wallahi gashi nan duk da in kaiki gida da na yi amma ya na nan ya na sa ido ya san ki fita,ke Juwairiya wannan ko mijin ki ne sai haka."Ta ruga da gudu har ta na tuntu e bayan ta gama maganar don Allah ya saka mata tsoron shi,bashi da mutunci in dai akan Juwairiya ne. Juwairiya da jikinta ya fara rawa ji ta yi kamar asa baza ta iya aukar halintar ta ba,ta tsorata iya tsorata zabura ta yi kamar zata ruga sai kuma ta fasa ta na karanta wallahu galibun ala amrih ganin ya tunkaro ta. araso ya na mata wani irin kallo da shi ka ai yasan ma'anarsa."Ina kika je?"Ya tambayeta da murya kakkausa tare da saka afafunsa ya take mata 'yan yatsun kafar,ta rintse ido ta na jin wani iri madarar azaba ya na taso wa daga kan 'yan yatsun na ta ya na zagaye ilahirin jikinta,taso ta matsa domin akoda yaushe ya tsaya kusa da ita ta na alubantar yadda yake matsowa daf da jikinta.Amma hakan ya ci tura ganin yadda ya take kafarta ya hana motsinta. "Bana hana ki yawon maula da uwarki ta koya miki,bayan Yayana bai rage ku da komai ba."Ya fa a ya na ara kusanci da ita fiye da na azu. "Don Allah kayi ha uri bani ta yi wallahi ban ro e ta ba,kuma Ibrahim zan bawa."Tace yayin da ta i sha ar numfashi ba ta son ta sha i iskar hucin bakin sa da take jin sa a fuskarta.Ya a ga kafafun na ta ya na are mata kallo hakan ya bata damar shirin arcewa ko takalminta bata auka ba,dan ya zame lokacin da ya take afarta. Da gudu ta ruga amma sai ta fa asa yayin da miyar tuwon ya zube,amma duk da zafin da take ji bai saka ta yadda tuwon ya zube ba,ta zabura ta mi e hanyar gida dai dai sanda ta ji ya na fa in."Ni da kene a duniyar na baza ki ta a jin da i ba matu ar ina raye,haka kawai na yi sakaci har tunanina ya faru mu zu ba mu gani Juwairiya na shiga cikin aki ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,a ranta ta na jin ba in cikin halinsa bata san mai ta tsare mishi ba,amma ya saka ma rayuwarta ahon zu Koda ta shigo Mama ba tace komai ba har ta sha kukanta ta oshi don tasan mai ya faru,tunna babu abin da za ta iya shi yasa bata tanka mata ba,sai ta jawo kwanon tuwon ta ba Ibrahim sannan ta bashi magani ragowar taci ta ragewa Juwairiya duk da babu miya kuma ta ji asa- asa a tuwon. Bayan ta gama kukan taji sanyi a zuciyar ta dama kukan shi ke sanyaya mata zuciya,duk lokacin da ya yi mata hakan don babu wanda yake ko tari a cikin iyayenta,su kansu tsoron sa suke yi duk da mahaifinta shine babba. ewa ta yi ta auro alwala ta yi magariba sai ta yi zamanta ta na jan carbi yayin da hawaye ke zuba fuskarta,wani gefe na zuciyarta ta na hasaso mata lamura sosai game da Baba Sani. Baba Sani ya yi tsaye a gurin bayan tafiyar ta ya na tunani sannan ya arasa dakalin ofar gidan ya zauna ya na gadin masu zuwa gurinta,ko da ka kira sallar isha'i ya yi sannan ya dawo ofar gidan ya ci gaba da gadin gurin. Sai misalin tara na dare mahaifin Juwairiya ya yi sallama ya shigo da ullin leda mai auke da garin rogo gwangwani biyu da siga.Mama ce ta amsa sallamar ta arbi ledan tare da shinfi a mashi tabarma,lokacin har baccin wahala ya fara aukar ta don yunwa take ji matu a kuma kamar zazza i yake son kama ta. Jin sallamar ya sa ta bu e idanu ganin leda a hannun Mama ya sa ta mi e tare da arban ledar bayan ta yi mishi sannu da zuwa ta fice dan ta ji a garin.Ya kalli Ibrahim dake kwance ya na bacci ya shafa fuskarsa ya na fa in." Ya jikinsa?Ina can amma hankalina ya na nan kin san jiya afarsa ta bani tsoro."Yace ya na lasar bushashshen bakinsa dan rabon sa da abinci tun jiya da yamma da suka girka taliya leda aya gashi ya wuni ya na faskare. "Da sauki amma ya kama ta a maida shi asibiti gaskiya,yau ya bani tsoro ina ki kamar zan rasa Ibrahim saboda halin talaucin da muke ciki."Tace sai kuma ta rushe da kuka ta na fyace majina. A sanyaye Juwairiya ta ije garin da ta ji a ganin Mama ta na kuka ta koma gefe ta zauna ta na jin zafin Baba Sani dan ita gani take shi ya takurawa rayuwarsu da ya hana ta naimi aiki,in da ace ta na aiki rayuwar su ba ta yi muni haka ba,ga Mariya da take aikin suna jin da i kuma matar ta na taimaka musu. "Ki bar kuka dan Allah da kin san halin da na wuni da kin tausaya min!Na dage tu uru ina faskare sai da na gama Malam Aminu yace bashi da ku i sai gobe,da yar na samu ya bani naira ari biyu wai shima kwana biyu ba cinikin iccen. Shuru sukai cikin jimamin