← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 102

Sashe 18

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

u ta din ga tamabayarta da in ta san inda yake ta fito mata da shi,hakan ya saka Juwairiya cikin tashin hankali ta dinga wani irin kuka gani take kamar Mama ba ta yadda da ita ba. Baba Sani ya sami abin da yake so don haka ya ara zuga Hajiya Binta kan ta tafi da ita ofishin an sanda,burinsa ya cika dama tintuni yake addu'ar Allah ya sa haka ya faru. Mama na gani aka tafi da Juwairiya ta na wani irin kuka gani take kamar dukan ta zasu ta yi har sai ta amsa laifin da ba ta aikata ba.Ganin an tafi da ita Mama ta nufi hanyar shiga cikin gida ranta na wani irin suya,hango halin da Juwairiya take ciki da yadda take kuka ta na kiran sunan ta,sai kawai gani akai ta yanke jiki ta fa asa. Hankalin Mariya ya tashi matu a wacce take zaune a asa ta na kuka sosai,gani take kamar ita ta saka ta a cikin wannan hali saboda hanyar aikin da ta yi mata. Ita da mahaifiyar ta suka kama Mama suka shigar da ita gida,sai dai daga baya kan dole suka kwasheta zuwa asibiti ganin numfashint a na aukewa gashi ta na aman jini! Baba Sani ya yi matu ar jin da in faruwar lamarin duk da ba shi da shiri akan hakan sai dai ya na ganin yanzu ne burinsa zai cika akanta,don ya tabbata basu da wanda zai yi belin ta hakan zai ba shi damar ora mata shara in zai yi belinta amma sai ta amince za ta yadda da bu atarsa,don haka ma ya i zuwa ogishin da nufin sai sun yi mata dukan kawo wu a ta galabaita saboda ya san ta a kwai kafiya. Juwairiya na zaune a cikin cell in ta udundune kanta a cikin jikinta tun da suka kawota take kuka,tunanin halin da Mama take ciki yake damunta wani irin sauro da yake damunta da ihu da cizo,yasa take ta zubar jawaye ga yunwa dake ularta."Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin fa ir."Abin da bakinta yake fa i kenan cikin tsananin tashin hankali. Tun da Hajiya Binta ta kawota ba ta ara zuwa ba sai washegari da safe lokacin ta matu ar galabaita,bayan sun tuhumeta amma ta i amsa laifinta dukan tsiya suka yi mata sannan aka maida ta. Da rana sai ga Baba Sani ya shigo ofishin ya na zare ido,gurinta yazo ya na kallonta." Kin ga abin da kika jawo ma kanki kosaboda shegen taurin ranki.'Yace ya na kallonta duk da ita ba shi take kallo ba saboda ta i ta kalleshi wani irin tsanar sa take ji matu " Har yanzu kina da dama zan iya fitar dake amma sai kin amince za ki yadda da bu atata."Yace da ita ya na kashe murya. Wani irin kallo ta watsa mishi " Allah ya yi min tsari da mugun nufin ka,da na amince gara na tabbata a gurin nan ko ya zamo shine ajalina." "Ok haka kika ce ko?To ai shikenan ku ina ya huta tunna kin za i rayuwar zuwa gidan mutane kina sata."Yace tare da watsa mata harara ya fice daga ofishin,kuka ta saka tare da cigaba da addu'ar ta ta na ro on Allah ya kawo mata mafita. Kwanan ta uku a gurin ranar da Hajiya binta ta shigo ta bu aci a saki Juwairiya taga sar arta,duk da cewa azafi aka yi mata amma ko ha uri basu bata ba.Ita dai da gudu ta dawo gida tasan yaran Hajiya Binta suka ulla mata wannan ullalliyar amma Allah ya fisu kuma addu'a takobin mumini. arin tashin hankali da ta zo Mama ba ta a gida Ibrahim ne yake sanar da ita ciwon Mama,wani kukan ta saka ta fita zuwa gidan su Mariya domin Mariya bata gaya mata Mama ba lafiya ba. Yadda ta ga Mama hankalinta ya tashi warai rungume Mama ta yi ta na kuka sosai.Mama ce ta bu e ido jin muryar Juwairiya hankalinta ya an kwanta ganin ta fito,don ba ta san halin da take ciki ba shi ya sa jikinta yake rikicewa. Likita ne ya shigo ya mi a ma Mariya takadda yace."Gashi ki siyo wannan maganin ya kamata ku din ga kwantar mata da hankali, domin ta na da hawan jini ga ciwon zuciya, matu ar ana ata mata rai to watarana zuciyar za ta buga!" Wani arin tashin hankali Juwairiya ta shiga jin Mama na da wa annan ciwuka rungumeta ta yi tana kuka."Mama kema mutuwa za kiyi?Don Allah karki mutu ki barni!Rayuwata za ta shiga cikin garari.Allah na gode maka ka bani ikon cin jarrabawa,amma karka auke min mahaifiyata ka barni da azzalimi." Mariya ta kama ta ta rungume ta na buga bayanta hawaye ya na kwaranya a fuskarta tsananin tausayi ya cika mata zuciya ganin halin da take ciki."Kin ga ni Mama za ta barni ko!Wai me ya sa rayuwata tazo a ba in jadawali ne?Nake kur ar ruwan bakin ciki mafi zafi da una a zuciya."Tace cikin kuka." A'a Juwairiya karki fa i haka!Kada ki kasa cinye jarrabawarki kin san Allah ya na jarraba mutum dai-dai imaninsa.Kar zuciya ta sa ki yi sa o.Ina ji a jikina zaki ji da i a rayuwarki.Allah zai ba Mama lafiya."Ta gaya mata ta na shafa bayanta. yar Juwairiya ta daina kuka sai ajiyar zuciya hannun Mama ta kama ta ri e ta na kallonta.Duk wani hidima na asibitin su Mariya da mahaifinta suka yi har kuka ta yi ta na gode musu domin Allah ne zai biya su. Bayan Mama ta samu sau i aka sallame su akan Mama za ta din ga zuwa ganin likita ta na kar ar magani,hankalin Juwairiya ya tashi ta na tunanin ina za ta din ga samun ku in da Mama za ta din ga zuwa ganin likita. Kan dole ta ara saka Mariya ta nema mata wani aikin don sana'ar da suke yi sun cinye tsugune kawai suke,da fari Mama ta i yadda ta ara yin wani aikin amma daga arshe dole ta ha ura ganin yunwa na so ta yi musu tabo. Kwasam ta ha u da wani matashin saurayi mai suna Mas'ud Allah ya jarabci Juwairiya da son shi yaro an gata da sanyin rai ga kyautatawa.Shigowarsa rayuwarsu ya sa sun samu canji sosai,duk da ya ga ita yar talaka ce amma be saka ya i sonta ba don da Allah yake sonta.Mas'ud ya na temaka musu sosai ya na aiki a Jami'ar Ahamdu Bello a library kuma an samaru ne iyayen sa sun rasu sun bar mishi dukiya sosai,sannan an kasuwa ne. Juwairiya ba ta ta a jin ta na son mutum ba sai akan sa, gabaki aya ta ji ta na son ta aure shi sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane,don babu yadda za'ai Baba Sani ya barta ta aure shi sai dai akan yadda take jin sonsa, za ta iya fito na fito a tsakanin su ko gidan me unguwa za ta iya kai shi. Haba tunna ya ga ya na zuwa gurinta ya saka tashin hankali yayin da shi ma Mas'ud ya kafe,ganin shi ma an zamani ne sai yace bai tashi uren Juwairiya ba don bashi da ku i,nan take yace mishi kar ya damu ya amince zai yi mata komai. Ranar da Mas'ud ya kira Juwairiya ya gaya mata Baba Sani ya amince da auren su har ya ba shi izini ya turo magabatansa,kawai jin sa Juwairiya ta yi amma ba ta yadda da abin da yace mata ba.Ganin haka sai ya yaleta kawai in ta ga zahiri ta yadda. Da misalin hu u da kwata an Baba Sani ya yi sallama ya shigo ya yi kiran Juwairiya taje shashin Baba Sani ya na kiranta a akin matarsa. Gabanta ya fa i amma sai ta saka hijabinta ta nufi akin ganin a kwai ba i ya sa ta ji a ranta a kwai abin da ke faruwa sai ta tsaya daga kofa ta na sallama."Yauwa Juwairiya shigo." Baba Sani ya fa a da murya sanyaya a hankali ta yaye labulen ta shigo tare da tsaya daga nesa ta na kallon mutane jikinta ya bata dangin Mas'ud ne. o mata alkur'ani ya yi tare da canza fuska kalar tausayi yace." Dangin yaron nan Mas'ud suka zo neman auren ki,amma ni bazan cuce su ba sun yi min tambayar kina da tarbiya nace gara suji a bakin ki, don nasan ke ar mace ce sannan kin yi yawon aiki gidajen masu ku i,duk mazan gidan sun sanki a matsayin a mace ga abin kunya na satar da kika yi,har aka kulle amma ga kur'ani ki rantse musu hakan be faru ba " ji ta yi asa ta gaza aukarta ta ji wani irin hajijiya ya kamata." Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un." Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu ha u a shafi na goma sha aya.Ga masu bu atar shiga cikin group ina na whatsapp ga numba 08144072423_. Kuma ofa a bu e take na orafi gyara ko arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce. Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za auran marubuciya,kuma awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani. *FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9*SAKACINA KO HALIN MAZA?* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *SUMMY M NA'IGE* _(Aminiya)_
Chapter 18 · 0% Book details