Sashe 31
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 15* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM A karo na biyu ta ara gwalalo idanunta." Ina hakan ba zai ta a yuwu ba!Gara na rayu a cikin talauci na kuma mutu a cikin sa.Anya ya san me yake fa i kuwa. Sai kawai ta nufi hanyar fita ba tare da tace mishi komai ba. Juwairaah!" Ya kira sunan ta da sauri tare ofar ya kama hannunta wani irin hajijiya ya kama ta wani abu mai kama da shokin,ya na zagaye jikinta yayin da yake fitowa daga gurin da ya ri e ta ya na ara wutar sonsa a cikin zuciyar ta. " Don Allah ka cika ni ba zan iya abin da kake fa i ba,hakan ya tabbatar min da ka tsane ni ba ka son ganin farin cikina dama na san ni ba'a sa'ar auren ka ba ne, to amma kaje ka auri mata masu aji irin matarka ta yadda za ka samu ara daga gidan ku i,ba irina wanda mahaifina ya mutu bai bar min komai ba. Ta fa a tare da fisge hannunta da sauri ya sha gabanta ya to are kofar da take son ta fice, jikinsa ya yi sanyi ganin kamar ba za ta yarda ba,amma kuma ya zama dole ya san yadda zai yi ya shawo kanta,saboda amincewar ta ne kawai zai sa ka ta jure duk wani abu da za ta gani a gidan. " Nima na so haka na sami mace mai aji kama ta, amma kin san babu wata mace mai aji wanda zan nema ta yadda da hakan.Kasancewa ta a namiji da kowa ce mace za ta yi burin samu shi ya sa na i nai mar me aji iri na, don na san ba za a kwashe dai-dai da ita ba,kuma kema fa so nake na ceci rayuwarki daga angin talaucin da kike ciki. arashe maganar da murya na salon yaudarar shi ya na son ta amince. Hawaye suka ara turereniya a fuskarta ta kalleshi da nufin ta saka wani mugun tsanar shi a cikin ranta,amma sai ta ji wani madarar son sa ya na ara shiga cikin bargon jikinta a duk sanda ta yi kuskuren ha a ido da shi. " Sai ni talaka ko?Ni da Allah bai saka min zuciya na so ba.Ko na asun talauci ya na yin tasiri a zuciya duk lokacin da ta ke son wani?Shi ya sa za ka zo ka cuci rayuwata ta a na kake son na haifa na ba wata mace na har abada?Don Allah ka fita daga cikin rayuwata na ro e ka na san ba za ka samu matsala da anin mahaifina ba,amma ni ba zan amince da mugun nufin ka a kaina ba.A yau na yi burin dama ban ta a sanin ka a cikin rayuwata ba." " Ke ya ishe ki ar talaka kawai zaki zo ki na jera min wasu maganganu kamar wani an ki!Dama ban yi miki dole ba." Ya fa a tare da kaucewa ya ba ta hanya ganin hakan ya sa ta zura da gudu za ta fita,dai-dai lokacin da Baba Sani ya yi gyaran murya."Ya kamata ka wuce abokin ka ya na jira,kawai ka nemo waliyin ka a duk sanda kake son a aura auren kar ka damu da ita ko amincewar ta" Da ido ya kalleta ya na gasgata abin da yake fa i." Kin ji da kunninki abin da kwa ayayyen anin mahaifin ki yake cewa?Don haka ina tambayar ki ne don kar ayi ba tare da yaddar ki ba kizo ki ata komai." Ya zaro waya mai kyau da tsada ya ije mata." Ga shi zan wuce na gaji da wannan kukan nan naki da kika tasa ni da shi.Fisabilillahi sai kace na zo gidan ta'aziya,duk abin da kika yanke zan kira sai ko gaya min." Ya mi a mata ku i masu yawa." Ga shi ki je ki yi ma marasa lafiya siyayya.Ina ara gaya miki aya kawai nake son ki siyar min bayan nan zaki iya auren namiji wanda ya fini,domin zan anta rayuwarki zan gina ma mahaifiyarki gida na ba su duk wani jin da i na rayuwa. Shekara aya ne fa kawai za ki yi kina ma masoyiyata aiki in ma kin sami ciki, da wuri zan auke ki daga gidan kin ga kin huta kenan,sannan ki iya takun ki ba da sani ta zan yi komai ba." Ya numfasa ya na kallon ta yadda ta yi zuru ta na kallon shi,yayin da zuciyarta ta ci gaba da bugu cikin tashin hankali. "kamar yadda na gaya miki haka za ki yi don haka ko kallona kar ki yi in dai ta na kusa da ni.Kasancewarta ba mai zaman gida ba ne kinga haka zai bamu damar aurenmu ya tafi cikin sirri." Ya ce da ita sannan ya fice ya barta a tsaye tamkar gunki sai da ta auki tsawon lokaci sannan ta yi zaman an bori a asa tare da fashewa da kuka. " Don Allah karfa ku yi min arya ku dawo fa in ba haka ba wallahi sai na nemo ku duk in da kuke don ba zan ga samu na ga rashi ba. Motar su na acewa ya ruga da gudu ya shige akinsa alokacin Juwairiya har ta mi e ta share hawayenta za ta fice." ar albarka Juwairiya zo mai ya baki." Sai kuma ya hangi damin ku in da ko ta kan shi ba ta bi ba, ai da sauri ya dafe ya na washe baki sannan ya mi a mata dubu biyar ya ce." Gashi maza ki tafi Juwairiya ya gaya miki komai ko?Ai Allah ya tarfa ma garin ki nono kin huta da auren wannan mutumin,dama an iskan tun da ya ga na ba shi auren ki ya dai na bani komai,duk da na yi ba in ciki amma ko ba komai ai na samu ta sanadin ki rayuwata za ta shiga cikin jerin masu da shi." Juwairiya ba ta ce komai ba har ta kai ofa za ta fita, sai kuma ta dawo ta ce." Ni fa ba zan aure shi ba haba Baba ka ji tausayina mana!Wallahi in..." "Rufe min baki banza shashasha!Don ma kin samu zai aure ki wallahi da bai zuba uban ku in nan ba, to ko megadin gidansa yake son ki yi masa ba zan bari ba,ai ke gaba ta kai ki ko banza a shekara aya zaki rayu cikin daula,ko banza za'a sha za i da mai o a rabu da tuwo wanda shima ba kullum ake samu ba." Da sauri ta fice jin maganar da yake mata wanda duk cin fuska ce. Juwairiya ta shiga cikin tsananin hankali tun lokacin da ta fito da ga akin Baba Sani ta kife kanta ta na wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare. Yayin da tausayin kanta ya rufe ta ganin mutumin da take matu ar so ya zo neman ta akan auren kwangila."Yanzu inna auresa shekara aya za mu yi? Shima tsakanin mu tamkar mage da era tunna matarsa ta yi katanga a tsakanin." Abin da take ta fa i a ranta kenan sai kuma ta share hawayen da damuwa cike a zuciyarta,don ta rasa yadda za ta kwatanta wannan auren da yake son su yi,amma a ranta ta udira koma me zai faru sai dai ya faru don ba za ta aure shi ba,ai gara ya barta a cikin tsananin talauci saboda in talaucin bai kashe ta ba,tsananin son da take mishi da kishin matarsa zai kai ta lahira! Ko da ta isa asibiti ba yan ta gama girki abin mamaki sai ta ga Baba Sani zaune a can,ya dage sai zuba ruwan surutu yake yi tamkar wani aku. Sai Juwairiya ta kasa shiga ta tsaya ta na kallon shi da mamaki ganin yadda yake ta magana har da dariya ga uban leda da ya siyo musu abu. Mama shiru ta yi ta na kallon shi da mamaki."Oh ikon Allah duniya juyi-juyi!" Abin da ta ce kenan cikin tsananin mamakin sa. araso mana Juwairiya kin ga har na riga ki ai daga gurin aiki sai na taho,ban san kina gida ba." A sanyaye ta shigo tare da ije abincin dai-dai lokacin da Baba Sani ya tashi tare da yi musu sallama ya tafi. Da sauri Juwairiya ta bi bayan sa ya na arin shiga motar sa ta ri e murfin motar idanunta na zubar hawaye " Ba zan aure shi ba gara ya barni a halin da muke ciki,amma ba zan yi aure ba wanda mahaifiyata ma ba'a son ta sani!Tun wuri ka mai da masa da ku in sa ni zuciyata ba irin naka ba ne!Na san mutuncina ai talauci ba hauka ba ne " Kau ya gaura mata mari " Baki da hankali kina wasa da ni ke baki san halina,ni murucin kan dutse ne! In har kika ce ba za ki yi wannan auren ba,kin ji na rantse miki Juwairiya zan iya kashe ki har da mahaifiyar ki.Don haka in baki bi umurnina ba ki kuka da kanki." Ya ja motar sa ya barta a nan tsaye cikin tashin hankali sai kawai ta rushe da kuka,sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shuru ta wanke fuskarta ta shiga cikin akin da Mama suke. " Ikon Allah abin duniya ba ya arewa kin ga abin mamaki ko.Ai addu'a takobin mumuni ne." Juwairiya ta ce."Umh Mama."Sannan ta auki filet ta zuba mata abinci. "Juwairiya bayan fitar ki likita ya zo ya ce in dawo ki je ki same shi,sannan ya ba da takadda kamar na magani ne." Ta ce cikin damuwa da murya asa- asa kai da ga ji ka san ta na cikin jinya mai tsanani. " To Mama bari na je na same shi." Ta mi a mata abincin sannan ta fita zuwa ofishin likitan. "Ok zauna" Ya ce da ita bayan ta wasa ta shigo a hankali ta zauna cikin tsoro-tsoro don ba ta san dalilin da likitan ya kira ta ba. Ga sakamakon gwajin da muka yi ma mahaifiyar ki nan gaskiya ta na cikin matsala ya kama ta a canza mata asibiti,saboda zuciyar ta ta kumbura dole a yi mata aiki. Da sauri Juwairiya ta mi e tare da zare idanun ta jin abin da likitan ya fa