← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 102

Sashe 69

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

makaranta ita da Hauwa Juwairiya ce ta siyo su agwaluma da yalon Bello,tana ta ci tana lumshe idanun ta domin su take son ta ci. Hauwa ta kalle ta ganin yadda take ci kamar wata mayunwaciya. Ganin yadda ta kafe ta da ido sai ta alli agwalumar ta cige baki,saboda tsami amma haka take son sha. " Humh ke ma ka yi mamaki kamar wata mayya haka na tashi ina son na sha agwaluma,bayan ni ba mutuniyata bace saboda tsaminta."Ta ara alla tare da lumshe idanunta saboda da Dariya Hauwa ta saki ta ce."Anya lafiyarki alau kuwa ko dai ciki kika samu?Ni fa ina ganin kamar ciki ne da ke?" Da sauri ta mi e tare da yar da agwalumar cikin tashin hankali ta zare ido ta ce."Na shiga uku ciki fa da kika ce gaske ne?" " Ina zan sani tunanin haka nake gani a jikinki yau kuma kin zo da ba on lamari abin da ban ta a ganin kin sha ba kike sha.To ke ya kamata ki gane yaushe rabon ki da yin atan wata?" Ta tambaye ta ganin yadda ta diririce har hawaye sun fara sintiri a fuskarta. " Umh umh wallahi na manta tashin hankali ba zai barni na tuna ba,amma ina ganin kamar tun ina gidan Mama wayyo Allah na bani!" "Mene ne na banuwa Juwairiya fata za ki yi Allah ya sa wannan cikin ya dasa so tsakanin ki da mahaifinsa." " Tab!Ai wallahi in Zainab za ta iya haihuwa to ni ma zan bar wannan cikin a jikina zubar da shi zan yi ko da zan rasa rayuwata ne,nufin ki na fara irga watannin rabuwa da A.m na koma gurin Mama? Ba zan iya ba domin ban san da wani idon zan iya kallon ta ba."Ta ce cikin kuka. " Haba wai ke mai yasa ba ya fahimtar magana da aukar shawara ne! Ki bar cikin jikin ki na tabbata shine makamin da zai jawo kusanci tsakanin sa da mahaifin sa." Hauwa ta fa a cikin zafi domin zuwa yanzu ta fara ba ta haushi ganin ta cika kafiya da taurin kai. " Na lura ba kya sona so kawai kike na rabu da farin cikina.To sai na zubar da cikin nan kuma babu wanda ya isa ya hana." A zafafe ta furta cikin acin rai tana gani n kamar ba ta son zaman ta da A.m. " Ni ban ce ba ina ba in cikin yadda kika auki so kika ba ma namiji wai shin shine ka ai namiji a duniya,na tabbata ko rabuwa kuka yi za ki samu namiji mai kyau ki aura,ke ma ki na da kyau." ewa ta yi tare da aukar takaddun ta."In har za ki taimakamin na zubar ki zo ki raka ni asibiti,in kuma ba za ki ba ai na san hanya." Ta nufi hanyar fita da sauri Hauwa ta biyo bayan ta duk da ba ta farin ciki da zubda cikin amma babu yadda za ta yi. Likita ya kalle ta cikin mamaki sam ba ta yi kama da mutuniyar banza ba,amma mai ya sa take son ta zubda ciki? Da kuma ya tuna mugu ba shi da kama. " Don Allah likita ka taimaka ka zubda cikin nan ko nawa ne za mu baka." Juwairiya ta fa a jikinta na rawa ta kwaso duk ku in da ke jakanta ta ije a teburin sa. Duk tsoron da take ji na allura haka ta bari ya zumbu a mata tana cige baki,sannan ya auko wani magani ya ba ta kan in ta ji ciwo ta sha guda biyu. Tun kafin ta dawo gida take jin wani irin jiri kamar za ta fa i! Ko da ta dawo gida kwantawa ta yi saboda ciwon da mararta take yi,yayin da ciwon yake ci gaba kamar ana tsira mata allura. A haka ta kwana kamar za ta ba unci lahira, duk yadda ta so ta auki waya ta kira Hauwa ta gaya mata za ta mutu,saboda Zainab na nan A.m ko kallonta ba zai yi ba,amma ta kasa saboda ciwon mutuwa da take ji. Washegari ko aga an yatsarta ba ta iya wa sunan Allah kawai take fa i a bakinta da yake motsawa,tana kukan rabuwa da Mama ba tare da sun yi bankwana ba. Jinin dake zuba kamar an bu e famfo ya sa ta gane mutuwa za ta yi,sai ta fara maimaita kalmar shahada numfashinta na aukewa. Zainab da duku-duku ta fice asibiti saboda a kwai wani bawon Allah da za ta yi mata aiki da misalin biyar da rabi na safe,tun jiya aka so ayi aikin sai dai an kawo shi ta riga tabar asibitin,kuma a'ida ne in har ta koma gida ba ta dawowa. A.m dake zaune a falo ya na kallon news mamaki ya kama shi ganin har wannan lokacin ba ta fito ba ta aura abin karya. ewa ya yi tare da saka takalmi ya nufi akinta. Halin da ya ganta ya yi masifar aga mishi hankali,ba tare da wani tunani ba ya taitayeta ya saka a mota ya nufi asibiti da ita. yar aka samu aka tsaida jinin bayan cikin ya fita.Hankalin A.m ya tashi gani yake kamar mutuwa za ta yi wani irin tausayin ta ya kama shi,ya na jin bai yi mata adalci zai barta ta mutu a aki. Zura mata ido ya yi cikin tausayi ya na shafa kanta.Da sauri ya kamata ya ri e tare da tallabota ganin ta bu e ido. Juwairiya zuciyarta ta buga ganin likita ya shigo ri e da fayal a hannun sa,tsananin tsoro ya cika mata zuciya don ta san yau a sirinta zai tonu. A hankali A.m ya maida hankalin shi kan likitan da ya mi a masa fayal,ya ba masa bayani da harshen turanci duk da cewar Bahaushe ne shi. " Ina baka ha uri na zubewar baby don madam ta yi ari ne,har sai da muka yi mata wankin ciki.Ga wa annan maganin za ka siya an sallame ta." Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ri e likitan ya yi tare da jijjiga shi." Mai ya sa ka bari cikina ya zuba ka san shekara nawa na yi ina son na haihu?Wallahi sai kun dawo min da cikina don ba zai yiwu ba!" A.m ya fa a ya na na e hannun riga zai yi dabbe gani yake kamar gazawar su ya sa cikin ya fita. " Am sorry wallahi bamu da hannu a cikin zubewar cikin na nan! Amma na yi mamakin yadda kake son kaga ka haihu matar ka ta iya zubda cikin dake jikinta,don bincike ya nuna mana magani tasha mai arfi har cikin ya fita." Sai A.m ya kalle shi kamar mahaukaci ko bai fahimci mai yake nufi ba,ya kuma juya ya kalli Juwairiya wacce ta bayyana gaskiyar zargin da yake mata,saboda yadda ta yi tsuru-tsuru na rashin gaskiya.Wani irin sha a ya kai mata cikin tashin hankali. Zainab da ke tafe a cikin motar ta tana tu i cikin tsananin nisha i,sakamakon ta yi aiki cikin nasara wanda hakan yake saka ta tsananin farin ciki a duk lokacin da ta yi aiki. Wayarta ta auka ta kira layin A.m amma har ta yi masa kira biyar bai auka ba. Ko da ta iso haka kawai sai ta ji gabanta ya fa Maigadi ya wangame mata get ta shiga ta yi parking da sauri ta shige ciki,saboda yunwa take ji matu a.Da fari ta so ta fara cin abinci amma sai ta ga rashin dacewar hakan ta shige wanka. Bayan ta fito tana an dube-dube a cikin dirowar gadonta sai ta ga wani magani an oye shi a cikin dirowar. Da sauri ta bu e gabanta ne ya buga dam! Sa'ilin da ta ga sunan dake manne a kwalin maganin. " Maganin aukar ciki da wuri."Ta maimaita sunan maganin da Hausa. " Me A.m yake yi da shi bayan ni ba na haihuwa?" Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ba ta da amsarta. Wayarsa ta gani duka uku a gida bai auki ko aya ba sannan ba shi a gidan. Juwairiya sunan da ya fa o mata a rai kenan ta saki wani irin ara,da sauri ta sauko har tana fa i ta mulmulo amma ba ta kula ba. Wayam babu ita sai wayarta dake yashe a kan gado.Da sauri ta auki wayar duk da ta san a halin da take ciki ba za ta iya karanta komai ba. TO FA ARA! ARA!! ARA !!! KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI. BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI SAKACINA KO HALIN MAZA TAKU JAMILA LAWAL ZANGO JAMCY Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_
Chapter 69 · 0% Book details