← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 102

Sashe 77

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 29* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Juwairiya kunya ta kama ta matu ar gaske ji ta yi kamar ta nutse a asa,juwaya ta yi za ta koma ciki,amma sai A.m ya janyo ta tare da ha a ta da irjin shi. " Ke! Wace irin mahaukaciya ce da za ki shigo gidan ma'aurata kai tsaye sai ka ce akin gidan ku." "Lantana jikinta ya kama rawa kamar mazari saboda tsawar da ya daka mata,ta yi mugun firgita ba ta gane abin da ya ce ba. " Ka yi ha uri yalla ai wallahi ban san ka na ciki ba,kuma Hajiya Zainab ta ce na zo na gyara gidan za ta dawo." Ta fa a jikinta na rawa kanta na asa ta na mamakin abin da ta gani don ta firgita. A.m ya yi farin ciki sosai jin abin da ta ce sai ya an ture ta daga jikinsa,ya kalli Lantana da har yanzu idanunta a asa suke,ba ta son ta ara ganin abin da ta gani,domin ila arya suke mata. " Ok sai ki je ki yi aikin ki munafuka na sha mamaki da Zainab ta tunume ni akan ina tare da Juwairiya,a she ke ce munafukar da take son raba aure. Wallahi kin ji na rantse miki in har kika yi gigin fa a mata abin da idanun ki suka gani,kaf an gidan ku ni ne ajalin su don bom zan siya na tashi gidan." Ware idanunta ta yi tsananin tsoron sa ya kamata saboda idanun sa sun tabbatar mata da zai yi fiye da haka. " Ba ke kin iya munafunci ba to bari na ara miki da abin da zai kashe ki,don ba za ki iya fa a mata ba duk munafuncin ki saboda in ban kashe ki ba,to ita za ta yi ajalin ki kin ga gulma ta yi riba kenan." Ya ce da ita ya na zare mata ido domin haushi take ba shi,tun da ya ji ita ta fa a mata komai,ga shi yanzu ta korar masa da matar so. "Juwairiya matata ce wanda na aura a bisa wasu dalilai da ba zan gaya miki ba,saboda bai shafe ki ba." ara matse ta sosai a jikin sa kiss ya sakin mata a kumatunta,ya na mata wani irin kallo da ya saka ta kauda idanunta saboda kunyar Lantana. " Kin ga in ta dawo sai ki gaya ba mata yau ara gani ba kuma iyakan runguma ba,ki sanar mata duk abin da kika gani kar ki rage." Lantana da sauri ta shige kicin tare da rufe ofar. " Innalillahi na shiga uku!" Ta sauke ajiyar zuciya mai arfi yayin da kanta ya kulle ta rasa in da za ta fara tunani. " Wallahi wannan mutumin ya rikita ni na rasa mai zan fara tunanin,a halin yanzu zuciyata ba za ta iya fahimtar komai ba,domin ya saka ni a cikin ru u."Ta ce yayin da ta ora hannu akanta. " Da gaske ya ke fa in matar sa ce ita?A 'a lamarin nan a kwai rikitarwa! Ji fa yadda ta koma tamkar wata gilas,saboda tsabar kyau kai Zainab shashashar mace ce,wai ta je hutu ai kuwa ki dawo za ki ga sakamakon hutu." " Wa ni ai komai na ga kuna yi ba zan iya gigin gaya mata ba,haka kawai ku da holewa ni da shan bugu.Kai amma fa A.m arshe ne gurin rashin mutunci don ko ka an Zainab ba ta yi tunanin ta na gidan ba." Irin maganar da take yi a zuciyarta kenan ta bu ofar a hankali ta na le en su,sai ta ga sun ara rugawa da gudu sun yi ciki. " Allah ya kai mu ki dawo gidan nan za mu sha kallo!Allah ya sa kar ki yi shigowar dare in ba ma idanuna abinci,sai ki gane sakaci kika yi ko halin maza A.m yake nuna miki."Ta fa a sannan ta kama aikinta zuciyarta cinkushe da tunani kala-kala. Bini-bini za ta le a ta na kallon sama amma sai ta ji shuru kamar bacci suka yi. " Ha ina tausayin ki yarinya ba ri Zainab ta dawo."Ta ce ta na aiki cikin mamakin lamari da al'ajabi. " Humh namiji bunun aya." Abin da take ta nanatawa kenan a cikin zuciyarta. A.m ya rungume hannun shi ya na kallonta da ta kwanta akan cinyar shi,ta ora filo a irjinta idanunta lumshe kamar ta na bacci,sai dai a zahirin gaskiya ba bacci take yi ba. Zuciyarta cinkushe da kishi da tunani jin Zainab za ta dawo,domin a yadda take jin son sa da kishin ta ba za ta iya oye kanta ba,kamar yadda ta yi a farko ta na jin ko sama da asa za su ha e za ta nuna kanta a wannan karon. Kamar yadda take tunani shi ma haka zuciyar sa take cinkushe da tunani,ga shi ya gagara samo mafita. Duk da cewa zuciya da gangar jiki sun yi kewar Zainab,amma in ya tuna za ta dawo gaban sa yake wani irin yankewa ya fa Ya sani a yanzu babu wanda zai kalle ta yabce ita yar aiki ce,duba ga yadda ta koma tamkar wata tarwa Ya na ta tunanin ko ya auke ta daga gidan sai dai ya na jin ba zai iya jure rashin abincinta ba,saboda har yanzu ya kasa iya cin abincin Lantana. Wayarsa ya zaro ya gwada wayar Zainab da ya daina kira,saboda auka da take yi. Sai dai ringing aya ya ji ta amsa tare da sakin kuka. " Ka daina sona A.m ban ta a tunanin a kwai ranar da zan yi fushi da kai ka yale ni ba." Ta amsa daga angarenta ta na wani irin kuka da yake tafarfasa masa zuciya. Tsam Juwairiya tami e daga jikin sa ta fice daga akin ba tare da ta kalle shi ba,yayin da zuciyarta ke mata luguden bugu na kishin sa. Binta da kallo ya yi ganin ta canza kalar fuskarta kamar ba wacce ya sani ba. Sai da ta fice daga akin ya saukar da nauyayyar ajiyar zuciya. " Ya kike son na yi kin mai da ni kamar wani wallo don kawai kin ga Allah ya jarabce ni da son ki?Kawai na ba ki dama kije duk abin da kika yi ninya ki yi,ni dai har yanzu ba zan fasa gaya miki ina sonki ba." Ya ce da ita ya na jin tsananin haushinta da kuma fargabar abin da zai faru,domin ya na ji a jikin sa kamar lokaci ya yi da zai gaya mata zaman Juwairiya a gidan su,don su daina samun sa ani,duk da ya san zai sha wahala kafin ta amince. " In har ka na sona da gaske A.m ka daina kawo rigima a cikin aurenmu,sannan ka tuna da al awarin da ka yi min don Allah karka canza." Shiru ya yi bai ce komai ba ya rufe bakin sa da hannun sa ya na jin saukar kukan da take yi. " Ka yi shiru ba ka ce min komai."Ta fa a cikin muryar kuka. " Mai kike son na ce miki Zainab wane irin halacci ne ban yi miki ba! Ki dawo a kwai wata magana mahimmanciya wace za mu tautauna,kuma in kika fahimce ni in sha Allahu ba za mu ara samun tarna i a aurenmu b." " A.m a kwai matsala ne don Allah ka fa a min?" Ta tambaye shi da za uwa jin muryar sa ta canza." Babu kuma kar maganar da na ce miki za mu yi ya aga hankalinki domin alkhairi ce." " Ok to shikenan baby ba matsala,amma fa ka canza gabaki aya,domin da ace babu wata matsala cewa za ka yi in jira ka mu taho tare."Ta ce da shi da wata kalar murya. " Wata ila da izinana kika tafi?" Ya ce da ita a ufule kawai sai ta ji ya datse wayar, a lokacin da take fa " Tun da ba za ka zo ba sai arshen za mu dawo,saboda zamu tsaya mu yi siyayya." ewa akan gadon ya yi tare da shafa gemun sa da ya awata masa fuska. Wani irin damuwa ya ji ya lullu e shi sosai. " Gaskiya na canza shawara ina ganin kawai zan oye Juwairiya duk san da ta samu ciki,sai na saka Zainab ta yi cikin arya a zuwan ita take da ciki in ta haihu an ya zama Zainab a zuwan ita ce ta haihu." Take ya amince da shawarar sai ya mi e da sauri ya saka takalmin sa ya fice zuwa akinta. Ta na tsaye a gaban mirrow ta juya bayanta tare da an jingina kanta da gefen mirrow,a ranta ita ka ai ta san mai take tunani,domin iya tsananin damuwar dake kan fuskarta na hango.Ba tare da ta san ya shigo ba ya fara magana. Kallon sa take yi da wani irin canji a fuskarta har ya gama mata bayani,ba ta tanka ba illa kallon sa da take kamar ba o a gare ta. Ganin ba ta da ninyar magana sai ya saki tsaki ya juya ya na fa in." Ina fatan kin ji mai na ce." Ko ka an A.m bai canza mata ba wai don Zainab za ta dawo,haushin da take ba shi duk ya yi mata maganar abin da ya tsara sai ta yi shiru ta zamar masa kamar wata kurma. Zaune suke a falo sun dawo daga siyayya A.m ya ce ta raka shi a kwai turaren da yake son ya siya. Sun zaune a falon asa sun baje kayan ciye-ciye suna ci Turaren da ya siyo ya na son ya yi ha a da wanda yake shafawa,saboda turaren ya tafi da imanin sa gashi ba zai iya canza wanda yake fesawa ba. A hannunta ya kama ya fesa mata a hannun ya ce." Matar shige ki ji amshin sa ya yi da i ko?" Juwairiya har ga Allah amshin bai yi mata ba,kallon sa ta yi ta ata fuska tare da toshe hanci." Humh ni ban ji wani amshin da i ba don ni warin almiski ya yi mini,kuma ni ba na son almiski." " Allah ko ka ji gulma wannan turaren ko shugwaban asa ya sha amshin sa ba zai kushe ba,balle ke ni na san gulma ce irin ta ki don ko wanda na ke shafawa
Chapter 77 · 0% Book details