← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 102

Sashe 14

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *SHAFI NA TARA* Abin mamaki da yake macece wayayyiya sai bata nuna komai ba duk da irin tarin luguden da zuciyar ta take mata,ta na jin kamar ta fita ta sha o shi munafiki kawai haba ya kamata a ce ta ago tuntuni saboda yadda yake yabon ta da kalamai magana aya biyu ya sako sunanta,amma da yake ba ta da wayo sai ba ta ago ba ta danganta kular da yake bata a dalilin ta na kular mishi da yara,sam ba ta yi tunanin zai ce ya na sonta ba ganin basu da komai ar Malam Shehu. Wayancewa ta yi ta na dariyar ya e tace."Haba Mama ni na yi tunanin wani lamari ne me girma yasa kika hana ta,amma akan wannan aramin abin zaki hana ta,in dai a kan wannan ne karku damu ai gara ya auro wacce na sani da ya auko min wata.Kuma karku manta shi fa mijin mata hu u ne,don Allah karku ce zaku hana mishi aurenta." Yanayin yadda take maganar ya nuna da arfin hali kawai take yi,amma ta na arin alo dariya. "Haba ar nan ai ana barin halas don kunya kawai ya nemi wata,amma Juwairiya ba tsarar auren sa bane." Anty Naja ta dage ta ri e kishinta ta na ba ma Mama baki akan ta ha ura ta yadda ayi auren,sannan ta ora da ko ba zasu bashi ba don Allah Juwairiya ta dawo aiki. Daga arshe ta yi ma Mama sallama ta fita har ta na tonon Juwairiya ta fito tare suke da angon ta yazo biko,ita dai ba tace komai ba a ranta take mamakin wani irin hali take dashi.Bayan ta jaddadawa Juwairiya tazo aiki ta yi musu sallama ta fita. Bayan ta fita ta bu e murfin mota ta shige tare da ha e girar sama da asa a ranta ta na mamakin raina mata wayo da ya yi wato ya turo ta ta yi mishi bikon budurwar shi,bayan ta sheda Juwairiya yarinyar kirki ne sai tace amanarta suke ci. A yadda ya ga yadda ta fito sai hankalinsa ya tashi don bai yi tunanin za su gaya mata abin da ke tsakanin sa da ita ba,sai ya yi dana sani da tuntuni ya tare ta da maganar. Bayan sun fara tafiya ya kalleta yadda ta ara cin magani fuskarta ba rahama yace cikin arfin hali ya yi mata tambayar."Ya take ko ba ta jin da i ne?" Haba kamar jira take ya yi tambayar lokacin da take kallon waje ta fara bala'i in da take shiga ba nan take fita ba tace."Munafiki da zamu taho ai da ka gaya min biko zan je na yi maka.Da ma amanata kuke ci kai da ita da ta amince ila sai dai in ji ta tare a gidana ko." Nan ta alle ta na gaya mishi kalamai zafafa mara sa da in ji,in da take shiga ba ta nan take fita ba a hanya ta zage shi tatas! Ta yi mishi wankin babban bargo.Shi dai shiru ya yi mata don ya san ya ibo ruwan dafa kansa kuskuren shi aya da bai sanar mata ba,kuma bai auka su Juwairiya za su yi su ul da baka su gaya mata ba. A haka suka kwana sam ba ta barshi ya rintsa ba,shi kan shi bai san ta iya rikici ba,sai ayau ya san ta na da zafi mata da kishi humh ba'a magana. Washegari Juwairiya ta na zaune ba ta da ninyar zuwa aiki amma Mama ta matsa mata akan taje.Sai dai yadda ta ga gidan ta san ba su kwana lafiya ba. Tun daga falon take kallon yadda ya hargitse ko ina an birkita shi sai gabanta ya fara fa i ta san cewa a kwai wani girman lamari da ya faru. "Munafuka kema me ya kawo ki gida!Maza fita matsiyaciya me kwacen miji kawai,in banda ke jahila kina ar talaka za kiyi tunannin mijina zai aureki."Anty Naja take magana cikin zafi sannan ta ora da cewa."Fita kar na ara ganin ki a gidana,sai abi wani sarkin amma mijina yafi arfin ki. Ko da ta dawo ta sanar ma Mama tace."To shikenan Allah ya sa haka yafi alkhairi.Hankalin Baba Sani ya kwanta ganin Juwairiya ta bar aiki kullum ta na gida,hakan sai ya yi masa da i musamman da yake tunanin yanzu komai zai kwa e musu. Juwairiya ta yi tunanin Baban Abnaj zai biyo bayan ta,amma shiru kake ji Malam yaci shurwa wato matarsa taci arfinsa.Ganin haka sai suka kama sana'a sosai da ku in da Baban Abnaj yake basu,yanzu har abincin siyarwa suke yi Ibrahim ya na kai wa ofar gida.Kuma suna samu ba laifi don da shi suke cin abinci. ********* Kimanin shekaru hu u da auren su suna zama cikin so da aunar juna,sai an sa anin da ba'a rasa ba a tsakanin ma'aurata.Kullum A.m ya yi kasa e ya ji Zainab tace mishi ta na da ciki amma hankalinta ba shi a gurin tunna ba ta ta a yi mishi maganar baby ba. Lamarin sai ya fara damunsa musamaman da annin shi da sa'annin shi suna da yara,amma shi matarsa ko atan wata ba ta ta a yi ba. Sai kuma Allah ya auki son ara ya ora mishi in ya gan su kamar ze zare.Ya na matu ar son yara kullum ya na hanyar gidan an'uwan shi ya na manne da yaransa.Daddy in shi ya fara orafi ya na tsoron kar A.m ya auko rashin haihuwa sai ya fara mishi orafi sosai kullum ya na kiran waya akan suje likita ya duba su. Ganin yadda ya auki son yara ya ora ma kansa sai Zainab ta yi gum da bakinta ba ta ta a su utar baki ta nuna mishi ita ce ba ta son ta haihu take shan wayoyi ba. Sun an fara samun sa ani yadda yake kwaso yaran an'uwan shi ya kawo gidan ya siyo musu kayan wasa.Ranta aci yake sosai ta na ganin hakan kamar takuratawa rayuwarta ne,duk yaran da ze kwaso ba ta musu komai sai masu aiki.Gaskiya Allah ya jarabce shi da son yara sosai. Wataranar Alhamis Zainab ta tashi da ciwon ciki kamar za ta mutu,hankalin A.m ya tashi matu a ganin a sume ya auke ta ya saka a mota suka nufi asibiti. Bayan an kar e ta aka yi mata an gwaje-gwaje tare da turata akin hoto,duk abin da ake ta na kwance kamar gawa ba ta san in da kanta yake ba.Likita ya gano mahaifarta ce ta samu matsala sakamakon tarin wayoyi da ta din ga inkira ma kanta masu arfi na hana haihuwa.Wanda sakamakon haka mahaifar na gabda ru ewa in da likitan ya ba A.m shawarar ayi mata aiki a cire mahaifar. Tsananin tashin hankali A.m ya shige shi ya din ga kallon likitan kamar arya ya yi mishi."Me yasa Zainab za ta aikata hakan?Hakan na nufin ba ta son shi ne har take shan maganin hana aukar ciki don kar ta haihu?" Irin tarin tambayoyin da yake yi ma kansa kenan amma ba shi da amsarta,daga bisani eshe zuciyarsa ya yi kan aryata likitan ya san Zainab ba za ta aikata hakan ba,musamman yadda ta ga Daddyn shi ya mutu akan ya ga ya haihu,sannan yadda yake nuna mata ya na son ta haifa mishi baby ta na nuna masa Allaha ne be kawo ba.To hakan na nufin yaudararsa take. Sai ya yi zuru ya na kallonta da take saukar da numfashi cikin rashin haiyaci ta na bacci,sakamakon allurar baccin da likita ya yi mata.Sai ya shafi fuskarta ya na me tausaya mata halin da ta shiga. "Gaskiya ban yadda da maganar likita ba ina ta ya ya zan rayu ba tare da na ga an cikina ba,duk da na san Allah ya ba jarabtar bayinsa amma gara wata jarrabawar ba wannan ba.Ya na ganin halin da Daddy in shi yake shiga saboda rashin a duk dukiyar da ya tara ya tafi a banza.In in haka ne ya zan yi da shares in da na saka ma yarana tun kafin su zo duniya a asashen waje. Nan take zuciyarsa ta i amincewa da abin da likitan ya fa a duk da ya san asibitin su wararru ne. Kusan awa aya ta na baccin wahala sannan ta bu e idanunta.Da sauri ya ri e mata hannu ya na shafar kanta."Kin tashi babyna sannu. Yace ya na arin temaka mata tashi ta zauna. Bayan ya ha a mata tea ya ba ta tasha ta lumshe idanunta ta na ji har yanzu wani abu ya na karta mata a cikinta,ita ka ai ta san irin tarin azaba da ra in da take kwankwa "Ya jikin sannu kin ji abin da likita yace game da ciwon ki?"Ya tambayeta da murya mai sanyi ya na gyara mata aurin ankwalin ta da yake son ya warware.Ba tare da tunanin komai ba tace."A'a hubbina."A ta aice ta ba shi amsar don ba ta son dogon surutu. an ja numfashi ya fesar ya jinjina girman lamarin baya so ya gaya mata,bai san yadda za ta kar i lamarin ba cewar ba ta haihuwa mahaifarta ya fara ru ewa wanda dole sai an yi mata aiki.To amma ya na son ya gane shin da gaske ita tasha maganin hana aukar ciki har ta illanta musu kanta,ba yan haka da ya bari sai ta warke. "Likita yace ba zaki ta a haihuwa ba yanzu ma mahaifarki za'a yi miki aiki a cire."Yace da ita ya na son yaga yadda za ta i lamarin. "Inna lillahi.Tace tare da bayyano wani tashin hankali a fuskarta nan take fuskarta ta sauya sai hawaye,ta yi asa da kanta ta na son ta yi magana amma ta kasa sai hawaye dake ta gasar sauka a fuskarta.A zuciyar ta kuwa illa tarin nadama da fa in"Na cuci kaina!" "Ina son na sani da gaske ke kika illan ta mahaifar ki Zeey sabosa bakya son ki haihu da ni,ko dama ba kya sona ne ko a kwai wani udiri a ranki."Yace bayan ya yi asa da kan shi dai-dai da kunninta saboda baya son aji me yake fa Ta dago ta kalle shi fuskarta cike da hawaye ganin yadda fuskarsa ya bayyana da tashin hankali,don in ba ta yi arya ba har hawaye
Chapter 14 · 0% Book details