Sashe 59
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
in kuma yau ba hau ba duk saina yi maganin ku." Ta fa a da tsamin murya ta na girgiza jikinta kamar ta na da aljanun da gaske. " Na shiga uku kin ji mai take ce wa?" Ta ce da Juwairiya da ta tsaya ta na mamakinta yayin da tausayinta ya cika ranta don ta san ta yi hakan ne don ta koma gida ita ba ta san A.m ya tsoratar da ita bayan wannan. Kama ta yi ganin ta na jijjiga sai hawaye ya wanke mata fuska. Zainab da ba ta ta a ganin wai mai aljanu ba sai ta tsorata ainun take ta kira Anty Fati jikinta na ari ta sanar mata halin da Binta take ciki nan take ta ce bari ta turo direba da mai aikinta su taho da ita don sam iyayen ta ba su yi mata bayani ba. Zainab ta tsorata sosai a ranta Allah Allah take direban Anty fati ya iso,abincin da take ci kasa ci ta yi ta tsaya ta na kallon ikon Allah yayin da jikinta ke ari. Suna cikin wannan halin ya shigo da sauri ta arasa gun shi ta yi masa bayani. Ya kalli Binta da take ka a kai kamar wata adangaruwa ta na zare ido,sai hakan ya so ya bashi dariya amma ya cije. Wata uwar tsawa ya daka mata ganin ta gan shi sai ta razana kamar za ta gudu don Allah ya saka mata matu ar tsoron shi. an natsuwa ta yi amma ba ta daina zare ido ba ita a dole ga mai aljanu. A.m ya kalleta sai ya kauda kansa tare da ta e baki ya ce da Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta na kallon Binta. " Maganin ki kenan da shegen kwashe-kwashen ki ta yi maza ya bar gidan nan ai ga yi nan kin je kin jawo ma kan ki mai almatsutsai." Ya yi maza ya haye sama ya na dariyar yadda Binta take yi sai ka ce wata adangaruwa,saboda in ya tsaya dariya zai kubce masa. Direba na zuwa Zainab ta saka aka kwashe kayanta tare da yi mata ihisani aka wuce da ita. Ta na shiga aki kuka ta fashe da shi na tausayin Binta haka kawai ya yi mata sanadin rabuwa da aikin ta bayan ya san ita marainiyace an ya ya kyauta kuwa. Ta na kallon shi akan mutum wanda ya fiye son kan sa bai damu ba in dai zai faranta ma kansa da masoyiyar sa bai damu don ya cutar da kowa ba. Don haka ko wayar da yake yi da ita in ya fita duk lokacin da Zainab take nan ta i daga arshe kashe wayar ta yi saboda haushin sa da take ji matu ar gaske,don ya faye son kan sa akan komai. Zainab ba ta ha ura da neman mai aiki ba don har ta yi maganar a kawo mata wata. Makarantar da ta fara sai hakan ya yi maata da i sosai ikon Allah kenan duk da ta cire rai sai gashi Allah ya saka ta na da rabon yi.Abin da iyayen gidan ta suka za a mata ya sa ta ara yadda da cewar nufin su rayuwarta ba ta da wani amfani sai dai don ta yi musu hidima saboda girki suka za a mata,ita ta na ganin wani kalar girki ne ba ta iya ba,amma kuma da ta fara karatu sai ta raina kanta don gani ta yi kamar da can ba ta iya komai ba. Ganin hakan sai ya dage damtse burinta ta iya girki ta yadda za ta siye zuciyar A.m,da take jin kamar ana mata wahayin son shi. Duk da cewa makarantar sau uku take fita a sati amma ta na jin da in karatun,sosai fiye da komai ba kamar da da ita ka ai take rayuwarta in dai matar gidan ta na nan. Juwairiya ta yi awa aya a makaranta wacce suka sha u sosai duk da ba su da e ba,sai dai ita matar aure ce har da yaranta biyu. Suna matu ar shiri sosai komai ma su tare suke yi ga halin su ya zo aya ba ruwan su da hayaniya,musamman ita da take kullum cikin bege da aunar masoyin ta. Kimanini wata uku da fara karatun Juwairiya wanda Zainab ta auko an aiki har guda uku sai A.m ya yi tsalle ya kawo auli da ba'adi. Ganin haka sai ta kori Baba in da aka kawo mata mai jini a jika ta na koya mata girkin amma ba ta kwana don ta na da miji sai dai tun safe in ta zo sai magariba take komawa gida. Ranar wata Juma'a Juwairiya ta tashi da ciwon kai mai zafi da zazza i ko tashi ta yi sallah ta kasa ga wani irin sanyi da yake shiga cikin ashin jikinta ya na nu usanta. Abin takaici gashi suna da test don ana gabda yi masu jarrabawa. Ganin ba zata iya zuwa ba gashi matar gidan ba ta nan kuma yau A.m zai dawo daga tafiyar da ya yi,wayarta ta auka tare da duba numbar ta kiran numbar Hauwa Tukur amma wayar ba ta shiga ba sai ta yi tsaki ta jefar da wayar ta kwanta. Ta na kwance jikinta na ara zafi sosai kamar wuta misalin tara sai ga kiran Hauwa Tukur ya shigo,da yar ta janyo wayar da ke kusa da ita ta kanga a kunninta ta na nishi a wahalce. "Hello Juwairiya ba za ki zo makaranta ba ne lafiya kin san muna da test ga shi Malam D.d ba shi da mutunci."Hauwa Tukur ta fa a a ranta ta na tunanin mai ya hanata zuwa,kasancewar ba ta wasa da karatu. " Wallahi ba na jin da i ne kin san sai da lafiya ake komai.Don Allah ki yi min test in in zai yi wu."Ta ba ta amsa ta na kyarmar jiki. Bayan ta yi mata sallama tare da mata al awarin in dai ya yadda za ta yi mata ta kashe wayar ta koma ta kwanta. Sai misalin shidda na yamma A.m ya shigo babu abin da ta yi masa na abinci. Ganin halin da take ciki ya ru e sosai kamar zai yi hauka a tunanin sa ciki ta samu,don haka jiki na rawa ya aga waya ya kira likita ya zo ya duba ta. Juwairiya ta ji hankalinta ya yi ololuwar tashi jin ya kira likita ita yadda take jin ciwon gani take kamar ciki ne. Kawai sai ta ji hawaye ya fara sauka a uncinta don ta san lokacin rabuwar su ya yi daga ranar za su fara irga kwanaki. Bayan likita ya zo ya yi mata gwaje-gwaje ya sa ta yi fitsari ta kawo masa. A.m da ya yi zugum duk ya osa ya ji abin da likitar zai fa a,ya na ta addu'ar Allah ya sa likita ya yi mishi kyakykywan albishir. "Ga wannan maganin za ka siyo maleria ce ke damunta in sha Allahu tasha magani za ta warke." Hankalin sa ne ya tashi matu a kawai sai ya ji hawaye na son ya zubo a uncin sa yayin da zuciyar sa ta karye da tunanin zai samu Jikin sa a sanyaye ya kar i takaddar ya fice tare da likitan don ya siyo magani ko kallon ta da take zaune bai yi ba. Wani wawan ajiyar zuciya ta saki wani irin sanyi ya ziyarce ta jin ba ciki ta samu ba. alla sai da ta yi kwana uku sannan ta warke sarai ta shirya ta tafi makaranta. Suna zaune da Hauwa Tukur ba yan sun fito daga lakca Hauwa Tukur da hankalinta yake kan danna wayarta ta kalle ta da ta zuba uban tagumi ta yi nisa gurin karanta wasi ar jaki. "Yawan tunani ba shi da amfani ga lafiya kuma ban ga dalilin da zai saka ki zo makaranta ki zuba uban tagumi,ba yan kin baro gwarzon ki a gida nifa da kika ce baki da lafiya na auka ciki ne da ke." Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta ta zare idanunta ta na kallonta. "Subuhanallahi ciki kuma ni fa ba matar aure ba ce." Ta fa a tare da gwalalo idanu jin abin da ta fa a yayin da take mamakin mai ya saka ta fa i haka. Sakin dariya mai sauti ta yi ta auki lemun robar da Juwairiya ke sha ta zu a tare da kwashewa da dariya. "To don Allah meye na tsorata haka sai ka ce na ce kin yi kisa." Ta fa a ta na mamakin yadda ta razana haka saboda ta ha ance ma kanta ita matar aure ce,sai dai in ba ta son ta ga ya mata amma ko wa ya kalle ta ya san ta na da aure. "Haba Juwairiya ko wane mutum ya kalle ki ya san kina da aure kin san a kwai matan da dole a gane matan aure,duba ga yanayin jikinta ki kalle kanki kema kin san bakya son ki gaya mini ne,to ki mai da wu ar ni ban ce zan gan shi ba bare ki yi tunanin ko zan bashi anwata ne." Ta ce da tsigar wasa saboda ta na son ta kwantar da hankalinta ganin yadda ta birkice lokaci guda. Jin abin da ta fa a sai hankalinta ya tashi sosai duk da garga in da zuciyarta take mata na kar ta fa a mata halin da take ciki,amma ta na jin lokaci ya yi da za ta daina shanye damuwarta ita ka ai ta sanar da ita ko don ta samu shawarar yadda za ta cire son maso wani a ranta. Kama hannunta ta yi ta ha e da na ta ta kalli ta cikin muryar son kuka ta ce."Tabbas tunanin ki haka ne amma ina bu atar mu samu in da babu mutane ina da damuwa ina son ki ba ni shawara." Ganin ta fara kuka sai ta ri e hannunta suka koma in da babu mutane. "Tabbas tunanin ki gaskiya ne ina da aure amma auren sirri na yi da mijina na shekara aya." Sai ta din ga kallonta irin kin zare kenan ko kuma baki san mai kike fa a ba ta kasa magana sai kallonta take yi. Ganin ta kasa yadda da abin da ta fa a mata