Sashe 101
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi ta ha a." Kana yi mini biyayya Allah ya yi maka albarka ya shirya maka zuriya." Sai kawai ya saki ara yana dukan A.k ya ce." Yes ni ma na kai lokacin da za a yi ma yarana addu'a." " Ya A.m ina Anty Juwai in?"Hamdiya ta tambaye sa don burinta ta gan ta. " Kull karki ara ce mata Anty ai daga yau ta girma Maman an biyu za ki ce,saboda kin rage mata matsayi."Dariya suka kwashe da shi. Bayyana irin farin cikin da suka shiga abu ne mai wuya musamman A.m, da yake ji a ran sa dole sai ya yi sadaka don bai ta a tunanin haihuwa ta farko,za ta haifa mi shi zu a-zu an yara har guda biyu kuma duka maza. Gida ya dawo don ya yi wanka sannan ya yi wa Zainab albishiri,saboda ya bar ta cikin jimamin halin da ake ciki. A lokacin gari ya waye ko da ya dawo tana akinta ga mamakinsa sai yaga tana bacci,don haka bai tashe ta ba ya wuce bayi ya yi wanka,sannan ya saka turaren da yake so don ya san daga yau ba za ta ara yi masa orafi ba. Wani irin gayu ya yi cikin murna da annashuwa bai ta a tunani yana sonta haka ba,da ya duba halinta da ha uri ga kula da ibada sai ya ga tabbas ta ya kamata a so ta,uwa uba kuma girkin da take mi shi. Ya auna tsa anin son Zainab da ita wa ya fi so sai dai shi kan sa ya rasa ganewa,domin har yanzu yana son Zainab saboda soyayyarta daga Allah ne,bayan nan ga tausayinta da ya cika mi shi rai,ya san cewa za su kai ruwa rana in ya gaya mata abin da ke zuciyarsa,amma ya zai yi ita zuciya ba ta da ashi,shi kan sa ba yin kan sa ba ne Allah ne ya saka mi shi sonta a cikin zuciyarsa,domin zuciya an halicce da son mai kyaukyata mata. Ya sauko zuwa falo har ya auki makullin mota zai fita, sai kuma ya tuna bai yi magana da Zainab ba,da sauri ya juya zai haye saman,a ran sa yana ma kan sa fa a dole ya yi adalci a tsakanin su. Matu ar kunya ta kama shi ganin ta a saman bene tsaye da kayan bacci tana kallon sa,sosai ya ji kunya don fa har ya mur a kofa zai fita ba tare da ya yi mata magana ba. " Inna lillahi! Tabbas zuciyata ta gaya mini yau A.m ya yi sabon abu, wanda ya saka har ya manta da ni Zainab wacce yake i irarin ba zai ta a rayuwa babu ita ba."Ta fa a yayin da idanunta suka kawo ruwa don ko bai gaya mata ba,farin cikin da ke auke a fuskarsa ya bayyana hakan. Dawowa ya yi da sauri ya hayo in da take." Tabbas ta haihu Zainab na ci wallon Juwairiya ta haifa mini yara kyawawa har guda biyu." " Wayyo Allah na!." Ta fa a tare da zubewa asa ta dafe kanta tana jin wani irin tashin hankali." Kamata ya yi ya rungume ta kalle shi da hawaye a fuskarata." Na shiga uku da gaske yau ka samu abin da za ka raba mana soyayya da su?Kuma ba yarana ba?"Ta ce cikin kuka. " Haba Zainab ke da za ki yi murna Allah ya albarkance mu da yara har biyu,bai kamata ki nuna tashin hankali a rana irin ta yau ba.Na gaya miki babu abin da zai saka na raba son da na ke miki har yanzu son ki na nan a cikin zuciyata sa..." Tura shi ta yi ta mi e ta ce " Ka barni na yi kuka domin ya zama dole a rayuwata,haihuwa fa ka yi da wata mace yau ko mutuwa ka yi Allah ya cika maka burinka ka samu magaji,ni fa A.m ba zan ta a haihuwa ba duk da tarin dukiyar da na mallaka.Kaga ya zama dole in yi kuka ko abin da ya fi kuka."Kawai sai ta rushe da kuka ta kama arfen benen ta ri e bayan ta mi e tsaye. " Haba Zainab yarana ai naki ne na har abada bai kamata ki ce haka ba,kuma na yi miki al awarin ba zan ta a nuna miki wani abu akan yaran ba,sannnan zan kasance dake har arshen rayuwata in har ina numfashi a duniya." Tun Zainab na kuka yana rarrashinta har ya gaji ya mi e ya ce." Bari na kai kaya ana ta jirana." Ya fice daga gidan. aramin hauka ta yi duk da ta san A.m zai cika mata al awarin da ya aukar mata,amma ta ji kishin ta matu ar gaske kamar ta je ta kashe ta,amma babu yadda za ta yi saboda ta san cewa ta yi sakaci sosai. alla sai da ta yi sati aya a asibitin sannan ta warware ta samu lafiya sosai. Yara sun ci sunan kakannin su wato Dadddy da Abbu,wayyo Allah zo ka ga murna gurin takwaran Hassan wani irin gata ya nuna musu na ban mamaki. Momi ta ce a kai Juwairiya gidanta har ta gama wanka,daga nan sai ayi taron suna da shagalin bikinta da ba su san da auren ba,amma A.m ya nuna ina sam hakan ba zai yu ba domin ba zai iya kwana ba tare da yaransa ba,sai dai in za ta ba shi gurin kwana to ya yarda,daga arshe Momi aka ce ta je ta kula da ita, ila ya manta yana da wata matar da zai tare a gidan,saboda ta lura yarda take zumu in yaran babu abin da ba zai iya ba. A.m da ya aukar wa kan sa al awarin in har mai asibitin ya dawo sai ya yi masa nasiha,akan ya kula da asibitinsa don ranar gobe kiyama sai Allah ya tamabaye shi akan yadda yake sakaci da rayuwar al.umma. Sai dai ya kama bakinsa ya tsu e saboda ganin sa da ya yi,zai iya cewa tun da ya ke bai ta a ganin mutum mai agawa da girman kai irin sa,duk da cewa shi ma ya san yana da na sa,amma doctor Garkuwa ya dame shi ya shanye,yana kallon mutum kamar kashi wanda sam A.m bai fahimci haka halintar idanunsa take ba,shi a bin da ya ara ba shi haushi da shi zuwa da gajeren wando da yake yi a asibitin,wanda ya fahimci dabi'ar sa ne,saboda ya ji an asibitin suna gulmar sa ko waje zai fita da gajeren wando yake fita,kamar zai tsallake wuta.Sai dai kuma matashi ne mai kyau da ku i da aji an kwallo wanda sunan sa ya zagaye nahiyar duniya. Sau aya Zainab ta danne zuciyarta ta je asibitin sai dai ta sha kuka,ta yi al awarin ba zata ara zuwa ba,saboda abubuwan da ta gani yadda suke ji da ita,don Hajiya Binta take mata wanka,Momi kuwa kullum tana asibitin . Ta sha kuka ta bari a sallamota su yi ta ta are da A.m ya kar i yaran ita za ta shayar da su ya sallami Juwairiya don zuciyarta za ta buga,wata ila kuma ta amshi ta yi da Momi take mata,saboda ba za ta iya barin sa da ita ba na har abada,duk da ta san ko yau ta bar gidan ta fita na har abada ganin yadda danginsa suke nan-nan da ita kamar za su lashe ta don so. Wani irin so yake nuna musu na fitar hankali don a yarda yake ji da su ko kan sa ba ya auna haka. Hajiya Binta ta hana shi sakewa da Juwairiya, saboda tun da ta haihu ta canza mi shi babu tsiwa,sai shiru-shiru sai kuma hawaye da take yawan zubarwa in har ya yi mata magana,wanda hankalinsa yana tashi matu ar gaske,ya yi mata tambayar duniya ba za ta amsa mi shi ba,gabaki aya ta canza mi shi kamar wata kurma,wanda hakan yake aga hankalinsa matu Zainab ta raina kanta ta muzanta tun tana mamakin halin da yake mata, har ta daina tana kallonsa kawai don ta fahimci shi bai auke shi wani abu ba. Ko kwance suke haka zai auki hoton su ya yi ta kallo yana dariya kamar mahaukaci,in har tana son ya yi mata magana to ta ce ai Hasan ya bu e ido ka ya yi kaza,sai ya saki baki ya yi ta zuba yana hira,gabaki aya bai da lokacin ta sai na yaransa. Duk da cewar Hajiya Binta tana mi shi fa a amma bai san lokacin da yake aikata hakan ba,shi dai ya san yana musu son mutuwa. Kwance suke Zainab tana gefen sa da kofi a hannunta tana shan tea,domin ya umama mata jiki,kasancewar lokacin sanyi ne. A.m da waya a hannunsa yana ta kallon video na yaransa da ya yi musu,yau kwanan su sha takwas. Dariya yake sosai yana kallon Husain da yake bu e ido sai ya rufe da sauri ya uma ara bu e wa. Zainab ta mi e cikin fushi ta fisge wayar da take hannunsa ta kwa a ta da asa ta tarwatse. Hannu ya aga da sauri zai mare ta ko mai ya tuna ya fasa ya dun ule hannun sa ya saki. " A she ba ki da mutunci kishi kike da yarana Zainab?" Kawai sai ta fashe da kuka ta ce." Na gaji A.m zuciyata gab take da ta buga! Ka san yarda nake son ka kuwa?Ka dai na kula ni ba ka da lokacina kullum sai na yaranka ba dole na yi kishin su.Ka sani ko da yaran nan sun dawo gurina ka ce haka za ka rin a yi musu,wallahi ba zan lamu ta b..." " Ya she ki kar ki kawo mini maganar banza! Idan yaran ki ne za ki furta hakan,in har kika ce za ki yi kishi da yaran da na haifa to kin saka ma kan ki wahala,don ina son yarana fiye da komai Shekaru nawa na auka ba tare da na samu magaji ba."Ya katseta da fa in haka. " Zan yi kishi da su har arshen rayuwata in har haka za ka rin a yi musu,sannan Juwairiya ta haihu don haka ka cika mini al awarin da ka auka." Kallonta ya yi she e ya ce."Sai ta gama wanka zan tara ku na yanke duk abin