Sashe 82
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 31* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM " Momi da gaske ne duk abin da na gaya miki na aikata,tabbas na sha maganin hana haihuwa don kar na haihu in tsufa A.m ya guje ni.Amma duk abin da na yi saboda shi ne ina..." Wani irin gigitaccen mari Momi ta kwasa mata sai da ta wuntsila. " Zainab are you stupid! Kin san abin da kika aikata kuwa kin san irin tashin hankalin da kika saka kan ki? Inna lillahi na shiga uku! Mai ya sa kika oye min ina matsayin mahaifiyarki? Da duk haka ba ta faru ba." Zainab da ta ji saukar marin Momi sai da ta yi suman wucin gadi,ta dafe uncinta cikin tashin hankali,saboda tun da take Momi ba ta ta a kai koda an yatsarta jikinta ba. " Momi marina fa kika yi?Bayan ba ki ta a ko yin ihu mai arfi gare ni ba,balle ki ora hannunki a jikina." Momi da take cikin tashin hankali saboda abin da ta aikata,kallonta ta yi ji take kamar ta rufe ta da duka. " Wallahi Zainab ji nake kamar na rufe ki da duka! Kin yi kuskure sosai in har kika yi wasa sai zaman duniya ya gundure ki,saboda girmar laifin da kika aikata. Maihaifinki na matu ar son ya ga kin haihu haka nima, dangin A.m suna nan suna tsananin damuwar su akan rashin haihuwa da ba ku yi,ina kallon sa a matsayin azzalumi baya haihuwa ya kuma i rabuwa da ke,ashe tawa ar ne ba ta haihuwa." Ta fa a cikin kuka sosai wanda ya aga hankalinta sosai. Hannunta ta ri e tare da fashewa da kuka ta ce." Idan har za ki yi irin kukan nan, ya kamata ni na yi hawayen jini Momi,amma har yanzu ban ji tashin hankali ba sosai don ba na haihuwa,asalima ni yara sam ba su dame ni ba saboda wahala kawai suke baka, kuma kin san Momi na tsani azanta sam ba na son na wahalar da rayuwa." Momi ta fisge hannunta ta juya mata baya,ta na kallon windo cikin wata irin murya,mai nuna tsantsar damuwa ga mamallakin muryar ya shiga. " Har yanzu ke yarinya ce ba ki gane komai ba,amma na tabbata za ki yi nadama in har ba ki auki mataki ba,na rantse miki duk ranar da ki ka yi sake A.m ya haihu,daga ranar za ki fara son yaran duniya ba ki aya." Ta juyo da ita suna fuskantar juna cikin murya mai sanyi ta ce."Duk da cewa Allah ya mallaka mini ke,amma mahaifinki har yau yana kukan rashin a,ba za ki gane mai nake nufi ba sai ranar da kika yi hankali gurin tunanin wa zai gaji dukiyarki.Ki duba irin dukiyar da kike da shi in kika mutu wa za ki bar mawa?Ko so kike duniya suci. A.m yana da ku i da ahalin sa mene nufin ki akan dukiyar babu rabon ki a ciki?" " Haba Momi mai zan yi da wata dukiya iya abin da Allah ya mallaka mini ya ishe ni, ba sai na nemi agajin kowa ba,ga kuma dukiyar mahaifina, da ni ce ka ai mallakin sa." Ta ce da Momi cikin jin osawar maganar ta, don ita ba ta yi tunanin za ta auko mata wannan shirmen ba,saboda damuwarta ta fi gaban wannan.Abu ne na zuciya da Allah ya ke halittar so a ciki,sam ba za ta yadda wata ta wace mata shi ba. " Ba za ki gane ba ne Zainab dole ki auki mataki na san mai kike nufi,kuma magana ta tana kan hanyar damuwarki,kin ga in kika yi gigin barin abin da kike fa i ya faru,wallahi sai kin raina kan ki." " Wannan dalilin ya sa na ce tuntuni mu watsa mata acid amma Momi kika i,da yanzu matsalata ta kau yanzu gashi kin sakani a cikin matsala,don ko ka an ban yi tunanin tana cikin gidana ba."Ta ce da ita tana ganin kamar Momi ta ja mata duk abin da ya faru. " Na hana ki ne saboda watsa mata ba shine mafita ba,in har yana sonta to zai yi komai don ya ceci rayuwarta.Na bari ki dawo hankalinki ya kwanta sai mu ullo ma abin ta ruwan sanyi,ba tare da ya yi tunanin da saka hannunmu a ciki." " To yanzu Momi ya zan yi?Ba zan iya barin ma wata kucaka azama yar talaka mijina ba,ina son sa shi kan sa ya san irin son da nake masa.Ki taimake ni mijina ya dawo gareni Juwairiya ta fita daga rayuwar sa,in har ba so kike ki rasa ni ba,don na yi rantsuwar ba zan ta a barin wata ta ra e shi ba,ko da ace ba ni tare da shi! In ko hakan ta kasance mutuwa zan yi,sai dai ku nemi wata ar." Jijjiga ta da arfi take yi ganin yadda ta fita hayyacinta tana watsi da kayan akinta. " Ya isa ki natsu ki gane wace ce mahaifiyarki sam ba zan bari hakan ta faru ba,ko da ace zan yi yawo tsirara ne! Kin san wace ce mahaifiyarki ya kamata ki zama jaruma.Irin zuciyata ya kamata ki auka,ba in aka yi miki abu ki ce za ki rama ta kisa.Sab ba haka jarumi yake cin nasarar sa ba,dagewa za ki yi ki saka makamanki ki ya i duk wanda ya zama garna i a cikin rayuwarki." Ta fa a yayin da ta yi shiru tana kallonta don ba ta fahimci mai take cewa ba." Bari na baki labarina wanda baki ta a sani ba Zainab.Mahaifin ki yaso wata mace kamar ransa yana jin zai iya mutuwa in bai same ta ba,ita kuma awatace da muka ha u a makaranta. Mun sha u sosai muna shiri da ita,duk an'uwanta na san su,don har zuwa nake na kwana a gidan su.Mahaifinta hamsha in mai ku i ne sosai suna da ku i,yayin da ni ina karatu a gidan kawuna shi ya auko ni ya sani a makaranta iyayena talaka. Tun da na fara mahaifinki na auki son duniya na ora mishi sosai,sannan ina son na canza rayuwata daga angin talauci. Matar kawuna ta yi mini hanyar wani malami ya ta kaini gurin sa,don ya janye hankalin sa daga gareta,amma sai dai in na yadda da sauran wayayen haihuwana za'a yi asirin,in da za'a bar aya kawai wato aya zan haifa a duniya.Ba tare da damuwa ba na amince.A lokacin har an saka ranar auren su biki ya rage kwanaki aka fasa auren,in da ya zo gidammu da fari iyayena sun i,amma ganin zai haukace dole aka aura aurenmu wanda dalilin haka ta aikata suicide. ta mutu. Sai dai na fara nadama bayan aurenmu duk lokacin da hankalin sa ya dawo jikin sa,sai ya kasance ina yawan zuwa a juyar masa da hankali,a haka muka rayu har na haife ki bayan na haife ki sai Allah ya saka mi shi tsananin sonki,domin yana son yara sosai ya sha gaya min zan haifa masa yara da yawa." Momi ta yi nisa tana kallon Zainab da ta yi zuru ta zuba mata ido tana kallonta cikin al'ajabin labarin da take gaya mata. " Na yi matu ar dana sani sosai da na yadda aka yi amfani da sauran waina,saboda dangin sa sun takura mi shi akan ya ara aure,sai dai na yi ruwa na yi tsaki har yau ya kasa ara auren.Don haka ki share hawayen ki A.m bai isa ya zauna da wata mace ba bayan ke,ke ka ai ce za ki zauna da shi har abada,na yi miki wannan al awarin in...." " No Momi don Allah kar ki saka wani abu daban a cikin aurena! Ina son A.m ina burin na rayu da shi har abada,kuma kin san ni ba na son wa annan halayen da kike yi,don haka in ba za ki taimaka min ba,kawai ni zan watsa mata acid ko na auketa a garin."Ta ce da Momi cikin shagwa a tana kallonta yayin da hawaye suke ara turereniya a fuskarata. " Banza shashasha! Ita kin san abin da ta yi har A.m ya kula ta? Ki zauna garin kallon ruwa kwa o ya yi miki afa,kuma Allah kin ji na rantse miki ko ke baki yadda da hakan ba,dole mu zamu auki mataki." "Haka ne Momi ki yi ha uri amma gaskiya ba zan amince da abin da kike so ba,zan kira Anty Lubna na san za ta ba ni shawara." Gabaki aya kayan sawarta suka kwashe ita da Momi,bayan ta kira mahaifinta ta sanar masa take ya buga ma Daddy A.m waya saka yi kaca-kaca. Jikin Daddy ya yi sanyi to fa asiri ya tonu ya san cewa a kwai daru saboda shi ya saka hannu aka aura auren. Jikin shi ya kama rawa saboda irin zagin da mahaifin Zainab ya din ga yi mi shi,ya san dole ya kira ainihin mahaifin shi ya gaya mi shi. Wani irin zufa take tsefo masa don ya san Allah kawai zai fidda shi,sai yanzu yake ganin mugun wauta da ya yi har suka yi galaba ya amince da aure. Wayar sa ya zaro ya don ya kira A.m cikin fushi.A ran sa yana ba in cikin halin dukan mata da A.m ya aukar wa kan sa. ********** " Wai mene ne haka ne A m ka san mai kake yi kuwa a asibiti muke,kuma ka duba idanun mutane a kan ka suke sam ba ka da kunya." A.k da ya yi wa Juwairiya rumfa da take kwance kan gado,ya kuma tura hannun sa a cikinta wai zai ji in da yaron yake. Juwairiya da wani irin kasala ya rufe ta zuciyarta tashi take yi,kamar wani aman yake son ya zubo mata. Da sauri ta ture hannun sa ji ta yi kamar an ora mata wuta a in da ya ora mata hannu a cikin. Ita ji ta yi da ya matso ta kamar wani irin wari za ta ce ko amshi mara da i yake mata. Hannunta ta saka ta toshe hancinta da jin wani amai zai taso." Don Allah ka matsa kusa da ni sam ba na son jin amshin ka kusa da ni."Ta fa a da muryar kuka tana jin wani unci a tare da ita. A.m ya yi turus kamar zai saka kuka ya juya ya kalli A.k