Sashe 48
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 20* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM A.m har ya bu e baki zai ara magana sai kuma ya fasa,ya auki wayar sa ya haye sama ba tare da ya ara kallon aya daga cikin su ba. Juwairiya ta dafe uncinta hawaye na zarya a fuskarta da ma ta san dole watarana Zainab za ta dake,ta tun da halinta ne sai dai yadda ta ji saukar marin ta ji sam ba za ta iya auka ba,domin da ya zo neman aurenta bai gaya mata har da duka a ciki ba. Hawaye ta share ta juya ta nufi kicin saboda rashin arfin da take ji,tsayuwa ma wahala take mata don haka ba ta ara ce wa komai ba ta shige kicin Jingina ta yi da slinder na gas in kicin ta saki kuka duk da ta na jin cewar,lokaci ya yi da za ta dai na asarar hawayen a banza akan su saboda ta fahimci bayan damuwar da suke saka mata,har da na auren su da suke fa a kamar kaji su hana walwarta sukuni. yar ta samu ta kammala girkin da taimakon Baba da ta dameta da tambayar mai ke damunta,ganin ta i tanka mata sai ta kalle ta ta ce bayan ta gama kwashe abinci ta saka a kula. ar nan ya kama ta ki naimi maganin basir saboda shi yake damun ki,ji yadda kike cije baki ki na tafiya da yar." Da takaicin maganar da ta yi mata aki ta wuce ba tare da ta tanka mata ba. Tun daga wannan ranar Juwairiya ta kame kanta ba ta barin ko ha uwa da shi su yi,saboda wani irin kunyar sa da take ji kamar ta nitse in ta gan shi,don ko gyaran muryar shi ta ji sai jikinta ya kama rawa kamar za ta ruga. Kwana biyu Zainab ta takura kanta ta hana zuciyarta fita don ta faranta masa,saboda ta ga canji kwana biyu ya na wani shareta,da ta yi masa magana zai hayayya o mata kamar zai cinye ta. Sai ta danne zuciyarta ta i fita ko ina daga aiki sai gida ta na ba shi kulawa,wanda da yar ta samu ya sauko suka koma rayuwar su kamar da. Juwairiya kullum za ta yi musu abinci mai rai da lafiya su ci suna yabawa a zuci,don girkinta ya na matu ayatar da su duk da babu wanda ya ta a yabawa,amma har iba sai da suka ara ka Sai dai fa mai hali ba ya fasa halin sa Zainab a daddafe ta yi an kwanaki a gidan, wadda take jin kamar ta na gidan yari duk da irin kayan alatun dake gidan amma saboda ta saba fita sam komai ba ya burgeta. Zaune take a aki ta kulle kamar yadda ta saba duk lokacin da za ta yi rawa ta tura. Tasha ado da wasu riga da wanda na an kanti masu kyau kalar pink,wandon bai kai asa ba. Gyara gashinta ta yi ta fara rawa cike da warewa ta tura ta na murmushi don ta san yanzu za ta ga ruwan comment da like. Ilai kuwa ta na turawa aka fara liking ta na kallo ta na murmushi,ta na shirin sauka wata numba da kullum take mata sallama a facebook,ta ara yi duk da ba amsa wa take ba amma ba ta gaji ba,ku san kullum sai ta yi mata sallama. Tsaki ta yi ta sauka da ga online gabaki aya ta na mamakin wannnan numba da take damunta,saboda ita in dai ba ta san mutum ba ba ta magana online,sanin cewar ita tauraruwa ce a yanar gizo so ba ta da lokacin da za ta tsaya ta na kula su,amma a ranta ta ji ta na son ta amsa sallamar don ta ji mai ke tafe da ita,saboda ta duba profile inta ta ga ita ma ba aramar mace ba ce,don da Barrister Mardiyya take bearing. Murmushi ta saki tare da ije wayar da sauri daidai lokacin da A.m ya mur ofar ya shigo,sai ta kama hannunsa ta ri e ta na dariya tare da kashe murya ta ce. "Barka da dawowa yanzu na ji arar shigowar ka, ina wanka ne shi ya sa ban fito ba." Dafe kan sa ya yi ya janye jikin sa ya zauna akan gefen gadon ya na kallonta tare da arin rage kayan jikin shi. "Babyna na gaji matu a kamar kai na ciwo yake son ya yi,yunwa nake ji kawo min abinci in ci anan bacci nake son na yi." Ya fa a tare da kwantawa ya mi ewa a kan gadon don jikin sa ko ina ciwo yake masa. Zainab ta an canza fuska ta ce " Na auka za ka ci abincin a dinning ne fita nake son na yi,kuma Juwairiya ta riga ta shirya abinci meye sai ka wahalar da mutum gurin aukowa." arashe maganar cikin yau i da yanga tare da aukar wayarta,da take kusa da shi don ta tuna kamar ba ta sauka a online ba,sai dai kuma da ta tuna ba ta ta a ganin ya auki wayarta da sunan ya duba ba,ko kuma ya ce zai yi wani abu. Gaban sa ya fa i da ta ambaci sunan Juwairiya ba zai ce ya manta da ita ba,amma sam ba ya son ya ji sunan sai ya ji haka kawai gaban sa ya fa " Zainab ba na son rainin wayo ni da gidana da kuma matata ba ni da ikon na ce ga in da zan ci abinci?Kuma da kika ce wancan za ta kawo min,to ba ita nake so ba matata wacce nake da iko da ita nake son ta kawo min,kuma ki je ki dawo bacci nake son mu yi babu in da za ki." an kausashe ya fa a ya na harararta wanda ya zamar masa a'ida,kamar wani mace in dai aka gaya mishi ba daidai ba, sai ya yi harara. Yarfe hannunta ta yi ta ije wayarta tare da fara orafi ta na ce wa." Haba Hubbi kai ma ka s an na yi ari ban je ko ina ba,na baka lokacina na tsawon kwanaki. an matsa kusa da shi ta ce." Yau fa bikin anwar awar Anty Fati ake yi,ka ga ai ya zama dole na je ko?"Ta tambaye shi tare da tsare shi da ido. Kallonta ya yi bai ce komai ba sai ya mi e ya kunna tangamemen tibin da ke akin ya ri e remote ya ce. " Dole ki je mana gayyar so i ni dai na gama magana ba in da zaki,ke ko kishina ba kya yi ki ta sa an aiki suna kawo min abinci,ko tunanin in canza miki ba kya yi." Kusa da shi ta zauna ta na fa in." Yarda da kai ne Hubbi Allah in za a ban kur'ani zan iya rantse wa a kan ka,sam ba ni da haufi ko da ba ka yi min al awarin ba za ka yi min kishiya ba,hankalina ba zai tashi ba saboda ban ta a jin ka yaba wata mace ba." an kalle shi da murmushin yadda a fuskarta ta ci gaba da ce wa." Kuma duk abin da nake yi ai ba na zuwa da awayena wa anda ba su da aure gidana saboda tsaro." Dariya ya yi jin abin da ta ce ya mi ar da ita ya na fa in." Ok Babyna ina godiya sosai da yardar da kika yi min,kuma ke in zazzafa ce ta ko'ina ga kyau ga ilmi da da tarin baiwa kala-kala,ina gaya miki ba wata sai ke a nan." Ya nuna mata irjin shi da da babbar yatsar shi dariya suka yi ta yi huggin in sa,sannan ta ba manna masa kis ta ruga da sauri don ta auko masa abincin,duk da ranta bai so haka ba amma fitar ta ta rantse sai ta fita. Don haka ko da ta dawo haka ta ci gaba da lalla ar sa har ya amince saboda ta dame shi,kuma bacci yake son ya yi da sauri ta auki an gyalen ta ta fice daga gidan. Bayan ya ci abinci ya an mi e tare da ba da tazara kafin ya kwanta,saboda abincin da ya ci sannan ya kwanta bacci. Juwairiya ta warke sumul bayan an ciwon kwana biyu da ta yi ta zage ta na ta aikinta,cikin osawa a ranta ta na addu'ar Allah ya sa ta samu cikin ya auke ta daga gidan,ganin yadda Zainab ta mai da ita baiwa,shi kuwa daga ranar bai ara neman ta ba. Ta na falo aiki take yi goge su tibi da abin da ya kama ta a goge a falon take yi. Sosai ta mai da hankalinta a kan aikin da take yi ta na son ta gama ta ora girkin abinci. Ya fito daga akin sa ya na sanye cikin doguwar riga na jallabiya mai ruwan madara,wayar sa ri e a hannun sa sam fuskar sa babu fara'a. Juwairiya ta saki aramin tawul in da take goge tibin da shi za ta ruga ganin ya fito, amma sai ya yi maza ya ri e mata hannu tare da kiran sunan ta. Tsayawa kan dole ta yi tare da juya masa baya cikin tsananin kunyar sa. Juyo da ita ya yi da murya mai sanyi ya fara magana. " Ban san tunanin ki in da ya tafi ba tun daga ranar kin auke wuta kin mai da ni kamar wani dodo,bayan kin san wannan kamar sharan fage ne akan tsarinmu har zuwa randa zamu cimma ha ar mu,kowa ya huta da wahalar da kan sa mu samu maslaha a rayuwar mu." Ta na son ta yi mishi magana irin ya fa a ta amsa mishi ko da maganar da ya yi mata babu da i,amma kuma ta na matu ar jin nauyin sa wanda ko ha a ido a bisa kuskure take yi. Sai ta kauda fuskarta a ranta ta na fa in." Kai ne kake son ka cimma ha ar ka,amma ni ina son na kasance da kai har abada A.m ina sonka burina ka auke ni daga gidan ka nima ka sama min anci na rayu da kai duniya ta san mijina ne kai." Amma a fili sai ta yi asa da kanta ta na kallon afafun sa suke da kyau da