Sashe 85
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 32* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM " Don Allah Abba ka tashi kar ka mutu?" A.m ya fa a sannan ya yi kan sa da sauri,take wani irin nadama ya shige shi. "Mahaifiyar sa umma ta zabga mishi mari, cikin acin rai ta nuna masa hanyar waje,idanuwanta suna zubar hawaye. " Fita daga gidan nan ba na son ganin ka! Sannan ba na burin na ara tozali da kai Abdul,ka cuce mu ka zubar da tarbiyar da muka ba ka,Abdul karuwa fa ka ije a gidan ka?" Kawai sai ta saki razanannen kuka ta kifa kanta jikin Mahaifin sa, tana wani irin kuka mai cin zuciya. A.m da ya ji matsanancin tashin hankali ya kauda kan sa,ga barin kallon Juwairiya da ta rintse idanunta,tana jin wani irin una mara misaltuwa a zuciyarta jin ana kiranta da sunan karuwa. A.m ya bu e bakin sa zai yi magana,daidai lokacin da Daddy ya ibo ruwa, ya yayyyafa ma mahaifin sa a jiki. " Ba na son na ji muryar ka na tsane ka A.m ka fita nace! Wane ido kake son mu kalli iyayen Zainab,da ka tozarta mu a gurin su,bayan ka ije karuwa sannan ka yi ma ar su duka,tun da nake da kai,ka ta a ganin mahaifin ka ya auki ko da tsintsiya ya buge ni da shi?"Ta ce mi shi cikin tsigar tambaya. "Momi na tuba ki yafe min amma kin san ba zan ta a aikata zina ba,Momi ba halina ba ne k..." " Ka tashi ka fita na ce banza mara tunani!Haka kake son annin ka su yi?" a wa ya yi da nufin ya kama afafunta,amma sai ta janye,da sauri tana mi shi wani mugun kallo. " Maza ka fita da wannan abar mara hankali kawai, ka rasa macen da za ka kula sai ar talaka azamiya tir! Wallahi ka zubda ajin ka." A.m ya mi e cikin dana sani ya kama hannun Juwairiya da ta ji yau ta tsani kanta fiye da kullum,ta muzanta iya muzanta tana jin kamar ta nutse a asa,ganin yadda mutanen gidan suke kallonta tamkar sun ga kashi.Fara tafiya ya yi da ita yana jan hannunta. " Wayyo Allah na shiga uku ya zan yi da raina wai yau an da na ba ma tarbiya ne! Yake ri e da mace maccen da ba muharramin sa ba." Sai ta fashe da kuka mahaifin sa kuwa tun da ya fa i,bai ara cewa komai ba sai kallon A.m da yake yi tamkar bai san shi ba. " A.m dawo mu yi musu bayanin ita in matarka ce ba yadda suke tunani ba,mu daina oye oye mu gaya musu gaskiyar komai." Abba da ke kwance ya mi e cikin mamaki ya ce." Na lura baku da hankali dukan ku,ta ya ya za'ai ya yi aure ba tare da sani na ba?" Ya tambaye shi cikin tsananin mamakin sa ya kuma kalli Daddy da ya yi fuska sosai,ganin ana muzanta mi shi shalelen sa. " Mai ya sa za ka tambaye ni dalilin auren sa bayan ka mallaka min shi halak malak?" Abba ne ya harzu o gani yake kamar Daddy ya raina mi shi wayo,don haka cikin fusata ya cakume shi. " Ba ka da hankali ne?Kai da shi duk kun zare! Duk da na ba ka shi kyauta,ai kwarmin ido ba ramin ba ne,in ba ka sanar da ni auren sa ba,ka gaya ma mahaifiyar sa da ta yi rainon cikin sa har na tsawon wata tara,ta kuma yi awainiyar shi." Sai Daddy ya din ga kallon sa cikin wani irin kallo yana matsawa,yayin da idanun shi suka fara zubar hawaye,ya kalli A.m da hankalin shi in ya yi dubu to ya tashi,ganin tun da yake bai ta a ganin iyayen na sa sun yi ko da sai in sa ba. " Allah na gode maka da ka san da ni a duniyar har ka jarabce ni da rashin haihuwa,yau ga an'uwana wanda muka fito ciki aya da shi ya yi mini gorin a,ya nuna ban isa da an shi da ya haifa ba,wanda na yi tunanin yaransa duka mallakina ne." Da baya baya yake tafiya yana zubar hawaye, duk da ya san abin da A.bba ya ce gaskiya ne,bai kyauta ba da ya biye masa aka yi auren ba tare da sanin su ba,amma ya ji zafin gorin da ya yi mishi sosai ya ji una a zuciyar sa fiye da tunani. " Amma ka san ba ku kyauta mana ba,haba ta ya ya zai yi aure ba mu sani ba,sannan ya ije matar sa a gidan sa,kuma ba tare da matar sa ta sani ba?Anya kana ganin ganin kun yi mata adalci kuwa?Sannan ya rasa macen da zai so sai yar talaka mai zai yi da ita" Ya numfasa ya ja numfashi yana kallon sa sannan ya ora da cewa." Yarinyar nan ar aminin ka ne,kana ganin bai tozarta ka ba ka duba iri tashin hankalin da mahaifinta ya yi maka."Ya ce yana kallon sa. " Tabbas ar aminina ne kuma na san haka,amma ka sani duk abin da ya faru ita ta jawa kanta,da fari da suka zo da maganar korar su na yi na i yadda da maganar su,amma da ga baya A.m ya gaya mini,ita Zainab in ce ba ta haihuwa sannnan kuma ta saka shi dole ya yi mata,al awarin kar ya yi mata kishiya,bayan duk abin da ya faru ita ta ja ma kanta,saboda mugun son duniya. Saboda haka na amince bayan na duba irin uncin da nake shiga sakamakon rashin haihuwa,wanda yau gashi kai ma da kake an'uwana ka goranta mini."Ya tsaya da maganar domin ya huta ka Abba da sauran mutanen da ke tsaye cikin mamaki suke kallon Daddy,suna al'ajabin wannan maganar da ya tayar da hankalin su. " Ganin na i yadda da maganar amma sai A.m ya nuna ya ha ura,wanda ni na i yadda ne kan ya canza haukar maganar da ya yi mata,na ba zai ara aure ba,amma sai ya nuna sam shi ba zai ara aure ba,saboda haukar so da ya rufe mi shi ido. "Na amince A.m ya aureta ne saboda in har ba ta hakan ba, a yadda ya nuna ba zai ta ara aure ba,ni kuma ba na son ya rayu ba tare da ya ga an sa a duniya ba,sanan in na fito fili na nuna kan dole ya ara aure ban san ya mahaifin Zainab da ita za su auke ni ba."Ya arashe maganar cikin mutuwar jiki yana ara goge sauran hawaye da yake ma ale a fuskar sa. Ya kama hannun Abba ya ri e sosai tare da sakin kuka ya ci gaba da cewa." Ka yafe mini amma yau ka nuna min iyaka ta,na san in da zan tsaya akan yaran ka,amma ka sani ba laifi na yi ma Allah ba da ya hana ni haihuwa,kullum ina godiya ga Allah da ya yi mini tarin ni'imomi a rayuwa." Abba da jikin sa ya yi sanyi sosai ganin an'uwan sa ya yi fushi sosai,shi kan sa ya yi dana sanin maganar da ya gaya masa,wanda hakan ya faru sakamakon acin rai da dokin zuciya,sannan ya yi ba in cikin abin da su yi haba sai ka ce shi bai fi su hankali ba,amma kuma duk abin da an'uwan sa ya yi masa bai kamata ya yi masa gorin haihuwa ba,duk da cewar bai san lokacin da maganar ta fito ba,don magana zarar bunu ce. Dukkannin su sun cika da mamaki iya mamaki da gaske A.m yana haihuwa ya yi musu aryar haka,don kawai ya faranta ma mace bayan ya san in da ace shi ne baya haihuwa da ba za ta zauna da shi ba. Mahaifiyar sa ta zo gaban sa ta din ga kifa masa mari, har sai da anin sa ya janye shi daga gurin. " Ka cuce mu sam ba ka yi mana adalci ba!Kasan iya tsawon lokacin da na auka ina tashi cikin dare,akan Allah ya sa ka sa a.Kusan kullum sai na yi maka addu'ar ya kauda matsalar da kake da shi,ina tunani da tsoro a kwai ranar da Zainab za ta yi maka tawaye ta rabu da k...."Kawai sai ta ara sakin kuka da arfin ta. Abba ya kalli Juwairiya da ta gaji da tsayuwa afafunta har rawa suke yi,ya kuma juya idanun sa ga Daddy da har yanzu yana jin babu da i akan maganar da Abba ya yi masa. "Ka yi ha uri ka yafe mini na san na yi kuskure da na gaya maka haka,musamman da na riga na mallaka ma shi duniya da lahira,amma abin da kuka yi kamar ba na masu hankali ba,ga in da abin ya kai ku." Ya yi shiru ko Daddy zai ce wani abu amma sai ya ga ya aure fuska don haka ya ci gaba da cewa. "Kuma sai ya rasa wacce zai aura sai ar talaka har da kai ka biye mi shi?Haba ta ya ya za'ai kamar shi ya auri ar talaka.Ai wannan kamar ya zubar mana da mutunci ne b...." "Wannan kuma sai ka tuhume sa domin cewa ya yi zai aure ta, su rabu bayan ta haihu ya ba wa Zainab yaron.Wata ila son ta yake shi ya sa ya yi mini aryar haka." Da sauri A.m ya kalli Daddy ya ce." Ba sonta na ke yi ba Daddy da gaske nake yi,yaron Zainab zan ba ta ri e ita kuma za mu rabu bayan ta haihu,saboda mahaifiyar ta ma ba ta san tana auren ba." " What mene kake cewa Abdul! Anya kana da hankali kuwa."Mahaifiyar sa ta ce cikin tsananin razana. A.m ya cire tsoro ya gaya musu duk abin da ya faru har auke Mama sai da ya fa a musu,da yadda Baba Sani ya takura wa rayuwar su,da dalilin da juwairiya ta amshi auren sa,sannan kuma ya yi al awarin tana haihuwa zai rabu da ita. Umma ta din ga mata wani irin kallo na mai kama da tausayi ko akasin haka. " Sam ba ki yi ma mahaifiyar ki adalci ba,duk da cewar kin yi hakan don ki ce ci rayuwarta,amma ta ya ya za ki yi aure ba tare da sanin mahaifiyarki ba?Gaskiya wannan babban kuskure ne da kika aikata,saboda mahaifiyarki Allah ka