Sashe 63
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
hawaye. Washegari A.m da kan sa ya shirya ta suka tafi asibitin.Bayan gwaje-gwaje da likitan ya yi musu har da ita,ya tabbatar masa da lafiyar ta alau ba sa bu atar wani dashi.Magani ya ba su wanda duk lokacin da zai yi tarayya da ita ya yi amfani da shi. Duk da cewar bai ji da i ba ya so ayi komai a wuce gurin,amma haka ya baro asibitin cikin jimami,ran sa duk babu da i bayan ya kar i maganin. A.m da gaske yake nufi da ya ce mata kafin su koma gida sai ya ba ta tsaraba,ita dai dariya ta ke masa suna gudanar da rayuwa a asar mai wuyar mantawa. A ranar da zasu dawo ta na kwance ta na tunanin in da za ta kai abubuwan da ya siya mata,saboda ya yi mata siyayya ya kashe mata ku i na ban mamaki ta san ko hauka ta yi ba za ta kai ma Mama kayan nan ba,haka kuma ba za ta kai gidan sa ta na amfani da shi ba amatsayin ta na ar aiki,mamakin sa take da ko tunani bai yi ba ya yi mata irin wa annan siyayya. Ta yanke shawarar kai ma Mariya ta ije mata ku in kuma sai ta din ga sakawa a banki. Kamar yadda suka tsara jirgin su na sauka ta wuce gida kan sai ta ara sati,in ya so sai ta ce jikin Mama ne ya tsananta. Juwairiya ta tsorata lokacin da ta yi sallama Mama ta amsa mata ta na udundune da bargo,sai hankalinta ya tashi ganin ta yi wa Zainab aryar Mama ba ta da lafiya gashi ta same ta ba lafiyar,shi ya sa aryar ciwo babu kyau don ita gani take kamar aryar da ta yi ne ya kama Mama. "Mama dama baki da lafiya shine baki kirani kin gaya min ba."Ta fa a cikin tashin hankali ganin ta na jin jiki. "Na so na kira ki ita ta hana gani take kamar jikin ba zai yi zafi haka ba." Ibrahim ya ba ta amsa don ta kasa magana sai hawaye dake gangarowa,saboda tsananin zafin ciwo kuma duka kwana biyu ta fara ciwo. Asibiti ta samo mai adaidaita ya kai su bayan an yi mata allura aka ba ta magani,suka dawo gida ta shiga jinyar Mama. Rashin lafiyar Mama sai ya hanata komawa gidan ta na jinyar Mama da yanzu ta fara jin sau "Juwairiya ya kamata ki koma aiki kin san yau saura kwana goma sha biyar shekara aya ya cika,kuma kin san na gaya miki ko duk duniya mutumin nan zai baki ba zan lamunta ki ara ko da kwana aya ba." Mama ta ce mata cikin murya mai an zafi duk da jikinta babu arfin da za ta aga murya. Gabanta ne ya fa i ta ago ta kalli Mama sai jikinta ya yi sanyi ta ce."Na sani Mama kuma da zarar lokaci ya cika ni kaina gida zan dawo na yi aure kamar yadda kike bu ata,amma ki kwantar da hankalin ki kin ga yanzu ba kya jin da Ta mi a mata kofin kunu tsamin da ta sa ta dama mata saboda tafi son abu mai ruwa-ruwa. "Ai ina tuna miki ne don ranar da shekara aya ya cika in har baki dawo ba sai dai ki ji na kai Baba Sani kotu." Ta kar i kofin kunun da ta mi a mata ta fara sha.Jikinta ne ya yi sanyi ta mi e ta fice daga akin domin ba ta aunar ta ji Mama ta irgo mata kwanakin rabuwar su duk sai ta ji hankalin ta ya tashi. A yau take son ta je ta gyara layinta da kampani m t n suka kulle mata tun washegarin da ta dawo saboda ciwon Mama ta kasa zuwa ta gyara,amma yau ta ga jikinta ya yi sauki ya sa ta shirya don ta san A.m zai neme ta har ma da Zainab saboda ta ara kwanaki akan sati biyu. Kasancewar da yamma ne sai ta yanke shawarar ta tafi a asa tun da babu wani nisa. Tafiya take a hankali kamar ba za ta taka asa ba ji ta yi wata mota ta sharo ta na shirin tureta. Da sauri ta matsa gefe cikin tashin hankali ta na tunanin waye wannan mahaukacin da zai kasheta. "Ke amaryar wucin gadi ina za ki je ba tare da izini mijinki ba?" Muryar A.m ya daki kunninta lokacin da yake saukar da gilas in motar sa. Mamakin ganinsa da tsorata ta da ya yi ya sa ta ata fuska amma da murmushi auke a fuskarta. "Allah ka ba ni tsoro na yi mamakin ganin ka"Ta ce mishi lokacin da ta tsaya a gefen shi. A.m ya kashe mota ya fito ya tsaya kusa da ita ya ce."Ina ta nemar wayarki ba ta shiga na kira wannan kwa ayayen Baba Sani amma kin san me ya ce."Wai sai na biya shi zai ha a ni dake hankalina ya tashi hakan nan na daure na zan zo gidan ku sai gashi mun ha e kin yi satar fita." Dariya ta yi jin abin da ya ce."Ni ba satar fita na yi ba layina aka rufe zan je na bu e ne."Ta bashi amsa ta na kallon shi. "Lafiya ba ki dawo ba gidan babu da i kwana biyu na yi missing inki ga tubbina da ya yi rashin dadda ar abincin.Gaskiya gangar jikina da tubbina sun yi rashin har na kasa ha ura ." Zuba mishi ido ta yi jin abin da ya fa a kamar da gaske. "Ai ko ya kamata ka fara sabawa ko ka manta saura kwanaki mu rabu.Kuma meye abin damuwa bayan ka na da matar so a gida ban ga dalilin da zai saka ka damu da matar wucin gadi ba." Ta fa a cike da tsantsar kishin Zainab da ya bayyana arara a fuskarta. Kallonta ya yi tare da matsowa daf da ita ta yadda har suna jin numfashin juna ya kama hannunta ya ce. "Kishi ko?" Ya saki hannunta ya juya mata baya sannan ya ci gaba da magana. "Bai kamata ki saka kishin matata a zuciyarki ba kin san cewa ita ce matar so.Kin sa dalilin aurenmu am sorry to say da Zainab ta na haihuwa babu abin da zai saka na aure ki.Kawai ni na san in muka rabu zan yi kewarki da kishin mijinki don ki na da baiwar da ba kowa ce mace take dashi ba." Ta na son ta yi magana kuka ya wace mata amma hakan na ta daure ta ce."Mai yasa ka shigo da ni cikin rayuwarka ka san ba gurbina a cikin zuciyarka?" "Saboda ki haifi yaro na bawa Zainab saboda ina son na ga waina ya sa na aure ki."Ya fa a muryar sa a age. "To mai ya sa kake gaya min maganganun da suke yaudarar zuciyata?Ka tsaya iya kan abin da kake bu ata a gareni." Cikin kuka take mishi maganar sai ta juya za ta ruga da gudu da sauri ya janyo ta zai rungume ko mai ya tuna ya sake ta ta ruga da gudu ta na kuka. Cikin motar shi ya fa a ya na wani irin huci kamar mesa ya da e a gurin sannan ya figi motar a guje kamar zai tashi sama. Lantana mai aikin Zainab da take la e a bayan kango ta na kallon A.m da ya yi shirin rungume Juwairiya ta fito cikin tsananin mamaki ta na kallon in da motar shi tabi. Zaro idanunta ta yi cikin tashin hankali ta na mamakin da ma cin amanar ta suke shi da ita?Allah Sarki baiwar Allah ta na can ta damu da ita gashi wayarta ba ta shiga,ashe ita ta na can suna cin amanarta.Haba!Biri ya yi kama da mutum ai ko yau dole Zainab ta ji abin da suke yi ita ta na can sai tsabar son ku i ta auko mace zu iya ta ije ma mijinta. TO FA WAYYO ALLAH BA RI NA YI NAN DON GASKIYA BAN SHIRYA GANIN WANNAN TASHIN HANKALI BA. KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI. BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI SAKACINA KO HALIN MAZA TAKU JAMILA LAWAL ZANGO JAMCY Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_