Sashe 8
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *SHAFI NA SHIDDA* Duk yadda Juwairiya ta so ta kwantar da hankalinta akan mutuwar mahaifinta, abin ya ci tura!Da ta tuna mugun nufin Baba Sani sai ta ara rikicewa,irin yadda ta nuna na rashin tawakkali ya so ya fara tunzura Mama tun ta na ba ta ha uri, ta taushe tashin hankalinta domin Juwairiya ta natsu amma ta kasa,sai uhu take ta na furta sunan Baba. Ganin irin abin da take yi sai Mama ranta ya ace matu a,ta saki hannun Juwairiya dake son a kyaleta ta fita da gudu kamar wata kamun aljanu tace."Ku kyaleta ta yi duk abin da ta ga dama,ban san baki da tawakkali ba sai yanzu Juwairiya!Na auka saboda arfin imanin ki ni zaki din ga ba ma ha uri,tare da jawo min aya akan na auki ha uri domin duk mai rai mamaci ne." Juwairiya ta du a tare da ara sakin wani kuka dai-dai lokacin da Baba Sani ya araso gun ta ya na mata wani kallo,mai kama da tausayi ko akasin haka tare da sausauta murya yace."Ku kyaleta rashin mahaifi abu ne mai ciwo na tausaya miki matu a,domin hakan da kika yi sai kika tuna min lokacin da mahaifin mu ya mutu ina kuka mahaifinki Yaya Ahmed shi ya dinga lallashina!" Sai ya saka kuka ya na fa in."Allah Sarki!Allah ya ji an ka Yaya."Ya nufo Juwairiya dake kuka tamkar ranta zai fita,da nufin zai ri e ta ya lallasheta. Da sauri ta matsa ta na wani irin kuka kamar za ta shi e,ja da baya take kamar ta ga dodo.Ganin haka sai ya kyaleta a ran sa kuwa murmushin mugunta yake mata.Bayan an gama cuku-cuku aka ba su gawar Baba da har ta fara sandarewa. Hankalin Juwairiya bai ara tashi ba sai da suka dawo gida ta ga inda yake kwanciya,wani arin abin tausayi tun da Ibrahim ya ji mutuwar mahaifinsa ya auke numfashi ko motsi ba ya yi.Lamarin sai ya jagule ma Mama ta rasa in da za ta sa kanta ta ji sanyi,ga wani irin kuka da Juwairiya take yi ta i ta yi shiru. Bayan an yi wa Baba sallah aka kai shi gidan gaskiya gidan da ko wane bawa yake da gadon sa domin ba'a wahala gurin mallakar sa.Cikin dare Juwairiya ta na kwance ta kasa bacci!A ranta ji take kamar mahaifinta kashe shi aka yi musamman yadda ta ga Baba Sani bai nuna tashin hankali game da mutuwar sa ba. Ta na lura da shi har shinkafa ya siyo a dafa ma an zaman makoki,wanda ko mutuwa za su yi ba zai taimaka musu da shi ba. Kwana ishirin da rasuwar Baba amma har yau sun kasa manta shi a kullum ta ranar duniya sai sun yi kukan rashin sa,musamman Juwairiya da yake sokanar ta duk san da zai fita ya na cewa Allah ya nuna mi shi ranar auren ta,a she ba shi da rabon gani. A lokacin da Baba ya yi arba'in Juwairiya ta saka ma ran ta za ta yi fito na fito da Baba Sani duk abin da ya shirya a shirye take ita ma.Tun lokacin da Baba ya rasu bai ara shiga sabgar ta ba,duk da cewar ba ganin ta yake ba don ba ta fita ko ina. Ganin ba su da cin yau bare na gobe sannan Mama ita ma kwana biyu ba lafiya take da shi ba,ya sa za ta gaya ma Mariya ta nema mata aiki ta din ga yi don da yunwa ya kashe ta gara dukan Baba Sani ya kasheta ita ka ai.Ta san ya na hana su abinci ne don kawai ya cutar da rayuwar su ko ya samu biyan bu atar sa,amma ba wai don ba shi da ku i ba tunna aikin gwannati yake yi. Ranar da Baba ya yi arba'in sun sha kuka bayan sun yi mishi saukar alkur'ani suka ha ura da kukan suna mishi addu'ar Allah ya ji an shi. Cikin sa'a bayan kwana biyu da gaya ma Mariya ta nema mata aikatau,ta zo da murnar ta an samu saboda ta na samun aikatau da dama kusan ita dillaliyar masu aiki ne. Tafiyar da Baba Sani ya yi sai hakan ya ba Juwairiya damar ta fara aikin ta cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba.Duk da ita Mama taso ta bari ya dawo su tambaye shi amatsayin sa na mahaifi,amma ta i ta kafe daga karke wasu irin maganganu ta jefa ma Mama wanda yasa ta ji babu da i,a yadda take gaya mishi magana duk da ta san dama ba sa shiri,amma ko ba komai yanzu shi yake da matsayin mahaifinta kuma ko aure za ta yi shi yake da alhakin komai. a sosai ta yi mata don ganin ta a maganganunta har da rashin kunya,wanda hakan bai dace ba musamman shi da yake da matsayi mai girma a ranta.Juwairiya ta ji maganganunta amma yadda ta fa e su haka ta watsar da su a gurin a ranta take fa in."Ta ya ya za'ai na mutunta mutumim da yake da burin ata min rayuwa,ko da mahaifina ne ya bijiro da wannan iyakan abin da zai yi mishi kenan Mama,domin babu biyayya ga abokin sabon halitta!Kema da zaki ji abin da yake so a gareni sai kin yi mishi fiye da nawa." Matar da Juwairya za ta yi ma aiki likita ce a shika ta na da yara uku,a kwai wata mace tsohuwa wacce take mata girki ita kuma Juwairiya aikin ta kula da yaranta mata biyu da namiji aya,in da za ta din ga mata aiki ta na tafiya har islamiya ta saka su tare da yaranta.Ranar da kuma take da aikin kwana za ta kwana da yaranta da safe ta shirya su ta tafi makaranta,wanda ta ba ta za i in ta gama shirya su za ta tafi gida duk da ita matar makaranta ta ba Juwairiya za i ta koma ta zana jarrabawar fita sakandiri. Juwairiya ta ji matu ar da i na samun aikin duk da ta na jin tsoron abin da Baba Sani zai yi mata in ya fahimci ta na aikin.Ta i amince mata kan shawarar da ta ba ta da ta koma makaranta,duk da ita ma ta na da bu atar haka amma ta san Baba Sani ba zai bar ta ba. Sai dai cewar da matar ta yi za ta dinga kwana da yaranta in ta na aiki ya so ya an tsorata ta,amma da ta gaya mata a kwai Baba tsohuwa sai hankalinta ya kwanta don ta yi tunanin tare za su din ga kwana. Juwairiya ta ara son ta yi aikin jin an ambaci ku i mai tsoka,sannan da suka tashi za su tafi sai ta ba ta kayan abinci da ku i naira dubu ta sallami Mariya da tsoka,saboda ta yaba da hankalinta musammam da ta ganta ba ta da azanta. Mama da ta ji aikin har da kwana sai ta fara yiwa Juwairiya fa a kuma tace sam ba za ta yi aikin ba,ta na ta fa a in da take shiga ba nan take fita ba.Ganin hakan sai ta saka kuka ta mi e domin ta yi sallar magariba."Ba gara na zauna a gidan Anty Naja ba tunna na ji Mariya tace mijinta ustazi ne me gamu,akan anin mahaifina dake son ya ata min rayuwa. Juwairiya ta yi tunanin za ta shawo hankalin Mama,amma sai ta ga ta kafe a dokin na i in da ta ara mata da cewar sam ata fau ba za ta yi aikin ba. A ranar da suka shirya da Anty Naja za ta fara aikin,Mama ta kafe ko da Mariya tazo suka lallashi Mama shi ma bai yi wani tasiri ba ganin haka sai ta ha ura,akan ta nema mata wani kawai wanda ba za'a din ga kwana ba. Da maraice ta na zaune akan kujera ta na wanke-wanke sai suka ji sallamar Mariya da wata a bayan ta,da sauri ta aga kanta duk da cewar ba ta yi ma Anty Naja kallon kirki a ranar ba,amma ta sheda ta. A kunyace ta amsa mata sallama tare da yi mata jagora zuwa aki,ta ibo mata ruwa a kofi ta ije mata sannan ta fice daga akin ta na jan numfashi ta ri e turaren Anty Naja da ya ba akin na su,wanda Juwairiya ta so ya dauwama a akin saboda dadda amshin sa. "Ba ki sanni ba ko Mama?"Anty Naja tace bayan ta auki ruwan da Juwairiya ta kawo mata cikin sakin fuska,kuma ta sha ruwan sosai ba tare da nuna yani ko tafi arfin shan ruwan randa,wanda hakan sai ya yi matu ar burge Mama wani arin burgewa ta baje akan tabarma har ta na cire hijabin ta da ankwalinta. Hakan ya yi matu ara burge Mama sai ta ara jin ta saki jiki da ita tace."Bam ma sanki ba yarinya,amma da na ganki da Mariya ar ma ocin mu na gane kece wacce aka yi maganar aiki da Juwairiya..." "Ni ce Mama tabbas ni ce ina ta jiran ta ba ta zo ba,sai da ga ba ya Mariya ta zo tace min kin hana ta "Tace tare da atse Mama ba tare da ta kai aya ba. "Haka ne gaskiya aikin nan ki nemi wata kawai."Mama tace ta an canza fuska ka an,ganin haka sai jikin Anty Naja ya yi sanyi amma saboda ya ba hankalin da ta yi na Juwairiya ta kasa ha uri tace."Don Allah Mama karki hana ta wallahi ba ni da matsala da ga ni har mijina,kuma in kina tunanin kwanan da za ta yi ne mijina ba zama yake ba wani lokacin ni kai na sai na yi bacci yake dawowa." Ta matsa kusa da Mama tare da ri e hannunta ta yi rau-rau tace."Don Allah Mama kar kice a'a ban auki Juwairiya a matsayin me aiki ba anwa ce a gareni,kuma duk ranar da kika ga wani abu ya faru mara da i a tsakanin mu ki hana ta zuwa." Ta yi shiru ko Mama za ta ce wani abu amma sai ta ga ta kauda kanta ta na tunanin wanda ba za ta iya cewa ta yanke ta barta ko a'a."Kin ji Mama ki amince don Allah!Na yi masu aiki da dama amma basa