Sashe 5
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ta hatta innerwears inta,mai aiki take wanke wa ko al'ada ta yi sai dai mai aiki ta kwashe abin a bayi ta zubar sannna ta wanke.Ta na matu ar alfahari da gatan da iyayen ta suka bata tare da yi musu addu'a.Mace sangartacciya mai son jiki da hutu da zallar wayewa mai anci wacce rayuwarta a cikin fararen fata ta yi. Zainab ta na da kyua na nuna wa tare da mannata a hoton irin matan nanne wa anda ka na ganin su kaga hutu,ko kai mace in ka hansu sai ka yaba.Doguwa fara ga gashi da kyan diri sannan ta na ara zuzuta kyanta da mayuka na gyara gashi da fata da kuma sabulai masu tsada.Ita dai ta yadda ta bautawa jikinta ko da za ta karar da wunin ranar ne,shi yasa in ka kalleta dole ka ara. Ta na da girman kai a gurin samari ga ta da farin jini,amma duk saurayin da yazo za tace bai yi mata ba.Mahaifinta ya na matu ar son yaga ya yi mata aure don ta haifa mishi jikoki,shi yasa kullum yake lallashin ta akan ta fidda miji daga cikin yaran masu da shi da alhazawan da suke neman ta,amma ta i ita ganin ta aure ta urawa rayuwar tane.Tafi son rayuwar hutu da jin da i sannan ba ta son ta ura da shishshigi ga lamarin ta. Abin da ara tsoratar da ita ganin awarta Nihal da ta yi aure shekara aya da ya wuce.Ta na da kyau da gayu,amma tun da ta yi aure ta haihu ta zama atuwa ga tumbi da ta yi,sannan irjinta ya zube,kullum cikin aikin yara ko a gurin aiki ta rage okari,ga takurawa an tiktok in da take yi mijinta ya hana. Wannan dalilin yasa ta ara tsanar aure ta na gani kamar koma baya ne a rayuwar ta,ganin mahaifinta na da ku i kuma ita ma ta tara ku in da za ta auki nauyin kanta.Ta saka ma ranta ba za ta yi aure ba,in ma dole sai ta yi aure to ba za ta yadda ta haihu ba kawai za ta yi rayuwar hutu ne don gani take kamar tara yara wahala ce gata likita kuma bata son jikin ta ya canza. Duk mazan da suke zuwa gun ta kullum cikin kushe su take yi ta na yi musu wulakanci,kuma in auren za ta yi tana son namji mai kyau wanda ya fita gayu da tsafta.Ba ta ta a jin soyayyar wani a cikin zuciyar ta ba,shi ya sa take wula anta duk wanda ya zo gurin ta. Kwasam!Ta ha u A.m a ranar wata daren alhamis da misalin arfe shidda saura kwata agogon birnin a asar London,ta raka yar gidan anwar mahaifiyar ta siyo kaya.Suna zaune a cikin jirgin za su dawo A.m ya shigo hannunsa ri e da waya da cingam a bakinsa ya na taunawa a yangace.A.m na son cin cingam kamar mace hakan ya samo asali ga matar Alhaji Sama'ila da ta rike shi ta na son cin cingam.Hausawa sun ce zama da ma aukin anwa shi ke kawo farin kai.Aiko haka ta kasance A.m ya koya cin cingam a gurin ta duk lokacin da ya ci abinci ko ransa yake a ace,sai ya huce a kan cingam Ran shi a ace yake akan taron da suka yi da safe a companin su,sam yadda yaso taron ba haka ya kasance ba,wannna dalilin ya saka shi baro London bai kammalla abin da ya kawo shi ba. Ya shigo cikin jirgin fuskar sa kamar an yi mishi mutuwa,bai kalli kowa ba sai kujerar sa da ya nufa ya na murza tafin hannun sa tare da tauna cingam in da arfi saboda fushin sa ya ragu. Wani irin kallo ya watsa mata ganin ta zauna masa a kujerar sa,da fari ya auka makauniya ce saboda kowa da numbar kujerar sa amma ganin ta na ri e da waya sai ya daka mata tsawa da arfi yace."Za ki iya tashi a ujerata ki nemi ta i tunna baki je makaranta balle kin san yadda ake irga numbobi." A hatsale ta mi e tare da fa in."What."Ita sai yanzu ta kula ba'a gurin ta ta zauna ba,saboda hankalin ta na kan wayar ta sanda ta shigo.Ranta ya ace jin kalaman sa sai kawai ta aga hannunta da nufin ta wanka ma mutumim da ya kira ta jahila mari,sai ya banbance waye ke da jahilcin atsakanin shi da tunna idanunsa sun kasa gane mishi wayayya mace mai a aji da class,wacce take tashe a tiktok. Zainab ta sauke hannunta a hankali jikinta ya yi sanyi matu a ganin matashin saurayin da ya kafa mata manyan idanunsa ya na kallonta,cikin zafin rai a yadda idanun sa suka nuna jira yake ta mare shi ila ball zai yi da ita yadda ya ha e fuska. Ta shiga in ina ta na arin matsawa daga gurin ya tureta ya na fa in."Matsalar an matan bahaushe kenan daga sunga sun fita waje su dinga nuna isa.Da kin mare ni wallahi sai na yanke duk yatsun ki na kai ma karan gidan mu nan gaba sai na ga da wane hannun zaki yi mari."Ya ja tsaki tare da zama ya ma ala earpis a kunninsa tare da har e hannun sa duka a irji,zuwa can ya cire earpis in ya lumshe idanunsa. Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu ha u a shafi na hu u dan har yanzu shinfi a ne har ba'a fara ba.Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. *FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE* *SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_