Sashe 83
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ya zuba masa ido sosai cikin son dariya. " To fa baban baby ka ce kai ma ka shiga daga ciki kenan." Ya fa a a ransa yana tunanin kamar Juwairiya tana daga cikin jinsin matan da Allah ya halitta,a lokacin da suka samu ciki sai Allah ya jarabce su da tsanar miji tsana mai tsanani,yayin da suke aurace ma mazajen su wasu har suna cutar da kan su. Don matar sa tana daga cikin irin masu wannan halittar,duk sanda ta samu ciki shikenan zaman lafiya ya yi aura a gidan su har ta haihu. " Humh ka na ji fa wannan yar rainin wayon take fa in na matsa,ai ita ta san in da ba babyna da yake jikinta ba babu abin da zai saka na matso kusa da ita,bayan ta san babu macen da nake so irin matar so."Ya fa a yana hararar ta sosai ganin ta hana shi jin motsin baby. Ga mamakin sa sai ya ga ta mayar masa da hararan da ya yi mata,don ita har ga Allah ta ji wani irin tsanar shi a cikin ranta,ba wai don abin da ya faru ba,sai dai wani canji da ta ji a jikinta,saboda in ya matso wani irin wari take ji har da arni- arni a jikin sa,wanda yake tado mata da hararwa. A.k da ya yi tsuru yana kallon abin al'ajabi ganin yadda suka auki fushi,bai ta a tsammanin Juwairiya tana da tsiwa ba. " Ikon Allah yau kuma irin murnar da za ku nuna kenan,bayan yau Allah ya kusan cika muku burin ku.Kai zaka samu magaji,ita kuma za ta koma gurin Mama kamata ya yi ku nuna ma Allah godiyar ku." A tare suka harari junan su sai ta ji wani irin kewar Mama da son ganin ta ya kamata. Hawaye ta soma zubarwa wanda ya aga hankalin A.m,cikin aga murya ya daka mata tsawa. " Ki yi ma mutane shiru so kike ana ya gado shegen kukan ki na rashin dalili." A.k da yake kallon dirama dafa kafa an sa ya yi ganin yadda ya daka mata tsawa. " Haba A.m be a man. Baka ka san ba'a aga ma mata masu ciki murya,irin shi ne suke haihuwar a motsi ka an sai ya birkice." Da sauri ya kalli A.k cikin razana ya kama hannun sa ya ri e sosai." Da gaske kake?Ina ga zan duba duba google akan yadda zan kula da cikin saboda kar a samu matsala, ina son yarona ya fi an kowa a duniya,kuma ba na son ya yi kama da waccan abar mai emotionally fence."Ya ce yana nuna ta da bakin sa tare da galla mata harara. Tura bakinta ta yi ba ta ce masa komai ba,don ita yanzu haushin sa take ji na rashin dalili A.m ya ara hassala don ya tsani raini, karfa don ta ga ta samu ciki tace za ta yi mi shi rashin kunya,da kuma ya tuna abin da A.m ya gaya masa sai ya du a kusa da ita. " Kin san fa yanzu bake ka ai ba ce,don haka duk kulawar da zan ba ki babyna nake ma wa,ki kwantar da hankalin ki yarona ya sakata ya wahala ya yi atoto." ara sausauta muryar da ba ta ta a sanin yana da shi ba." Baby mai kake son ci?Ka fa i duk abin da kake so zan kawo maka shi." Ture hannun sa ta yi ganin ya ara kawo wa "Don Allah ka yale ni ba na son cin komai." " Ba ke na tambata ba babyna nake magana da shi don na san dole yana bu atar abinci." Ya fa a a kausashe don shi jin yake anya zai iya aukar raini daga gare ta. " Ka dai kula da abin da na ce maka, in ka din ga daka mata tsawa ta haifi yaron matsoraci, kai ka sani ka san dai wannan shikenan babu ari."A.k ya ce da shi. Sosa kan shi ya yi." Na ji kuma zan kiyaye in sha Allah.Dole na samu babban likita wanda zai dinga orani a kan yadda ake rainon ciki." Juwairiya ta mi e ta tana wani yatsina irin na masu ciki gabaki aya ta ji wani canji a jikinta.Dambu da kalalla a ta ji kawai tana son ta ci,amma ta san ko ta fa a masa ila ba zai nemo mata ba. Amma kuma da ta ji son cin abincin zai saka mata amai,in dai ba ta ci ba kallon sa ta yi ta ce." Ni fa dambu zan ci da kalalla a kuma yanzu nake so." A.m ya zare ido ya ce." To yar rainin wayo gara dambu na san shi matar A.k tana yi,amma kuma mene ne kalalla a?Ni fa kar ki raina mini wayo ila ba baby ba ne zai ci." " Ko ma waye zai ci dole ka nemo ai wallahi tausayinka nake ji,don yanzu ka shiga hannu dole ka zama an siyayya."A.k ya ce mishi yana kallon doctor da ya turo ofa ya shigo. " Yauwa doctor yau she zan dawo ka ba ni shawarar yadda zan kula da babyna." Dariya ya yi suka tafa da A.k." Abinka da sabon shiga."Hararar A.k ya yi jin abin da ya fa Wayar sa da take da can gefen Juwairiya ta auki ruri sosai.Gaban sa ne ya fa i don ya san kiran bai wuce daga gidan su. " Please A.k aga wayar ba zan iya ba na san bai wuce Daddy."Ya fa a yayin da fara'ar shi ta kau. Shi kan sa A.m a tsorace yake ya san ayau Allah kawai zai raba su da shi. Da ya aga wayar sai ya saka ta a hands pree. " Kaicona Abdurrahman! Yau na yi dana sani da na ora ya inina akan ka.Abin da ka aikata kenan?A she baka da hankali wallahi ban ta a sanin mahaukaci ba ne kai sai yau.Maza ka taho gida ina neman ka duk in da kake, da kuma yarinyar da Zainab ta ce ka dake ta saboda ita,don ni bazan ce matar ka ba ce sai dai kuma in ka canza iyaye bayan ni da Daddy inka.Minti biyar na baka." Mahaifin A.m ya fa a yana huci ya kashe wayar,yana kallon Daddy da ya yi tsuru-tsuru. A.m jikin sa ya yi sanyi ya kalle ta duk tana jin abin da ke faruwa,amma ba ta nuna komai a ranta ba. "Mahaifina ya na son ganina dotor ka sallame mu." Ya fa a jikin sa a sanyaye saboda ya san a yau duk wanda yake da ima a idanun su, imar shi za ta zube,ya san mahaifiyar sa ba ta da wasa mace ce da ba ta aukar raini,hankalin sa ya ara tashi da ya tuna annin sa ko ya za su kalle shi. " Ka san Allah babu in da za ni, sai da na garga e ka amma ka yi mini rashin mutunci,yau sai ka waci kan ka da Daddy,amma babu in da za ni na san Daddy ya yi fushi sosa."A.k ya ce da ya ga yana kallon sa. " Juwairiya tashi mu tafi sai ki jure duk abin da za ki gani,sau inta ma siyen ki na yi da ku ina balle ki ce na kai ki in da za'a wula an ta ki." Hankalinta ya tashi gabaki ta fita hayyacinta ji take kamar ta ga ta ace. " Na shiga yau zan ga ahalin A.m wani irin tarba za su yi mini?Yau na san zan sha wula anci wata ila dukana za su yi." Ta fa a cikin tashin hankali ganin yadda shi kan shi ya ru e,sai ta raya a ranta babu in da za ta don ba za ta je su kashe ta ba. Kamar ya san mai ta raya a zuciyarta ya ja hannunta,da arfi ya nufi mota yayin da gabansa yake dukan tara-tara. A.k kuwa daga asibitin gida ya koma ko aiki ya i zuwa,tunanin shi Daddy zai iya bin shi gurin aiki,bayan ya shiga gida ya sanar da maigadin gidan sa duk wanda ya zo ace ba ya nan,ya rantse ba zai ara zuwa aiki ba sai ranar da aka gama wannan rikici. A lokacin da ya gaya ma matar sa ta yi shiru,ta zuba mishi ido tana jin tatsuniyar da yake mata,zuciyarta na matu ar mamakin sa,tsawon shekara biyu suka shirya hakan,amma ko wanka mai kama da jirwaye bai ta a yi mata ba,sai abin ya ara ba ta matu ar mamaki ta din ga kallon sa tana son ta yi magana amma ta kasa. Kofin gilas in da ke hannunta ta saki tare da zare ido da ta ji ya ce." A yanzu Juwairiya na da ciki kuma Zainab ta gane,Daddy ya yi kiran sa tsoro ya sani na i zuwa don babu irin abin da ban fa a masa ba,amma ya yi kunnin uwar shegu da ni sann..." " Na shiga uku wayyo Allah na! Oh Zainab mai ya kai ki aikata wannan kuskuren lallai kin yi sake."Ta ce da tsananin mamaki sai abin ya ba ta tsoro hararar A.k ta yi ta ara cewa. " Amma wallahi kun munafunce mu gaskiya ba ku yi mana adalci ba,haba Baban Najwa yanzu watarana in za ka ara aure haka za ku munafunce ni." Dariya ya yi ganin ta birkice kishi arara a fuskarta." Baki fahimce ni ba A.m ya kashe ma udan ku i ya auri Juwairiya akan za ta ba shi baby in ta haihu su rabu ya bawa Zainab,wannan dalilin ya ije ta a gidan sa don tana haihuwa za su rabu,sakacin Zainab ya kusanta Juwairiya da shi,don tana da hankali ga kula da tsafta da iya girki ni kaina in na ci abincinta ina yabawa." Ya numfasa sannan ya ora da cewa."kuma kin san A.m da son kula shi ya sa nake kallon Zainab a matsayin wawiyar mace,saboda mijinta irin mazan nan ne masu son mace ta mai da su yaro,a yadda na kula da A.m zai iya barin mace ta yi masa komai na kulawa,wanda ita ta gaza hakan da haka Juwairiya ta samu ta saka sha uwa a tsakanin su,duk da har yanzu yana kan bakan shi na rabuwa da ita,ni dai lamarin yana aure min kai sosai ina tunanin yadda za ta haihu ta ba wa wata