Sashe 100
Sakacina Ko Halin Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 37* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Zainab da ke kwance ta mi e cikin tashin hankali jin arar A.m ta ruga akin da gudu.Abin ta gani ya yi matu ar razana ta, ora hannunta ta yi aka tare da sakin ihu,saboda ta rasa me za ta yi. Girgiza sa ta fara yi tana fa in." A.m ka tashi don Allah kar ka mutu ka bar ni!Ka san ba zan iya rayuwa babu kai ba." Ta kalli Juwairiya da take cikin wani hali gani ta yi kamar babu rai a jikinta,sai jikinta ya kama rawa ta rasa ba in ciki za ta yi?Ko akasin hakan. Dabara ta fa o mata ta ruga da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa. e idanunsa ya yi da sauri tare da mi ewa ya kamata kamar zai allata ya ce." Ina Juwairaaah ta mutu ko?" Zainab da ta kasa magana idanunta ta kai gurin da take kwance rai kwakwai mutu kwakai. Da sauri ya bi in da ta kalla da idanunsa sai ya mi e zubbur ya nufe ta ya auke ta zai fita da ita. " A.m dare ya yi fa yanzu ina zaka kai ta?" Ta yi masa tambayar da ko kallonta bai yi ba ya fice,ba ta ankara ba sai jin tashin motarsa ta ji ya fice da ga gidan. A.m da yake tu i cikin tashin hankali Allah ne kawai ya kai shi asibitin. Ba tare da ata lokaci ba likitoci suka rufu a kanta,wacce ba ta san halin da take ciki ba. Jikinsa har rawa yake yi wani irin tashin hankali ya ziyarce shi,ji yake kamar zai yi hauka,domin ya rasa asarar babyn insa ne bai so ya yi,ko halin da take ciki ya saka shi cikin wannan halin. Wayarsa ya zaro a cikin daren ya kira A.k ya fi sau goma sai dai bai aga ba,sannan ya kira iyayensa ya sanar musu. Ya yi shiru yana tsaye a gurin akin da aka kwantar da ita sai le e ta windo yake yi,amma duk iya arin da likitocin suke yi ba ta farfa o ba,sai ya du ar da kan sa yana jin tsananin tausayinta,yayin da hawaye yake bin uncinsa. " Na shiga uku! Yanzu in yarinyar nan ta mutu ya zan yi?" Ya tambayi kan sa cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa. Salati ya ji tana yi cikin murya asa- asa sai kawai ya danna cikin akin ya dur usa a kusa da gadonta ya kama hannunta ya ri " Juwairiya ina son ki!Ina son ki!! Ina son ki!Kamar yarda kika fa a mini na maimaita miki,na ro e ki don Allah kar ki mutu ki bar ni wallahi ina son ki,ban san cewa son ki nake ba sai yau da na ga za ki mutu ki bar ni.Na ha ura da baby kar ki mutu don Allah ki tashi zan rayu da ke ko da ba za ki ba ni baby ba." Cikin wata irin murya yake maganar yana ji kamar ciwon ya dawo jikinsa,ganin yadda take shan wahala matu Juwairiya ta bu e baki za ta yi magana amma sai wani irin nishi ya hana ta,ta rufe bakin da sauri tana salati a ranta,don ta sada ar mutuwa za ta yi,wannan nishin na cire rai ne. Kawai sai suka ji kukan jariri yana ta tsala kuka sosai duk ya cika asibitin da ihu. A.m ya saki hannunta da ta rufe idanunta jin wani irin ciwo ya ta so kamar ba ta haihu ba. Ya kai hannun da sauri zai auki babyn yana fa in." Alhamdulillahi adada ma khala Da sauri wata nurse ta riga shi aukar babyn,sai ya du asa yana jin kamar an yi masa bishara da gidan aljanna. " Doctor Marwan ina ga kamar an biyu ne za ta haifa da wani jariri a cikinta." Doctor Bilal ya fa a cikin razana ganin ciwo ya koma sabo. " Anya kuwa ba na tunanin haka saboda scanning inta ya nuna mana yaro aya."Ya ba shi amsa da shakku a fuskarsa. Tun suna tunanin cewar mahaifa ce za ta biyo har suka yadda an biyu a cikin. Ganin irin wahalar da take sha A.m kuma kamar zai zare kamata ya yi ya ri e,sai murna ta koma ciki. Likita ya bada umurnin a fitar da shi saboda yana ata musu aiki,duk lokacin da ya ga sun danna cikinta ta saki ara mai razanarwa,sai ya ware zai bugi likitan. Duk yadda likitan ya so ya raba hannun su, amma ina ya asa saboda sun ri e junansu am,sun i saki daga arshe kan dole ya yale shi. Duk iya arin su jaririn ya i fitowa,amma kuma in suka saka hannun suna ta a kan sa. Hankalin su ya tashi matu a gashi a lokacin arfinta ya are,ko motsi ba ta iya wa balle ta yi nishi,sai idanunta da take wul ita su cikin ra in azaba. " Ina gani ya kamata a kira doctor Garkuwa don shi kawai zai iya maganin wannan matsalar, ila ya ce a shirya mata aiki fa,domin ba ta da arfin da za ta iya nishi yaron ya fito."Doctor Bilal ya ce da doctor Marwan. " Ba ya asar ka san ya yi tafiya zuwa asar America akan wallon gasar afa da zai buga." " Kai wai me ya saka doctor Garkuwa yake yin haka! Sai ka bu e asibiti amma ba za ka rin a kulawa da patient ba,kullum ba shi da aiki sai zuwa asashen waje akan wallon banza,wanda iyayensa ba sa son yana yi Yanzu ya yake son mu yi da wannan baiwar Allah da take cikin wani hali?"Ya fa a cikin tashin hankali. " Waye wannan Garkuwa mahaukaci ne shi zai fifita wallon afa akan mutane?Na rantse in ya kashe mini mat a sai na kashe shi ko kuma kotu za ta raba mu."A.m ya ce cikin hargowa bayan ya sha e likitan. yar ya wace kan sa ya ce." To sakar mini riga shi ma an zafin rai ne kamar kai sai ka bi shi can ku arata."Ya ce tare da wace rigarsa. " A nemo amininsa doctor Isa abin takaici jiya ya gama duting dar." " Ashe asibitin mahaukata na kawo matata ba ku da hankali,asibintin ya zama yali banza,ba ku damu da halin da take ciki ba,to bari na gaya muku in har Juwairiya ta mutu kuma duk sai na kashe ku." Likitan ya bu e baki zai yi magana da fushi ganin ya raina arin su,sai suka ji kukan jariri da ya kusan fa owa asa,wanda taimakon Allah kawai ya fito da shi daga cikin. " Wayyo Allah na! a biyu! Wallahi a biyu kika haifa mini gaskiya aurenmu mai albarka ne." A.m ya fa a yana kallon jaririn da ya daina kuka saboda wahalar da ya sha. " Na yi mata allurar tsaida jini amma ya i tsaya fa."Nurse in ta ce cikin tausayin wahalar da take sha. Shiru kawai ya yi ya tsaya yana tunanin wace alllura zai ara yi mata,kafin wannan mahaukacin mijin na ta ya farga. Hankalin su ya tashi warai duk yadda suke oye- oye sai da ya fahimta,ya ri e hannunta am yana hawaye." Juwairaaah na ga tashin hankalin dama haka mata suke wahala in za su haihu? Allah Sarki Momi zan kasance mai yi miki biyayya har arshen rayuwa,zan miki duk abin da kike so duk da na san ko mai na yi miki ba zan ta a biyan ki ba.Bazan raba ki da yaran ki ba Juwairaah domin in na yi haka Allah sai ya hukunta ni,wallahi kin biya ni komai da kika haifa mini yara har biyu duka maza." aramin wahala su ka yi ba kafin su tsaida jinin,don har idanunta sun fara afewa. Ya tsura mata idanu yana kallon fuskarta da idanunta ke rufe tana saukar da numfashi a hankali. Kiran sallar asuba na farko ya sa shi ya mi e sai kuma ya kalli jikinsa,ba tare da ya shirya ba dariya ta kama shi ganin duk wannan diramar da ake kayan bacci ne a jikin sa. Wayarsa ya auka yana kiran mutane yana gaya musu,don a ranar har wanda bai kamata ya gaya wa Juwairiya ta haihu ba,sai da ya gaya musu,saboda in dai zai ga numba a wayarsa sai ya kira ya fa a musu. A.k ya fara isowa cikin asibitin kafin ya shigo sai ga motar su Daddy kowa yana rige rigen shiga,don ko gaisawa ba su yi da junan su ba. " Wallahi ta haihu ka gan su ni ma na zama Baba Allah Daddy za su rin a kirana suna gudu suna bina,kuma fa kama da ni suke yi har da tabon fuskata."Ya ce da A.k da ya sawo kai cikin akin yana nuna masa yaran da suke cikin shawul,duk da ba su taho da kaya ba,amma tsarin asibitin ne komai na bu ata a kwai. " Ikon Allah ka ga sabon shiga yara biyu a lokaci aya! Gaskiya Juwairiya ta iya haihuwa.Amma na kasa gane tsakanin kai da ita wanda ya yi na udar duba ga yadda jikinka ya ace da jini."Ya fa a yana dariya bayan ya kar i yaran a ran sa yana ta ya amininsa murna. A.m ya ji kunya sosai saboda iyayensa da suka shigo shafa kan sa ya yi ya ce." Bari kawai ar albarka ta ci ba ar wahala,amma duk da haka bayan shekara za ta rin a kawo mini kyawawan yara irin wa annan." Momi kuwa rungume yaran ta yi ta saka kuka sosai." Ikon Allah ashe a kwai ranar da zan ga yaranka Abdul,sam ba ka kyauta mini ba da ka oye mini wannan lamari,don kawai ka birge wata mace can wacce ta cuci kanta da kanta,wai kai an soyayya haka kawai ka hana ni ganin sanyin idanuwana jikokina."Momi ta ce tana goge hawaye. " Sha kuruminki Momi duk da cewa ana shan wahala amma duk shekara za ta rin a kawo miki irin wa annan."Sai ya ha a hannunsa ya kama mahaifiyarsa ya rungume yana hawaye. " Momi tabbas na ara girmama lamarin uwa a raina ashe haka mata suke shan wuya kafin su haihu!Mutuwa ce kawai ba ta yi ba.Momi zan miki biyayya har arshen rayuwa,ko da wuta kika tura ni zan shiga." Kama hannunsa ta