Sashe 94
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 35* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Zainab zaune a cikin akinta ri e da wayarta,hawaye ne ke sintiri a fuskarta da ta ji e sharkab da hawaye.A ranta tana jin wani irin tsananin ba in ciki da tashin hankali mai tsanani,duk sadda ta tuna abin da ya faru tsakaninta da A m,wanda har yau ta kasa yarda wai a zahirin gaskiya lamarin ke faruwa. " Wayyo Allahna! Da gaske A.m ka guje ni saboda wata a mace marar gata a duniya,da gaske jikinka da na ke kishinsa ka mallaka wa wata mace wula antacciya.Me ya sa ka yi mini haka bayan ka yi mini al awarin ba za ka ta a ha a jikinka da wata a mace ba?" Sai ruwan hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta tana jin tsantsar ba in ciki da kishin Juwairiya a zuciyarta. aran tsa o da ya shigo a cikin wayarta ya saka ta yi tsaki tare da jefar da wayar,wanda ta san A.m ne ya yi,don kusan a rana sai ya yi mata sun fi goma,amma ba ta ta a gigin bu e wa ba.Da wayar a kashe take barin ta sai yanzu da ta ji zuciyarta ta an rage zafi ta kunna ta. " Ba zan aga wayarka ba macuci azzalumi mayaudari! Ka mai da ni shashasha ka sa ina ta iyayi a cikin awayena mijina ba ruwan shi da mata,ni ce mace ka ai birnin zuciyarsa a she banza ka mai da ni rainin wayonka ya fi na kowa,yanzu da wace fuskar kake son na kalli awayena suna fa a musu?Haba ai gara a ce mutuwata na sanar musu." Sai kuma ta mi e kamar wata zararriya ta ara cewa bayan ta fisge an kwalin kanta ta ya mutsa gashinta da ke aure tare da cilli da ribon "Mai ya sa na rayu don na ga ranar da A.m ya yi wa wata ciki bayan ni ba na haihuwa?" Kamar wata zararriya sai kuma ta auki wayarta da sauri tare da arin e sa on da ya yi mata. " Na rantse sai na koyar da ku hankali sai na shayar da ku ruwan ba in ciki saboda girman zunubin da kuka aikata mini." Ta ce sannan ta fara karanta tsa on cike da jimami da tashin hankali bayyane a fuskarta. (Zainab don Allah ki tsaya ki fahimce ni tabbas na san ban yi miki adalci ba,amma in kika fahimce ni za ki gane na yin wannan auren ne saboda ke."Kalar sa onnin da ya turo mata ranar farko kenan.) Wata uwar ashar ta danna masa sannan ta bu e na gaba. (I dan son Juwairiya nake yi ta ya ya za yi na ije ta a gidanki a matsayin mai aikin gidanki,haba ya kamata ki gane na yi hakanne duk saboda ke.Kin san irin yadda nake son yara .Kin ji na rantse miki da zarar ta haihu zan saketa kuma na ba ki yaron da ta haifa, ta fita daga rayuwarmu domin an halicci rayuwata da ke ka ai.) Ire iren sa onnin da yake yi mata kenan wa anda ba ta dubi zuwa gare su,sai yau ta fara dubawa domin ta gaji da zama ita ka ai zuciya da gangar jiki sun yi rashin sa,da zarar ta yi shiru muryarsa take mata amsa kuwwa ma kunnenta. " Ka cuce ni!Da na yanke rabuwa zan yi dakai sai dai na lura ba zan iya yin haka ba,domin kai ne namiji na farko wanda na ji zan iya mutuwa akan sa,amma mai ya sa ka za i ka cutar da ni bayana ka san ina son ka matu ...." " Mijin na ki za ki yi fushi ki bar ma wata! Lallai ba ki da hankali." Momi da take tsaye ta har e hannunta a irji tana jin abin da take cewa,ta tambayeta da mamaki a fuskarta. "Momi ya kike son na yi A.m ya cuce ni bazan iya yafe masa ba." Rungumeta ta yi tana rarrashi ta ce." Na yi magana da Hajiya rabi gobe za ku je in da na gaya miki s..." " No Momi na gaya miki ba zan ata aurena da wannan ba in har ba za ki taimaka mini,ta wata hanyar ba to ni zan koma akina na rantse sai na ga bayanta,da kaina zan auki mummunar mataki a kanta.Ita da abin da ke cikin zan bankawa wuta duk su on..." " Rufe mini baki banza kawai shashasha! Ana nuna miki hanya ki na kaucewa ki je ki yi duk abin da kika ga dama,ai dama da za ki aikata ba ki nemi shawarata ba,wai ke da i miji ai gayi nan in da ya kaiki,duk abin da kika ga dama ki je ki yi,amma ina tuna miki mundin kika salwantar mi shi da ciki ba zai barki ba.Ita yarinyar kin san ta yadda suka yi har ya aureta kasancewar ta ar matsiyata." Fuuuu! Ta fice daga akin ranta na zafi sosai saboda gani take ba ta da wayo,da ba zata bi hanyar da ta saka ta ba don ita ce kawai mafita a garesu. Sai ta kife kan gado tana kuka domin duniyar ta yi mata zafi sosai. Kusan sau uku yana kiran wayar ba ta auka ba,sai a na hu u kamar an saka ta dole ta janyo wayar tare da kanga ta a kunninta. " Munafiki mayaudari mai za ka ce mini na baro gidanka ba za ka bar zuciyata ta samu sausauci ba."Ta fa a a zafafe da acin rai. Ya saki naunauyar ajiyan zuciya mai arfi wace ta ta a zuciyarta,ya rintse idanunsa yana jin zafin abin da ta ce mi shi,amma sai ya daure ya ce da murya sansanya. "Zainab please don Allah kar ki kashe waya ki bari ki saurari abin da zan gaya miki don Allah!" Tsaki ta yi ta yi shiru ba tare da ta tanka masa ba. Ya cire wayar a kunninsa ya kalli wayar don a tuninsa ta katse wayar,amma sai ya ga ba ta yanke ba,sai ya fara magana da muryar da ya san yana kashe mata zuciya,yake kuma narkar da bargon soyayyarsa ya zagaye duk wata kafa da take jikinta har ta kasa gane girmar laifin da ya yi mata. " Kin san Allah ya jarabce ni da son yara ko?Sannan ki duba irin tarin dukiyar da nake da shi,amma ba ni da magaji Zey ba kya tausayin rayuwata,ke kan ki ina za ki kai umbin dukiyar da kike da shi?Sannan in muka mutu ba mu da wanda zai rin a yi mana addu'a,duniya za ta manta da mu." Ya numfasa ko za ta ce wani abu amma sai ya ji ta yi shiru don ji take kamar ta sha e shi ta wayar. Wannan dalilin ya sa na ga da in ce miki mu yi adopting yaro a gidam marayu, na ga dacewar kawai na auri mace na siyi an da za ta haifa." Shiru ta yi bayan ta ji duk abin da ya ce zuciyarta ta kasa yadda da lamarin da ya fa a,ba rashin son a da ba ta yi bane ya dameta don ba za ta iya wahala da shi ba,amma kuma wannan ba matsala ba ce saboda za ta iya aukar mai aiki ta kula da rayuwarsa,to amma ita Juwairiyar za ta iya auke idanunta daga gareshi." Abin da take ta tunani kenan a cikin zuciyarta, sannan kuma mai ya sa bai gaya mata ba tun lokacin,sai kawai ta sauke ajiyar zuciya mai arfi. Kamar ya san abin da ke zuciyarta ya ce." Na i gaya miki ne don ba lallal ba ne ki amince,sannan kuma idanuna sun rufe sosai ina son na ga yarona a ha a sunana da na sa,idan kika san Juwairiya matsayin matata ba za mu ta a samun zaman lafiya,ga shi rashin fa a miki bai yi amfani ba saboda na so ace cikin arya kika yi lokacin da ta samu ciki,sai mu yi aryar ciki har ta haihu." Jikinta ya ara yin sanyi matu a kamar wacce ta fito da ga firjin. " Haba dama na san A.m ba zai ta a cin amanata ba sai yana da dalili ga shi yanzu ba in kishina ya saka na je na tona asiri,da yaron ni zan ce na haife shi."Ta ce take wani irin mugun nadama ya shigeta ganin yadda ta kwafsa gefe guda kuma sai ta ba shi laifin in gaya mata da ya yi. " Ki yi ha uri ki dawo gareni ji nake kamar zan mutu na yi rashin wa annan hot kis na ki masu zafi da sanyaya zuciya,yanzu aikina ya are da ita ko kallonta ba zan ara ko kallonta ba ke ka ai ce matata."Ya ce mata da salon muryar shi da yake rikita ta. " Na ji zan dawo duk da ka zubar da imata a idanun duniya amma ta zauna a gidanku har ta haihu in ya so sai a bani yaron ita ta tafi." Gaban sa ne ya fa i ras!Amma kuma ba zai iya gaya mata gaskiya ba,gara in ta dawo sa fuskanci wannnan matsalar. " Ba ki da matsala na zo na auke ki?"Ya ce zuciyar sa da fargaba. " Ba yau ba." if ta kashe wayar tana jin haushin sa matu ar gaske domin ya zubar mata da ima a gurin mutane. A.m ya ri e waya yana kallonta sororo har yanzu zuciyarsa bugawa take yi,ya san in ta dawo ta ga Juwairiya a kwai dirama,balle ta ga yadda ta koma ta yi wani irin kyau komai na jikinta ya bu e shi kan sa baya iya auke idanunsa a kanta. Mai da wayar ya yi cikin aljihunsa ya fesa turaren da ya zamar masa dole,tun ba ya son amshin har ya fara so don babu yadda zai yi,sai ya fara saukowa asa zuciyarsa na ta " A.m!" Ta kira sunan shi da arfi kuma cikin isa da gadara ba tare da ko an girmamawa ba,ganin yana son ya fita bai kalle ta ba,duk da ya ganta a falon. Wani irin kallo ya yi mata ganin yadda ta zauna a falon riga daban zani daban sai hular sanyinsa wacce ya ba ta saboda jin sanyi da take yi,tana ri e da remote a hannunta fuskarta