← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 102

Sashe 67

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 26* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM A cikin motar da suka zo da ita suka sakata,sun yi tafiya mai nisa gaske sannan suka tsaya. Duk nisar tafiyar da suka sha amma Mama da Ibrahim ba su farfa o ba. Wani aton gida suka shiga da su tare da kwantar da su,sannan suka fice daga gidan. Kusan awa aya Mama ta yi sannan ta farka cikin tsananin razana tana salati.Ta kalli in da take yayin da take tsananin mamaki,idanuwanta suka firfito tana mamakin in da ta tsinci kanta. Ibrahim dake kwance ta rungume tana jijjiga shi,cikin tashin hankali tana mamakin ganin ta a wannan gida. Ko da ya bu e ido sai ya cika da tsananin mamaki ya kalle ta ya ce. "Mama ina ne nan kuma mai ya kawo mu wannan gida?" Mama dake cikin tashin hankali ba ta ba shi amsa ba,sai mi ewa da ta yi tana arewa gidan kallo. Duk da rashin arfin jikinta amma haka ta mi e ta kama hannun Ibrahim suka fito waje. " Madam lafiya ina za ki je." Ta ji muryar wani mutum wanda yake tsaye a get in gidan,ya na sanye da kakakin sojoji da bindiga auke a hannunsa. Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa da tsoro a fuskarta. " Waye kai kuma mai ya sa kake tambayata?Zan koma in da kuka auko ni." Ta ba shi amsa da muryar tsoro a fuskarta,tana ja da baya saboda ta tsorata warai da ganin sa. " Madam ki yi ha uri oga bai ba mu izinin ki fita ko da ofar gida ba ne." Ya ce cikin aure fuska ba tare da ya kalle ta ba,balle ya ga tashin hankalin da ke auke a fuskarta. " Waye kai mene ne ha ina da kai har za ka ce ba zan fita ba,sannan waye agan ka ina ruwana da shi." Ta jera masa tarin tambayoyin da take tunanin ba zai amsa mata ko aya ba. " Wannan kuma sai ki jira har sai ya zo ki yi mi shi tambayoyi,amma ba ni da masaniya ina kan aikina ne kawai. Mama da fari ta auka wasa yake mata amma da ta dage kan dole sai ya bu e mata,sai ta ga ya aure fuska ya aga zungureriyar bindigar sa,ba tare da ya ara kallon ta ba. Da sauri ta kama hannun Ibrahim suka koma ciki,saboda ta tsorata da shi gani take kamar zai harbe ta. " Inna lillahi! Wai me ke faruwa ne na kasa gane komai ya Allah ka fahimtar da ni,na san cewa Baba Sani ba zai ta a killace ni a gidan nan ba don kawai na bu aci Juwairiya ta dawo." Ta fa a cikin tashin hankali tare da rashin madafa tana ji kamar ta yi hauka. " Ina Juwairiya mai ya sa ita ba'a taho da ita ba?" Ta tambayi kanta da tsananin mamaki yayin da ta rasa ta in da za ta fara tunani,domin lamarin ya aure mata kai sosai. " Ko masu garkuwa da mutane ne suka sace mu?" Ta fa a tana kallon Ibrahim da ya cika da mamaki ya na kallon daular gidan da aka kawo su. A jiyar zuciya ya yi mai nisa sannan ya sauke tagumi ya kalli Mama,da fuskarta ya nuna tsantsar tashin hankalin da take ciki. " Ba na tunanin za'ayi garkuwa damu har gida sannan aka wo mu cikin wannan daular Mama! Ki duba irin wannan gidan na masu ku i ne sosai.Ni dai ina zargin a kwai wata a asa.Tabbas a kwai lauje cikin na " Haka ne Ibrahim zuciyata ta fara hasasomin haka,sai dai ina zargin duk abin da ya faru a kwai saka hannun Baba Sani a ciki.Zuciyata ta fara zargin in da ya tura Juwairiya ba alkhairi ba ne,sai dai ina an jin sanyi ne, in na tuna da Juwairiya yarinyar kirki ce,na yadda da tarbiyar da na ba ta sam ba na tunanin za ta aikata abin da nake zargi,duk da cewa ba'a shedar an yau." Hannu ta ora a ka yayin da gabanta ya fa i ras!Sa'ilin da wani tunani ya fa o mata. " Kar dai a ce Baba Sani ya yi mini arya ne akan aiki zai kaita,ya saka ta a hanyar banza?" Ta tambayi Ibrahim da take tunanin bai fahimci abin da take nufi ba. Mama ta saki ara tare da zubewa a asa tana fa in." Ya Allah na kasa samun natsuwa zuciyata,na shiga ru anin halin da Juwairiya take ciki,kar a ce Baba Sani ya ata mini tarbiyar da na gina ta akai,ya saka ta a harkar banza.Kar a ce da ku in da take aikata alfasha muke ciki." Sai ta girgiza kanta tana kuka da arfi ta ci gaba da fa in. " Iya tsawon yaushe zan zauna a wannan gidan ba tare da na san gaskiya ba,in har Juwairiya ta canza tarbiyar da na ba ta tabbas ba zan iya yafe mata ba,domin na ci burin na ga na aurar da ke Juwairiya kar ki yi mini haka." Da sauri Ibrahim ya taso ya rungumeta yana rarrashi ganin tana son ta fita hayyacinta. "Mama mu bi abin da sannu-sannu kar ki aibata ta,na san cewa sam Anty Juwairiya ba za ta aikata haka ba,tabbas a kwai abin da ke faruwa.Kuma duk wanda ya sa aka kawo mu cikin wannan daular,to a kwai saka hannun Baba Sani a ciki don zuciyata ba ta yadda da irin sanyin da ya yi ba,lokaci guda ya zubda duk wani makaman sa akanta." Mama ta shiga cikin tsananin ru ani warai ta yi ihu ta yi kuka,tana ro on mutumin da ya taimaketa ya gaya mata abin da ke faruwa,amma ko kallon ta bai yi ba don ba'a ba shi izinin haka ba,bayan haka shi bai san komai game da lamarin da ya faru ba. Ganin irin kukan da Mama take yi tana kiran sunan Juwairiya ta i shiga cikin gidan,a farfajiya ta tsaye tana kuka sosai ya kalle ta ya ce. " Hajiya ba ni da nufin na cutar da ke gara ki koma ciki,don wallahi ko kukan mutuwa za ki yi ba zan bu e miki ki fita ba. Jin haka Mama ta ara sakin wani kukan ta zauna a gurin ta i motsiwa,sai kuka da take yi domin kanta ya kulle. ***** A ranar da aka auke su Mama Juwairiya ta yi wani irin bacci mai nauyin gaske,ba ta tashi ba sai da ta auki tsawon lokaci tana bacci mai kama da na mutuwa. e idanunta ta yi cikin tsananin mutuwar jiki don ji take ko an yatsa ba za ta iya agawa ba. Sai da aka auki tsawon lokaci sannan ta samu ta iya tashi zaune. aga idanunta da ta yi ta kalli agogon da ke manne a bangon akin,da gudu ta mi e tana salati saboda tunawa da ta yi ko sallah ba ta yi ba. " Na shiga uku mai ya faru yanzu fa arfe aya har da kwata,wane irin bacci na yi ko dai mutuwa na yi na dawo?" Ta tambayi kanta domin wannan bacci da ta yi bai yi kama da na lafiya ba. Da sauri ta mi e ta shige ba yi tana tunanin to wane sallah ya kamata ta fara. Bayan ta idar da sallah sai ta yi sauri ta ruga zuwa falo,saboda kiran curoma da cikinta yake yi.A haka dai ta arasa tana mamakin jin gidan ya yi shiru,kamar ba mutane a gidan. Ta shiga cikin tsananin tashin hankali da ta duba lungu da tsa o ba ta gan su ba ,sai ta fara kuka da salati tana dubawa cikin tsoro.Ta auki tsawon lokaci amma ba ta ji uriyar kowa ba. Tana tsaye a farfajiyar gidan motar Baba Sani ya sawo kai.Da sauri ta arasa gurin shi cikin muryar kuka don tunaninta ya fara ba ta yana da saka hannu na rashin ganin su,ko kuma shine ya auke su. " Baba Sani ina Mama na duba ko ina ban ganta ba." Wata irin tsawa ya daka mata ya ce."Ku ji min munafuka ban sani ba,duk abin da ke faruwa ba da saka hannunki ba za ki raina min wayo." Zare idanunta ta yi ta ce."Wallahi ba ni da masaniya akan komai mai ya faru?" Kallonta ya yi sai ya matso kusa da ita ya fara magana cikin aga murya." Jiya A.m ya sameni ya ce kun yi da shi zai kai Mama wani gari har zuwa lokacin da za ku rabu,saboda na gaya masa ta kawo min an sanda." Ya fa a ranta a ace da ba in ciki arara a fuskar sa." Wallahi sam ba haka na so ba na so a ce yabar mini komai a hannuna,saboda na yi ba in cikin irin daular da ya kaita." Juwairiya ta ka u da jin abin da ya fa a sai ta saka kuka sosai,ganin yanzu Mama ta san abin da ta aikata. asa ta zauna tare da ara sakin kuka." Na shiga uku ba zan iya ara ga a ido da Mama ba,wane irin kallo za ta yi min wallahi na yi dana sani warai,yanzu idanuwana ba za su ara ganin ta ba har saina haifa mi shi yaro."Sai ta ji hawaye na sintiri akan fuskarta. Sosai ta shiga tashin hankali ta na jin ba za ta ara iya ha a ido da Mama ba,don ta san daga ranar da ta ji abin da ke faruwa za ta tsaneta na har abada. Ganin irin kukan da take yi sosai kamar ranta zai fita a ranta ta na jin ba in ciki matu Baba Sani bai duba halin da take ciki ba ya ce." Ki kwantar da hankalin ki ni kaina na yi al warin saina raba auren ku,in har na bu aci ku i bai ba ni ba,wallahi saina tona asiri komai ya wargatse saboda na tsani ganin ki a cikin wannan daular,in kuma baya haihuwa ne sai ya sake ki don ba za ki zauna da shi ba." Ba ta ce masa uffan ba har ya gama magana ya fice. Juwairiya sai ta ji ba za ta iya zama a cikin gidan ba,domin duhun da ya yi mata yafi duhun abari. Ta yi kuka har ta ba uku lada tana ji wani irin kunyar
Chapter 67 · 0% Book details