← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 102

Sashe 46

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fushi nake dake har na fito cikin hotel in da nufin na auki mota na auko ki,sai ga shi kin kira ni in bar shi mijin Fati ya turo muku direba shi ya sa na karyo mota na dawo gidan tunna matar gidan ta dawo." Ya fa a ya na kaida kansa gefe shi kansa ya na mamakin kansa. Zainab murmushinta ya aru ta na jin wani irin girman kai da alfahari da mijinta da take yi,sai ta kama shi ta rungume ta na fa in."Ina sonka Habibina ni na san ba za ka iya rabuwa da ni ba,ko ce wa da ka yi na bar maka gidan ka kana fa i ne kawai amma ni da kai mutu ka raba." " Tabbas Zainab maganarki dutse da sai dai ki taho asibiti jinya."Ya fa Dariya suka yi duka ya rufe su da bargo ya kasheta da soyaryar shi sannan ya sa ta baccin dole,saboda ya sakin mata nauyin shi wai dole sai ta kwanta sun yi bacci,duk da ba shi take ji ba. Kallonsa take yi yadda yake saukar da numfashinsa a hankali,daga gani baccin na kai mishi karo ita kuwa ta kasa baccin saboda wani irin yunwa dake wularta,saboda rabonta da abinci tun daren jiya ta kasa ci ta na fargabar yadda za su kwashe da shi. Shafa fuskarsa ta yi da yake ta she i da kyau ta na mamakin mai ya hana shi bacci,sai kuma ta danganta hakan da ce mata da ya yi ba'a gida yake kwana ba ila ya kasa bacci ne. A.m da fari baccin arya yake yi ya saka mata nauyin jikinsa don kar ta ce za ta bu aci abinci, ta je gurin Juwairiya don ya san a halin da take ciki ba yadda za'a yi ta iya wani aiki a gidan,amma kuma daga ba ya saboda rashin baccin da bai yi ma wannan mai kukan tsiyar da ta hana shi bacci sai bacci ya kwashe shi. Da Zaina b ta gaji da juyi a gado ta bubbuga shi ya an bu e ido ya na kallonta. " Gaskiya ka tashi ni fa na gaji da baccin nan yunwa na son ta yi min lahani." Ta fa a ta na jan shi ya sauko shahada ya yi ya sauka tare da mi a da salati,ya shige bayi ganin haka ita ma ta sai ta wuce akinta ta shiga bayi wanka ta yi ta zira duguwar riga,suka fito falo suna taku a jere sai kace ba su suke ta fa a ba. ************ Juwairiya kuwa bayan ta gama jin wayar da A.m yake yi da Zainab ta shiga tashin hankali matu a! A wannan lokaci ji take kamar ta bu e ido ta ga ba ta a doron asa kuka take yi sosai na rashin abu mafi girma a rayuwarta,wanda Baba Sani ya so ya yi galabar raba ta da shi dama mutane da dama amma ta yi ya i tukuru,ta ada na abin ta sai ga shi yau ta siyar da shi saboda ku i ta na shan wula anci ba tare da an daraja ta ba. Ta rintse idanunta ta na jin wani irin ciwo mai ra i a zuciyarta yayin da wasu tarin hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta. Cije bakinta ta yi lokacin da ta mi e ta na jin wani irin azabar ra i ya na zagaye duk ilahirin jikinta. A hankali ta fice daga akin ba tare da ya sani ba jin matar so ta dawo yayin da hankalinta ya tashi,amma ta wani gefen ta na jin ina ma ace Zainab ta riske su a wannan yanayi koma mai zai faru ya faru,don ta gaji da tarin ra in azabar da take kur ar ruwan ba in cikinsa a cikin rayuwarta. Ta na shiga aki sai ta fashe da kuka sosai har ta yi mai isar ta sannan ta rarrafa ta shiga bayi ta gana ma kanta,azaba da ruwan zafi don ta rage ma kanta ciwo da nauyin da jikinta ya yi. Bayan ta yi wanka ta fito ta yi sallah a zaune sai bacci mai ha e da zazza i ya kama ta wanda fa an su ya tashe ta,ba wai don ta gaji da baccon ba tunna duka yaushe ta kwanta sai dai ta ji da in baccin don ya an rage mata wani unci daga cikin damuwarta. Ta din ga jin hayaniyar su da kukan Zainab har da saukar marin da ya yi mata. Ta saka hannunta ta toshe kunnin ta amma sai ta ji sun sauko asa suna ta fa a sosai,ya fa a ta fa a sam babu tsari a rayuwar auren su don ba sa daraja juna. Gabaki aya sai ta auki laifin ta ora akan A.m wanda yanzu take jin haushin sa fiye da komai a rayuwarta,ga wani irin kishinsa da ya ara ninkuwa a ranta mai girma wanda take jin kamar ta illata duk wadda ta ra e shi. Ta na jin suna fa a daga bisani ta ji shiru sai muryar namiji ta ji ya na sasanci,wanda daga baya ta game mahaifin A.m ne. Sasancin da aka yi a tsakanin su suka koma ciki shi ya ba ta damar yin baccin wahala,duk da ta san ya kamata ta shirya ma mutanen gidan abinci,sai dai ba za ta iya ba saboda jikinta da ko ina yake mata ciwo. A tare suka sauko asar sun ci gayu sosai an sha kyau. Zainab ta tsaya ta na kallon dinning cike da mamaki ganin ba komai wayam. Ta kalli A.m ta na fa in." Ina wannan wawiyar take ba ta shirya min abinci ba duk da na kira ta ba auka ba na tura mata da text." A.m ya da gaban sa ya fa i amma sai ya ta e bakin sa ya ce. " Ina zan sani ko kin bani ajiyar ta ne?Ni da ba'a gida nake kwana ba." Ya fa a ya na wani cin magani har da an harara yake sakin mata. wala mata kira ta yi sau uku sai ga Juwairiya ta fito a wani yanayi ta na jan afarta. Da masifa Juwairiya ta kalle ta ta fara magana da ce wa." Ina abinci na kuma gidan uban wa kika shiga na kira wayar ki na gaya miki zan dawo amma baki auka ba." Ta fa a tare da tsare Juwairiya da ido kamar ta na son ta gano dalilin aga wayar da ta yi. Juwairiya ta saci kallon A.m da yake zaune a aya daga cikin kujerun dinning ya na danna waya,kamar bai san da mutane a gurin ba amma kuma a zahirin gaskiya hankalin sa na gurin su ya na son ya ji mai za ta ce,yayin da gaban sa yake fa i duk a tsorace yake sai dai ya yi ta maza ya dake. Juwairiya ta mai da kanta asa hawaye na bin fuskarta jikinta har kyarma yake yi,saboda har yanzu zazza i take ji,ita kanta ba za ta ce ga in da wayarta take ba don rabon ta ita tun jiya da ya ce ta gyara masa akinsa. " Ki yi ha uri wayata ba caji na gaya ma maigadi ya kunna jannareto don ba wuta,amma ya i tashi sannan na so na kunna sola sai dai ban iya ba ina gudun kar na ata na ha ura k....." " Rufe min baki n banza da iya jahila solar ce kika kasa kunnawa abu a rubuce ba na tunanin kin yi firamari,ni tsoro nake karki din ga ona min kayan wuta ko ki ta da gobara ai dai yi asarar ku in tara wallahi.To uban me ya hana ki yin abinci." Zainab ta ce ta na hararar ta don ranta ya ace ta so ta samu abincinta da ta yi rashin sa na kwana biyu mai da i da,shi ya sa ta i sakin jikinta ta ci abinci da za ta taho. Wannan karon A.m ya yi tsubbul da bakinsa ya ce." Wa za ta dafa ma abincin ni da na gaya miki a hotel na ke kwana ita da masu aiki ne kawai ila sun yi sun ci,tunna ba ta san za ki dawo ba." Ya ce cikin sauri ya na tsoron kar ta yi kato ara don ganin ta fara kuka. Juwairiya kuwa gwalalo idanunta ta yi ta na kallon sa jin aryar da ya shirya mata. Karab! Kuwa suka ha a ido kowa ya yi saurin auke kansa. A.m sai da ya sakin mata harara sannan ya auke kansa,Juwairiya kuwa wani irin kunyarsa ya kama ta ta rintse idanunta da sauri. " Ke." Ta daka mata tsawar da ya firgita ta." To uban wa kike ma kuka daga tambayarki?Maza ki je ki ora min abinci yunwa nake ji kuma ki kawo min abun da zan iya ci kafin ki ora girkin." Sai hawayen Juwairiya ya ara zarya a fuskarata ta kalli Zainab ta ce " Don Allah ki yi ha uri bani da lafiya zazza i nake ji,ba zan iya girki ba." Ta fa a cikin muryar da ta bayyana irin kukan da ta sha tun daren jiya. Zainab ta harare ta ta ce." Allah ya sa mutuwa za ki yi amma sai kin yi min abinci kin san yunwar da nake ji maza wuce.Kuma ki kawo min abin da zamu ta a ni da zauji." Ta zauna tare da aukar remote ta kunna kallo ta na karka afa ta na jan A.m da hira wanda ya kasa ko da tari ne ya na ta kallon fuskar wayarsa,da ya kasa auke idanunsa a kanta bayan babu abin da yake yi. Juwairiya na shiga ta ha a kanta da bangon kicin in ta na kuka sosai take jin jikinta ba da Ta da e a haka sannan ta soya dankalin turawa da wai ta kuma ha a musu da tea mai kauri ta kai musu,ta na tafiya tamkar wacce wai ya fashe mawa a cikin ta. " Ok maza ki je ki ha a mai nauyi don wannan ba zai osar da ni ba." Ta ce mata ba yan ta ije mata ba tare da ta kalle ta ba. "Anty Zainab ki yi ha uri ba ni da lafiya don Allah sa..." Mari ta wanka mata a fuskarta da take
Chapter 46 · 0% Book details