← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 102

Sashe 54

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 22* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ke uban me kike yi haka ki ka canza ko kayan shafana kike amfani da shi in ba na nan? Duk da na kulle akina." Zainab ta ce ta na kallonta cikin tsananin mamakin yadda ta ga Juwairiya ta koma lokaci guda. Juwairiya hankalinta ya tashi ita kanta ta yi tunanin hakan dama dole ta yi maganar canzawarta,ko A.m da suke tare kullum sai ya yi maganar ta ara kyau bare Zainab da ta an jima ba ta ganta ba,sai ta yi shiru ta na zare ido. "Dear ba ka ga yadda yarinyar nan ta zanca ba kalli jikinta ka gani da key na na tafi,amma ina tunanin shafe-shafe take yi da siyan supplement irin yadda an matan yanzu su ace da siya don su yi kyau. To in ma shi kike yi wallahi ina tausayin ki matu a don babu in da zai kai ki sai motar nadama,domin duk tashen kyau da kika yi daga arshe cutar canser ita ce ajalin ki,kin ga kin kashe kan ki a banza saboda kwa ayin duniya da son burge namiji,gara ki tsaya a haliitar da Allah ya yi miki,saboda namijin da kike yi don shi gudun zai yi,kin ga wa gari ya waya? " A.m da ko kallon Juwairiya bai yi ba haka zalika bai kalli Zainab ba da take zuba nasiha,a ran sa ya na tunanin dama ta na da hankalin yi ma wani nasiha ta kasa yi wa kanta.Ya na cin abincin sa hankalin sa kwance,irin ba ruwana can ku arata ba ta shafe ni ba. A yatsine ya juya ya kalli Zainab sannan ya yi ma Juwairiya kallo aya ya auke kansa don ji ya yi ta burge shi sosai ya ije cokalin abincin sa ya na hararar da ta zame masa a'ida tare da kallon Zainab." "Ta ina zan gane hakan tun da ba kallon ta nake yi ba ke ma tsokana na kike bayan kin san idanuwana ba sa iya kallon wata mace sai ke,kuma in ta na shafe-shafe ina ruwan ki ba aure za ta yi ba.Kuma ni ba na tunanin haka wata ila canjin abincin da ta samu ne ta canza kin san ko wace mace da kalar jikinta.Kuma ga shi ta iya girki sosai wallahi ina yabawa abincin ta a kwai saka natsuwa a zuci." Zainab ta harare shi ta tsaki tsa i jin abin da ya ce." Oho Allah ya sa a duniya za ka ce ita ta ci gasar iya girki bai dame ni ba, ba wahala na zo yi a duniya ba bare na bautawa wani can,kuma da kake magana in dama ba ta iya abinci ba korar na zan yi tun da dalilin da ya saka aka auko ta kenan." Kamar ba zai ce komai ba ganin yadda ta ule amma ya na son ya untata mata, saboda ya fahimci in ya ce dukan ta zai din ga yi haka za su ci gaba saboda ba za ta ta a canza halinta ba,shi kuma sam ba ya son ya mai da gidan sa gidan dabbe musamman da yanzu Juwairiya ta auke shi kamar wani waliyi." Spoon ya auka ya ta e bakin sa tare da are ledar tuwon shinkafa da ta tu u sosai ya zuba miya,ya kalli Zainab da take huci kamar wata kububuwa don ya ya bi Juwairiya ya ce."Ai ita komai ta iya ta na da ari matu a dubi gidan nan komai tsaf-tsaf sai tashin amshi da yake saukar da nisha i a zuciya ga..." A.m ya yi shuru da maganar da yake yi jin an yi jifa da kayan abincin da yake ji a asa. " Na ji ta iya koma mene ne ba ruwana kuma in ban da munafunci ce wa ka yi ba a gida kake kwana ba in na yi tafiya shi ne kake maganar iya abincin ta." ewa ya yi a gadare ya ba ta amsa da ce wa."An gaya miki ku in banza nake samu da zan din ga yawo hotel ina kwana?Da ma sau aya da kika yi tafiya na kwana a can tun da na ga ba canza wa za ki yi ba, na na ha ura ina kwana a gida ai da babu gara ba da i ko banza a kwai wace za ta ba ni abinci." "Ya ishe ka a gaban wata banza da iya kake gaya min wannna maganar?Ya zama dole Juwairiya ta bar gidan nan duk da ba na tunanin ko kallon ta za ka iya kuma na yadda da kai A.m,amma ai ta isa aure kawai zan auko yarinya arama in ya so ta koya mata aiki ta bar min gidana." Am ya kalle ta ya aga kafa unsa alamun bai dame shi ba ya ce." Ya rage na ki Zainab mijinki na ke matu ar ba za ki zauna ki kula da ni ba,ni kuma ina da damar da zan hana duk wata mai aki shigowa gidan nan sai wanda na ya ba da abincin ta tun da ni ake girka ma wa,in kuma za ki canza ta fine amma kece za ki zama makwafinta ba ki ba fita gantali sai kin girka min abinci." " Kalle ni da kyau ai wallahi arya ka ke don ba ka nemi aure in da matar ka za ta dafa maka abinci ba." Ta fa a ta na juya jikinta tare da takun girma sannan ta ora da ce wa." Kuma kan ka ake ji ni ara fita zan yi saboda kaya ake so da yawa,amma kafin na tafi dole na kawo yariyar da Juwairiya za ta koya ma aiki." Ta wuce zuwa da sauri bayan ta harari Juwairiya ta ce "Kuma da ga yau na hana yin girki tare da na ku ki yi mana na mu daban kuma daban." " Allah ya sa bangon duniya za ki ba wata asa ba mu zuba ni da ke shege ka fasa." A.m ya fa a mata lokacin da ta haye sama ya juyo ya kalli Juwairiya da ta bushe a tsaye ta na kallon dirama,girar sa ya aga mata tare da kashe mata ido aya ya ganin ta firgice ya manna mata kiss a kumatu. "Abinci ya yi da warai " "A kwai tukwici an jima." Zare idanunta ta yi ta zuba mishi ido lokacin da ya haye sama ya na sakin mata murmushi mai tsada wanda ya saukar mata da kasala har sai da ta zauna. A hankali Juwairiya ta ja jikinta ta shige cikin aki ta na mamakin A.m da kullum saka ta yake a cikin shakku. Ranar wata safiyar talata Juwairiya ta shirya za ta gurin Mama.Ko da ta isa gidan Mama ba ta nan sai da ta jira ta sannan ta dawo daga mo ota da ta shiga. Cikin mamaki Mama ta tsaya ta na kallonta tare da ri e bakinta don ta rabu da zuwa gidan kwana biyu. "Juwairiya kin gan ki kuwa haka kika dawo sai kace amaryar da take ganiyar cin amarci!Gaskiya kin yi kyau sosai." Gaban Juwairiya ya yanke ya fa i gani take kamar Mama na zargin wani abu,irin yadda take kollonta cikin mamaki. " Kai Mama hutu ne fa kawai saboda ku i suke da shi sosai." Mama ta matsa kusa da ita ta zauna tare da ri e hannunta ta na shafawa. "Gaskiya kin yi kyau matu a ki na sane da saura wata biyu da kwanaki ki gama aikin ki ko?" Ta tambaye ta da osawa sannan ta ora da ce wa." Na matsu warai na ga kin yi aure ji nake kamar rai na ya na jiran wannan ranar ne kawai." Mama ta fa a ta na arewa Juwairiya kallo tare da tunani barkatai a zuciyarta. " Mama aure lokaci ne ai zan yi in lokacina ya yi kuma ni yanzu aure tsoro yake bani,ji fa Mariya har sun rabu da mijinta.Na matu ar tsorata Mama ina tsoron kar na yi aure na dawo ina zawarci." Ta fa a yayin da idanunta suka yi rau-rau tuna maganar da A.m yake gaya mata a kullum. " Ko wa da addarar sa Juwairiya kuma mutum ba zai iya tsallake ta ba,wata ila zaman su ya are da mijinta a kwai rabon wani a gaba shi ua sa suka rabu,amma kar ki saka wannan a ranki ki saka a ranki za ki yi aure da zuciya aya." Ta fa a ta na kallonta sannan ta mi e tare da juya ma Juwairiya baya ta auko ku i ta ce."Kin ga wannan ku in nan,ina adana su ne in kika gama aikin nan kamar yadda aka iba she ara aya,in dai Sani bai amince ki yi aure ba to za a haifi a mara ido tsakanina da shi." "Mama hakan ma ba zai faru ba in sha Allahu aure zan yi kar ki ta da hankali Mama." Juwairiya ta fa a jin abin da Mama ta ce ma ta sai hankalinta ya tashi matu a, ta shiga zubar hawayen da ta kasa gane dalilin yin sa saboda tarin damuwar da yake ranta. A ranar Juwairiya ta je da nufin ta ba Mama irin tarin ku in da A.m yake ba ta saboda hannun sa a sake yake,amma jin irin maganganun da take yi mata mai kama da wanka da ruwan jurwaye, sai hankalinta ya tashi ta koma ba tare da ta iya ba ta ku in ba,saboda ta na tsoron kar Mama ta tuhume ta. Koda ta fito za ta tafi Mama ta auki tsawon lokaci ta na mata nasihar da ta kula da mutuncin kanta,a haka suka rabu jikinta kamar an yi mata dukan tsiya. Zaune suke a falo Zainab ta na gefen A.m da hankalin sa,ya auku akan labarai da ake yi tashar aljazira.Zainab ta na ri e da filet da ta yanka apple ananata na ci. Zainab ta kalli A.m da ya an juyo ya na kallon ta ta ce." Ka san me wannan shashashan yaron ya ce?" auke kan sa ga barin kallon ta tare da aukar remote da ke gefen kujerar da ta ke,ya canza tasha ganin an gama labarai ya ce. " Wa kenan." "Amir ma na." Ta na nufin cousing inta sai ta ci gaba da ce wa." Kirana ya
Chapter 54 · 0% Book details