← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 102

Sashe 15

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta gani a fuskarta. "Na shiga uku yanzu in yace ya na son ya haihu ga shi ni bana haihuwa ya zan yi?Kuma wallahi ba zan ta a iya lamun ce na gan shi da wata mace ba.Gara ma ace na ga ranar mutuwata!Tace a zuciyarta ta na kukan nadama. "Ka yi ha uri hubbi ka yafe min na san na yi wa rayuwata illa ba zan ta a haihuwa ba!Girman lamarin ya yi wa zuciyata girma.Duk akan sonka ne ina son karka juya min baya inna fara haihuwa na saki sanann jikina ya canza,kuma na sha jin kana fa in baka son jikina ya canza kafi son na kasance yadda nake.Kuma a wannan lokacin ban shirya haihuwa ba gani nake yara kamar takurane a gareni duba ga irin yanayin aikina."Sai ta fashe da kuka ta na arawa taci gaba da cewa."Wallahi ba zan iya bu e idanuna na ga wata mace a matsayin muharramar ka!In kuwa ranar ta kasance to kasa a ranka zan kashe kai na na kasheta sannan na kasheka.In ta aice maka mutuwar kasko za muyi,don ina sonka ba zan juri wata a kusa dakai ba." Tsananin tashin hankali ya shige shi tare da nadamar furta mata wa annan kalamai da yake na baya son yanayin ta ya canza,duk da be yi tunanin za su yi tasiri a gareta ba har ta aikata wannan abu su yi dana sani. Ya zura hannun sa a aljihun wandon sa ya na kallon yadda fuskarta ya canza zuwa tsabar tashin hankali,ita kanta ya san ta yi nadama amma kuma mara amfani. Ganin be ce mata komai ba ya na tunanin wanda shi kansa be san tunanin da yake ba,sai ta ci gaba da cewa."ko ma me ya faru duk akan sonka ne A.m ina kishin ka zan iya komai a kanka,son da nake maka ya sa na lalata mahaifata." Ta kalle shi idanunta ya na zubar hawaye ta kama hannunsa ta ha a da nasa tare da kai bakinta dai-dai saitin kunninsa."Don Allah ka yi min wani al awari,ka amince za ka yi min sannan gaya maka." Ya dam e hannunta am ya na hawaye matu ar tausayinta ya kama shi ganin duk akan son shi ta shiga cikin wannan halin domin ta burge shi. "Na yi miki al awari amma wa ya gaya miki in mace ta haihu mijinta ya na tsanar ta ni fa ina yaba miki kyawun halittar ki amma ba wai ba na son ki haihu ba.Yanzu ya zan yi da iyayena da suka ora idanunsu akaina suna son suga jikar su?" a tambayeta ya na ganin tsananin wautar ta da ta aikata hakan,ita ma da ma wannan kan gabar take so yazo sai ta ara dam e hannunsa tace." Ka yi min al awari ba zaka ta a juya min baya ba kuma wannan ya zama sirri tsakanin mu cewar nice ba na haihuwa,sannan ka gaya ma dangin ka cewar matsalar da ga gareka take.Bayan haka ba za ka ta a yi min kishiya ba,in kuma ka yi to lai-lai nice ajalinmu baki aya." Ta fa a da farko da son ya auki al awarin muryarta a sha e ta na murza hannunsa,amma daga arshen maganarta sai ta arashe da murya kamar wacce take ba shi umurni ko tsoratarwa. Rungumeta ya yi ya na jin matu ar tausayin ta duk da girman lamarin amma sai be ga wata illa a ciki ba,musamman da ya ga duk akan sa lamarin ya faru don haka zai amince ya gaya wa iyayensa da hakan, dama shi a duniya be ga wata mace wacce za ta ha a kanta da Zey in sa ba ita ka ai ya ji ta burge shi kuma zai ci gaba da son ta ba tare da ya ha a ta da wata a mace ba don babu ita a duniya. "In dai akan wannan ne karki damu na miki al awari,zan shirya mana viza zuwa asar indiya a duba min ke don ban yadda cewar ba zaki ta a haihuwa ba. ara ru ume shi ta yi ta na fa in."I love you nureel albi.!" Loakacin da suka ji Zainab ba lafiya hankalin su ya tashi take a ka cika asibitin domin sun auka ko ciki ta samu.Mahaifinta da ba shi asar ya na jin ta na asibiti ya biyo jirgi ya dawo,ya na ta addu'ar Allah ya sa ta samu juna biyu,saboda ya na tsoron kar ita ma ba ta haihuwa kamar Mominta,duk da ya so ya ara aure ta yi ruwa ta yi tsa i ta hana. Wani irin gata suke nuna mata sosai musamman gidan su A.m duk tunanin su ya sami a ne,saboda tunanin su ya sa suke yi mata abinci irin na masu ciki suna kawo mata. Hakan sai ya sa jikin A.m ya yi sanyi ya na tausayin su don haka ya shirya musu biza suka wuce Indiya domin a duba lafiyarta. Kwanan su biyu suka huta sannan suka fara ganin likita,sai dai gwajin farko da suka yi mata aikin gaggawa suka sa aka shigar da ita tiyata,saboda mahaifar ta fara ru ewa ta na narkewa a jikinta wanda hakan zai iya kawo mata matsala.A.m ya shiga tsananin tashin hankali duk yadda yake cikin tashin hankali sai ya kwantar da na sa ya na lallashinta ganin ta na son ta yi aramin hauka. Be baro asar ba sai da ya tabbatar ta warke garau babu wanda ze ce an yi mata aiki.Sannan suka wuce zuwa yawon sha atawa don ya kwantar mata da hankali. Zainab ta yi kuka har ta ba uku lada daga arshe suka tattaro suka dawo cike da alhini. A lokacin da A.m ya sanar ma family in sa sun shiga cikin tsananin tashin hankali barim ma Daddy da har sai da ya yi kuka,ya rungume A.m ya na shafa bayan sa da tsabar tausayi da ya cika mishi zuciya." Yanzu son kai ma ba zaka ga wanka a duniya ba.Allah Sarki ni da kai ne kawai ba mu da rabon haihuwa."Sai ya ci gaba da sharara hawaye. Mahaifin shi ya jinjina lamarin tsananin tausayin an na sa ya kama shi."Ni yanzu nafi tunanin matarsa an ya anyi mata adalci ina ga ka bata za i kawai,domin na tabbata da ita ne ke da matsalar aure zaka ara in kuma ta amince za ta zauna dakai kaga ba'a shiga ha in ta ba."Yace ya ba kallon an nasa cikin tausaya wa. A.m ya ji matu ar tausayin iyayen nasa ganin yadda suka tashi hankalin su,suna jimami da alhini anya ya kyuata musu kuwa.Sun ba shi tausayi matu a wanda ya sanyaya jikinsa amma ko ma menene ya riga ya yi mata al awari. "Haka ne Baba nima na bata za i,amma tace ba za ta iya rayuwa ba ni ba."Ya ba shi amsa kansa du e." To shikenan Allah ya kyauta ai fa an likita ba na Allah ba ne,sai kaga Allah ya canza lamuransa "Sun yi matu ar jimami suka fauwala ma Allah lamuran sa an'uwan shi suna ta yi mishi tayin ya kar i yara daga cikin an su,duk da ya na son hakan sai dai ya san Zey in shi ba za ta yarda ba. Zaman nasu sai ya i jituwa tun daga lokacin sai suke samun sa ani da ya fara mata fa a, sai ta saka kuka tana fa a masa don ya ga ba ta haihuwa ne. Tun ya na ha uri har ya fara kai su gaban iyaye mahaifin shi kullum ha uri yake ba shi ya na nuna mishi halin mata,dama tunna baya haihuwa ya shirya kar an fiye da haka a gurinta. Rashin zaman ta a gidan shi yake ara damun sa kullum ya dawo aiki ba ze sameta a gida ba sai tarin azaman an aiki masu kama da mayu a gurin kallo.Shi ya manta rabon da yaci abinci me da i in dai ba gida yaje ba ko,gidan amininshi A.k.Kullum ba ta da gurin zuwa sai awa ta gayyace ta bikin awarta ana birthday awarta aikin ta ne kullum yadda ka san ana tsikarin ta in ta zauna a gida mace kamar me aljanun fita yawo. Ya dawo da misalin karfe hu u da rabi rabi na yamma yanayin garin hadari yake ha awa ya canza iskar garin ta na bada wani iska mai sanyi-sanyi babu abin da yake so ya sha ruwan tea me amshi ya shige cikin bargo ya yi bacci shi da ar matar shi. Sai dai abin takaici ya na shigo da motarsa ya ga ba nata motar tsaki yaja ya yi parking in motar a kasale ya fito be kula sannu da ma'aikan gidan suke mishi ba ya shige aki. Sharab!Ya zauna a falon sa ya na jin wani irin unci ya saka yatsu biyu ya tallabe gemunsa ya lumshe ido da takaici,burinsa ya bu e idanunsa ya sauke su akan kyakykyawar matar shi amma sai ya yi tozali da mero me aiki da tiren abinci ta kawo mishi tsaye ta na kallonsa. "Ke!Uban wa kike kallo."Ya daka mata tsawar da yasa ta watsar da tiren abincin za ta ruga,sai kuma ta dawo da sauri ta tsaya ta na arin gyara gurin ganin iri n aika-aikar da ta yi. " Anty ce tace na kawo maka abinci in ka dawo."Tace da shi bakinta na rawa ta na ci gaba da kallonsa.Ji ya yi tamkar ya sha eta ya mi e kamar ze kai mata duka da gudu ta ruga.. "Zainab kina bani tarin matsala na gaji da kwashe-kwashe da kike min gaskiya."Ya fa a idanunsa suka ara rinewa saboda tarin damuwar da yake ciki. Bata dawo gidan ba sai zuwa arfe tara na dare ta shigo da gudu saboda ruwan da ake yi tamkar da bakin warya,a lokacin A.m na zaune akan kujera two seater ya matsu ta shigo yau sai ta gane kuranta. Ba ta kula da shi da yake zaune da waya a hannunsa ya na dubawa ba,ta tsaya a falon ta na arin cire kayanta da ruwa ya soma ji ata saboda tafiyar da ta yi zuwa cikin gidan. Gyaran murya ya yi wanda yasa ta fahimci ya na falon gaban ta ya an fa i,amma ta dake bata ce komai ba sai arin
Chapter 15 · 0% Book details