← Book details Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 102

Sashe 28

Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 14* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Sakamakon aiki da ya yi musu yawa sai hakan ya hana su zuwa kamar yadda suka shirya a ranar,saboda ba su tashi daga gurin aiki ba sai bayan sun yi sallar magariba daga nan kowa ya nufi gidan sa. A.m ya ji da i sosai ranar kasa bacci ya yi gani yake kamar ya auri Juwairah ya gama musamman da aminin sa ya amince,duk da a cikin zuciyar sa har yanzu ya na tunanin mai ya saka A.k ya sauko har ya amince duk da dokin na i da ya hau daga farko. A haka dai ya yi ta sa e-sa en shi amma ya rasa gano komai daga arshe ya janyo bargon da Zainab ta rufe jikinta da shi ta na bacci,ya rufa da shi tare da juyawa dai-dai fuskarta ya rungumeta ya na sha ar dadda amshi daga gareta,yayin da hankalin sa yake kwance kamar ya yi ba o ya mutu a ransa duk ya osa gari ya waye su ji yadda za su kaya da anin mahaifin Juwairah. A.k kuwa ko da ya koma gida hankalinsa a tashe gani yake kamar ya aikata zunubi me girma akan amince masa da ya yi,amma da ya auna a mizanin hankali sai ya ga da ta auri wannan tsohon rayuwar ta ta shiga garari gara A.m da ko ba komai za su samu ci gaba a rayuwa,duk kuma abin da zai faru wannan kuma ya bar ma Allah lamuran sa shi yake da iko akan komai,kawai abin da zai yi shi ne ya gaya ma Juwairiya kar ta yadda zuciyarta ta fara son A.m. Ya da e sosai ya na shawara kafin ya furta ya amince da auren musamman da ya ji mahaifiyarta ba da lafiya,a ta aice dai tsotsan tsamiya suke yi a rayuwar su tare da alhini. Washegari da safe A.m ya yi mishi dirar mikiya ko karyawa a gidan sa ya yi,wanda Maman Najwa ta yi mamakin sammakon sa amma sai ta yi tunanin ko ya na son A.k ya manta komai. Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Juwairiya. Baba Sani ya na arin fita gurin aiki da uran motarsa da yake ri e da makullin ta a hannun sa ya na karka awa. Ganin su a kofar gidan sai ya yi turus ya na tunanin mai ya kawo wa annan larabawan kofar gidan ko sun yi makuwa ne,saboda ya na da agawa sai ya auke kansa zai shige cikin motar sa ba tare da ya kalli in da suke ba,duk da tunani ya cika ran shi ganin sun tunkaro sa. "Assalamu alaika Malam barka gurin ka muka zo,don Allah ko zaka ba mu lokacin ka duk da ba ka san da zuwanmu ba,amma in ka bamu an mintuna zamu tafi musammam in ka yi ma abin da ke tafe damu kyakykyawar fahimta." Yace da shi da murya mai sanyi duk arin sa ya tabbatar masa da ba in sa ne saboda fuskar sa ta nuna kokwanton ko sun yi makuwa ne,duk da ya san ya na da an mata amma ko ka an bai yi tunanin za su zo neman aya da ga cikin su. Ya kalli A.m da ya aure fuskar sa kuma bai ce komai ba ya lura wamda ya yi mishi magana ya fi shi sakin fuska,sai ya mai da hankalinsa ga A.m yace a cike da shakku don shi har yanzu bai yadda gurin sa suka zo ba. " An ya gurina kuka zo ko kuma kun yi makuwa ne wata ila tambaya ce da ku." " Ka na shakkun mun zo gurin ka ne mu ba mutane ba ne? Ko aljanu ka gani." A.m ya ce mishi ba tare da ya kalle shi ba hankalin sa na gurin wayar sa dake hannun sa ya na daddannawa. Baba Sani nan take ya ji ran shi ya ace ya kalle sa a ran sa ya na fa in." Ba ka sanni ba kenan amma bari na ji da wanne kuka zo." " Gashi kuma sauri nake zan tafi aiki sai fai ku dawo wani lokacin." Ya ce fuskar sa a aure ganin A.m ya zo da rainin wayo.Am ya bu e baki zai yi magana sai A.k ya watsa mishi kallo kuma aka ci sa'a ya yi shiru ya ci gaba da kallon wayar sa. " Don Allah ka yi ha uri ka bamu an mintina kamar yadda na bu ata da farko ka saurari abin da yake tafe da mu." A.k ya ce cikin marairaicewar fuska ya kuma ha a hannun sa biyu ya na ro on sa.A.m kuwa kofar gidan ya din ga bi da kallo ya na jin wani tsigar jikin shi na tashi,wai shi zai ha a jini da ar wannan wula antaccen gidan mai kama da bola,duk da Baba Sani ya na arin gyarawa amma abincin wani gubar wani. " Ok to muje in har zaku ta aita maganar da ta kawo ku a cikin lokacin da kuka iba." " In sha Allahu." A.k ya bashi amsa a lokacin da suka shiga cikin gidan zuwa akin Baba Sani A.m ya na ta wul ita ido ko zai ga Juwairah don shi yanzu ma ya manta da kamannin ta. "Maza ku gaya min mai yake tafe daku da farko ina fatan ba laifi na yi ba kuka zo kama ni."Ya fa a kamar kuma ya ji tsoro a fuskar sa. Hakan ya sa A.k ya murmusa shi ko A.m ko kallon sa bai yi ba.A.k ya gyara zama ya kalli Baba Sani ya ma rasa yadda zai fara ya na son ya ce A.m ya fa i bu atar da ta kawo su,amma ya san dun ula maganar zai yi ta yadda ma ba zai fahimce shi ba ya lalata abin,bayan dai in ina da ya yi,ya kuma shiga umbiya- umbiya daga arshe ya fa i abin da ya kawo su don barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Alokacin da Baba Sani ya ji maganar da A.k ya fa a sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba. " Ikon Allah bayin Allah don Allah ka ara maganar wallahi ban ji me ka ce ba yadda ka san ciwon kurumta ya kamani,a lokacin da ka yi maganar sake fa i kamar yadda ka fa a kuma da Hausa don Allah ba turanci ba. A.k ya so ya yi dariya jin ya ce ya yi magana da Hausa ila in ya ara maganar da larabci zai ce ya yi mishi,A.m ya mai da wayar sa a aljihun rigar sa shi bai ga dalilin da A.k zai tsaya ya na an waken zagaye ba,ya san a ran shi irin abin da suka zo mishi da shi bai isa ya hana auren Juwairah ba " Auren Juwairiya kuka zo nema!" Ya maimaita hakan ya fi sau ba adadi daga bisani ya mi e zubbur ya na fa in." Haba dama na yi tunanin a lokacin da na ganku irin yaran manya ne da suke shaye-shaye su yi atan kai su dami mutane,kun ga tunanina ya zama gaskiya ga ku kamar mutanen kirki ta waje amma ta ciki ba hali." Ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya ba su ikon koda jan numfashi ba." Wallahi na auka wani abin ya kawo ku ko ba sa rana akan Juwairiya a bazan ta a yadda ta auri wani daga cikin ku ba,bare na ba da Juwairiya yanzu haka bikinta saura sati aya don haka ku wuce ki bani guri waya kawai." A.m ya harzu o ya na fa in." Wa kake ce ma waya kai ne mugun waya da ka kasa gane mutanen kirki da na banza,ba giya muke sha ko kuma kamfanin wayar muke ha iya." "A.m ya kamata ka saukar da fushin ka kasan me muka zo nema." A.k ya ce mishi tare da kama shi ya zaunar ya na dafa kirjin sa. " A'a ka barshi ya yi min rashin kunya ya biyo ni har gida zai gaya min magana,a akina fa kake.To bari kaji ko mutuwa za kai sai dai ka mutu, kai ko maka mutu ne aka fito da kai a abari,a ka ce na baka auren Juwairiya numfashin ka zai dawo wallahi sai dai a turbu aka a cikin asa ta rufe maka ido." " Wai tsaya kun ma san me kuka zo min da shi?Juwairiya da na tsana a rayuwata shi ne zaka kazo ka na da ku i ka aura ta wallahi ina." Da aka kai wannan gabar sai A.m bai ce komai ba ya rintse idanun shi kawai don aikin A.k ne.Amma sai ya ji A k ya yi shiru ya na kallon Baba Sani da yake fa iri- iri ba ya son ar wansa ta aru,kai wannan wane irin mutum ne an ya a kwai zumunci a duniya saboda son duniya ko ya ce son kai,mutane sun manta zumunci bayan Allah ya gaya mana zamu tsallaka sira i mara zumunci ba zai sha ba. A.m ya bu e baki zai yi magana ganin A.k ya i magana dai-dai lokacin da Baba Sani ya sausauta murya ko me tuna ya sa ya yi sanyi ya ce." To kai in ban da ku me za ku yi da mace irin Juwairiya yarinyar da ta gama zagaye duniya ta na yawon aikatau kuma duk mazan gidan sun san ta,sam ba ta da hali mahaifiyarta ta koya mata bin maza har sata take yi ka tambaya har kulle ta a ka yi a prison." ara sausauta murya ya matsa kusa da A.k don ya fi A.m sau i ya fara magana kamar zai yi mishi ra a amma A.m ya na jin me yake fa i." Ina da yara sun yi karatu na boko in kuma so Juwairiya ba ta san komai ba har talla yi take yi,ai da ka aure ta gara na yi maka fatan ka mutu ba aure. " Juwairah nake so kuma zan aureta ko da ace duk mazan duniya sun san ta a matsayin a mace."A.m ya ce ransa a ace. " To ba zan ba da ba kuma kamar maganar ta
Chapter 28 · 0% Book details