← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 102

Sashe 16

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ta na cire doguwar rigar da ya matseta kamar za ta yi amai,ta na wala ma Mero kira. Wani arin haushi ya turni e shi ita sam ba ta kishin jikinta ganin shigar da ta yi,sannan ta na cire kayanta amma take kiran me aiki tazo kai Zainab lamarinta a kwai gyara. Bayan ta cire rigar ta umurci Mero ta auko mata wani wani kayan ta saka,sannan ta nufi gurin sa da yake zaune saboda tsaban takaici be kalleta ba bare ya tanka mata,sai kallon agogon hannunsa yake. Ba tare da nuna damuwa ba taja tiren abincin da ya saka Mero ta kwashe wan can ta kawo mishi,saboda tsabar yunwa da yake ji amma ya kasa cin abincin sam babu tes jira yake a gama ruwan ya ya yi take away. Fara ci ta yi ta kalle shi tace."Habibi ba ka ci abinci ba lafiya."Banza ya yi da ita yaci gaba da kallon wayarsa ya na danne-danne a cikinta. Kai hannu ta yi ta ta a wuyan shi ko ta ji da zafi a tunaninta ba shi da lafiya,amma sai ta ji jikinsa normal.Ta e bakinta ta yi ta ci gaba da cin abincin a ranta ta na fa in."Miskilancinne ya motsa bari na kama kaina." Kusan minti talatin ya na kwance be tanka mata ba har ta gaji da zama ya i kunna kallo ta san ta na kunnawa, ze taso mata tunna dama a yadda ta gan shi jira yake ta ta o mishi,sai ta mi e sif za ta shige akinta ta hau charting. Idanunsa a lumshe ba tare da ya bu e ba yace."Da ga ina kike?"Yace a cikin wata irin murya me kama da da baya son maganar. Dawowa ta yi ta zauna ta duburbuce ta fara in ina.Ya ara jeho mata wasu tambayoyin da cewa."Sai yanzu kika dawo ba na hana ki dawo min gida da daddare ba?Me yasa baki wuce gidan kuba.Kuma da izinin uban wa kika fita?" Gabaki aya ta tsorata ta kuma ru e ganin yadda yake jeho mata tambayoyin da ta kasa amsa koda aya ne. ewa ya yi ya matso kusa da ita ya na kallon kayan da tasa ya auka ya na kallonta a wula ance."Ba na hanaki saka irin kayan nan ba wai ke me yasa bakya kishin kanki yanzu fa a gaban ar aiki kika canza kaya,sam bakya kishin sirrina Zainab hauka kike son na yi a kanki na fara gajiya da halinki." Duk cikin maganganunsa ba wanda ta ji haushi sai tambayar ta daga ina take da an yi jim ta kuma dake ta ba shi amsa da cewa."Ina tunanin mun gama magana akan fita ba sai na tambaye ka ba saboda gaskiya ban ga a na wannan takurar a gidan mu ba.Kuma fa gidan awar Anty Usaina muka je yau ake birthday anta."Ta arashe maganar ta na son ta ja hankalin shi ya sausauta fushin da ya auka. ara jan tsaki me arfi dama ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta Tsawa ya daka mata yace "Malama karki raina min wayo na gaji da wa annan banzan bidi'oin da kika saka a ranki.Kin raina ni matu a Zainab baki auke ni da daraja ba a matsayina na mijinki,watakila haka kika ga ana yi a aure a matsayinki na matar aure ba zaki shigo gidana ba sai tara da mintina." a kansa ya yi ya mi e yaci gaba da cewa."Kin san nace miki in har kika fita ba da izinina ba,ban yafe miki ba kuma mala'ikun rahama suna tsine miki harki dawo sai ki kiyaye." Hararan shi ta yi tace cikin gunaguni."Ta ni ai na gaya maka ba zan amince a takurawa rayuwata ba.Haka kawai to meye amfanin ilmina na lura so kake ka mai dani irin gidahuman matan nan marasa ilmi,wa anda suke bari namiji na raina su wai duk in da zani saina tambayeka Allah ya kyauta." Da takaicin yadda ta raina shi bata shakkar shi yace."Ba ma fita ba na hanaki driving sai dai duk in da zaki a yi driving in ki."Ya na fa in haka ya fara taka matakalan bene ze haye. A sukwane ta jawo rigar shi ta baya cikin fushi tace."Wallahi ba za ta sa u ba wai bindiga a ruwa Ka mata ni zan yadda wani shashashan direba ya tu a ni,karka manta kusan motocina daga gidanmu na zo da shi bare ka yi min iko,in ma akan wace ka siya min ne ba zan ara hawa ba amma ba wanda ya isa ya kafa min dokoki." Nu na ta da yatsa ya yi ya na cewa."Ba na hana ki kuma na yi miki warning akan ri e min riga da kike yi ba,to wannan ya zama na arshe da zaki ara wannan gangancin.Kuma kika kuskura kika zage ni sai kin raina kanki,don jikin ki ze gaya miki." Dariya ta yi me sauti ta ba shi amsa da fa in."A lai-lai da ka tabbata waya kamar ni zaka buga aiko ruwan sama se inna so bare wani gardi can.Duk mutanen gidan ku kuwa sai an koya musu hankali ai ban yi kalar matar duka ba.Ko ka manta matsayin uba na."Ta numfasa sanann ta ora ta na kallon shi da tsananin acin rai ya sa shi tsaye ya na kallonta. " Kuma da kake fa in karna zage ka inna zage ka me za ka yi?"Tace mishi cikin zallar rashin kunya ta na karka ugunta.A.m ya yi uta yace. " To ki kwatanta ki gani fitsararriya kawai." Baki ta turo mishi tare da murgu awa." Ni ba fitsararriya ba ce banza mara m....". Wani irin mari ya gaura mata wanda yasa ta auke lokaci guda ta yi taga-taga za ta fa i amma ta dake tare da kwarma wani uban ihu,abin ka da farar fata lokaci guda fuskarta ta sunduma domin marin ya gigitata sosai. Amma saboda taurin zuciyarta ta cakume shi ta na ihu ta na zagin sa shi kansa ya yi mamakin kafiyarta,ture ta ya yi ya shige akinsa tare da bugo ofar kai tsaye bayi ya wuce ya sakar ma kan shi ruwa,domin ta ha a mishi zafi kwanyar shi har wani tafasa take yi. Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu ha u a shafi na goma.Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. *FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE* *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_
Chapter 16 · 0% Book details