← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 102

Sashe 65

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai iya auren ar aiki ba,amma yanzu sun cika ora kwa ayin su ba sa iya auke idanun su. an danne kishinki ki gano wani abu in har kika gane ya na tare da ita, ni zan siyo miki acid ki watsa mata,ko ki bani kwangilar watsa mata babu uban da zai aure ni yar manya ce ni mijina kuma canal." yar Nabila ta yi nasarar kwantar mata da hankali,duk da har yanzu ta kasa amincewa,don haka ta saka a ranta ya na dawowa za ta tambaye shi dole ya gaya mata komai. A tare suka fito daga akin suka nufi kicin in da Lantana take aiki,ganinZainab da gudu ta ruga ta na fa "Wallahi Hajiya na gan...." Da sauri Zainab ta ora an yatsa a bakinta kan ta yi shiru,don ta na jin kamar ta ara mata wani dukan.Ku i ta ara ma Lantana da take ta murna sosai ga duka ga samun ku i ita kam yau gulma ta yi riba. Zainab na zaune a gaban madubi ta na tsantsara kwallliya zuciyarta cunkushe da tunani kala-kala. Ji ta yi an rungume ta ta baya sannan ya ora kan sa a bayanta,ba ta juya ba kasancewar tun kafin ya shigo amshin turaren sa ya bayyanar masa da shigowar sa. Fuskarta a aure ta juyo ta kalle shi sama da asa haka kawai sai ta ji wani mugun haushin sa da tsanar ha a jiki da shi. Sakar mata murmushi ya yi tare da kamo hannunta. " Gibbiyar mata sarauniyar mata a cikin birnin zuciyar Abdurrahman mai na yi ake fushi da ni? Ko don rashin dawowata da wuri ne am so so sorry babyna wallahi wani uzuri ya tsare ni na kira wayarki ba ta shiga." Ya fa a da muryar sa mai sanyi da take kwantar mata da hankali ya kuma san ya na sace zuciyarta da ita. Ganin ta i kula shi sai ya kamata suka fa a gado ya na sha an kamshin turarenta ya na fa " Wane irin turare kika sa yau kamar yafi wanda kike shafawa da i,don ban ta a jin amshi mai kwantar da zuciya da saka nisha i a rai ba.. Gaskiya kuma kwalliyar ta yi na kuma yaba bari kiga in siye ta koma nawa ne babu tayi." arin warware tawul in dake jikinta yake yi ya na gaya mata kalamai masu da i da kwantar da hankali. Da sauri ta wace jikinta ta harare shi ta saki tsaki ta saka kayanta ta fice daga akin ba tare da ta kalli in da yake ba. Tsayawa ya yi yana kallonta ran sa ya ace saboda ya tsani tsaki ita ma ta san haka,don haka bai ara kula ta ba ya tu e kayan sa ya watsa ruwa,bai nemi abincin ba saboda sai da ya tsaya gidan A.k ya ci abinci tun da ya san Juwairiya ba ta nan gashi ya kasa iya cin abincin Lantana. Kwanciyar sa ya yi ba tare da ya ara kula ta ba,wanda hakan ya sa ta fara yadda da abin da Lantana ta fa a mata,tun da har zai iya yaleta ganin ta yi fushi ba tare da ya rarrashe ta ba ko ya tambayi ba'asi. Tun tana saka ran zai zo ya rarrrasheta amma sai ta ji shiru,ta kalli agogon hannunta arfe aya na dare sai ta sauka a chert ta shige akin sa tare da buga ofar da arfin gaske. Tsayawa ta yi a kan sa ta na huci kamar wata mesa ganin bacci yake yi,filo ta auka tare da maka masa ya bu e ido cikin razana ganin ta tsaye a kan sa sai ran sa ya ace,ya kalle ta bai ce mata komai ba amma idanun sa suna masa kallon garga " Kaga Malam ka tashi magana nake son mu yi da kai."Ta ce dashi tana girgiza ugu idanunta a bushe kamar ba dare ba. " Zainab." A cikin wata irin murya ya yi magana sannan ya ora da ce wa." Don Allah bacci nake ji ki bari sai da safe." Ya rungume filo tare da mirginawa ya ci gaba da bacci,komai ya tuna sai ya juyo ya na kallonta ya mi o mata hannu yana nufin ta zo su kwanta. Wani irin kallo ta watsa mishi." Ka ga Malam wallahi sai ka tashi ba za ka barni da ba in ciki na kasa bacci ba don ba zan iya bari gari ya waye ba." Sai ta fara tsiya ta na mishi wasu irin maganganu da ya kasa gane mai take ce wa,sannan kuma ta hana shi bacci da ga arshe dole ya tashi saboda magana take da murya mai arfi,kuma abin da take fa i ya yi mugun aga masa hankali duk da bai wani fahimce ta ba. Tashi ya yi zaune ya na mata wani mugun kallo. " Wallahi baki da mutunci ga shi na tashi gaya mini damuwarki,amma ki sani in na ji maganar ba ta da mahimmanci kin san sauran." Ya fa a da muryar garga i ganin ta hana shi bacci. Hararar shi ta yi tana fa in" Oh koma me za ka ce kai ka sani tun da ka zama munafuki, ka bani mamaki fir'auna a zuci Annabi Musa a baki." Ta fa i hakan ne don ta gane ko arya Lantana take mata don har yanzu ta kasa yadda da abin da ta fa a mata. Bai ce mata komai ba ya ara watsa mata mugun kallo na na garga in ta iya bakinta. Cikin tsanani mamaki A.m ya ji ta watso mishi tambayar da ya girgiaza shi ta ce. " Mene ne ala ar ka da Juwairiya?" Ya shiga cikin tsanani tashin hankali ya ru e matu a ya kuma razana domin jikin shi rawa yake ayi,jin tambayar da ta watso mishi ya shiga damuwa Baba Sani ya fa o mishi a rai yana tunanin ko shi ya fa a mata,ya san zai iya don ya na shakkar sa ba shi da mutunci na arshe. Allah ya so babu wadatacciyar haske a akin sai fitila mara haske na bacci dake kunne mai kama da babu,domin da a kwai ya tabbata babu abin da zai hana ba ta gano gaskiya ba,saboda jikin sa ya ji e sharab da gumi sai zufa yake karyo mishi,ya na ji a ran sa in Allah ya ha a shi da Baba Sani sai dai Allah zai raba su. Shirun da ya yi sai zuciyarta ta karye ta fara tunanin to ko gaskiya ne. A.m da yaga zai tona a sirin kanshi da kanshi sai ya dake cikin wata irin murya ya ce." Mai ya sa kike min wannan banzar tambayar waye ita kuma meye ha a ni da ita? ar aikin ki fa kike danganta ni da ita kin cuce ni,mai zan yi da ar matsiyata jinin talauci kin ta a ganin na kula wata mace duk da damuna da suke yi balle ita. Wani irin sanyi ta ji ya kamata jin abin da ya fa a dama ta san ce wa babu yadda za ayi ya kulata,amma don kar ta yi saurin sauko wa ta ce." Ba wani nan munafiki ai ni ka bani mamaki ka rasa wacce za ka kula sai ita,to bari ka ji na rantse maka ba ita ba ko wace mace ka kalla nine ajalinta saina illata rayuwarta,yadda ko wa anda suka kawo ta duniya ba za su so su ganta ba balle kai kana tunanin zaka haihu ne ni bana haihuwa." A.m da ya koma ya kwanta jikin sa a mace hankalin sa ya tashi sosai,ya an ji da i da ya fahimci ba Baba Sani ya gaya mata ba,don in da shine duka zai ata lamarin ya tabbata sai ya kunna mata wannan recording da ya yi,amma a ran sa ya na mamakin wane munafukin ne ya gaya mata,ya san ce wa A.k ba zai ta a gaya ma matar sa ba." Domin ya cire mata shakku sai ya mi e cikin aga murya ya ce. " Look Zainab na lura baki da hankali ko kuma kin sha wani abu ko kin fara aukar zigin awaye,in baki yadda da ita ba mai zai hana ki daina yawo ki zauna ki kula da ni,wanda ni kaina zan fi bu atar haka,bawai ki tsaya kina zargina da wata kucaka ba,kamana kike tunanin zan iya kula ta mai take dashi kuma waye ubanta a duniya." Ya yi uta ya ci gaba da magana da arfi ganin maganganun sa suna tasiri a kanta saboda ta yi shiru ta na sauraren sa. Janyo ta ya yi zuwa jikin sa." Zainab please trust me." ara marairaice murya ya na shafa bayanta da ta yi lamo a jikin sa kamar wata mage ta na ara jin madarar son sa na waranya a zuciyarta. A.m da ya ji ta yi lamo a jikin sa ya saki gwauron numfashi,ya na tunanin yadda zai yi ta amshi yaron da Juwairiya za ta haifa masa,amma ya saka a ran shi dole ta kar a ko ana ha mata ana ha maza. " Bai kamata ki yadda da zugin ma iya a kanmu ba ki tuna na yi miki halacci har yau babu wanda ya san ke ce bakya haihuwa,kuma na kasa ha a wata mace da ke na ri e al awarin da ba yi miki duk da ina son naga waina a duniya fiye da rayuwata,hakan ba zai sa ki yadda da ni ba?" Zainab jikinta ya mutu murus duk da ta yadda da shi,amma ta auki aniyar cusgunawa rayuwarta da wula anta ta agaban shi,domin ta cire an shakkun da take yi a zuciyarta kuma in ta gane gaskiya Lantana ta kuka da rayuwarta. " Ka yi ha uri zauji zuciyata ce ta kasa gasganta hakan bayan na san halinka fiye da kaina,amma in sha Allahu ba zan ara maka irin wannan tuhumar ba, kuma ni ma na fahimci ma iya ne suke son su raba mu sai dai su mutu don ni da kai mutu ka raba." Rungumota ya yi ya ce." Wannan dalilin ya sa nake matu ar son ki auren mu da ke sai mutuwa za ta raba ni da likitar likitoci. Yauwa bari na siya kwalliyar da aka hana ni siye bayan daga kallo aya
Chapter 65 · 0% Book details