Sashe 96
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Kallon rashin sani su ka yi masa. Ya murmusa ya ce dama basu san shi ba. Shi kuma bashi da wata alaƙa da donor ɗin. Amma ga saƙon da ta ce a kunna musu idan an fito. Daga gyaran muryar Mubina ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba da ta gane Yaya ce.
(Assalamu alaikum wa rahmatullah. Suna na Khadija Yusuf wadda aka fi sani da Jinjin matar Habibu.)
"Wannan ba muryar Yayan Hamdiyya bace?" Umma ta soma magana da wata irin kaÉ—uwa.
"Ku saurara" Alhaji ya karɓi wayar don ji yayi duk wani gashi na jikinsa ya miƙe tsaye.
(Na bawa Kamal ƙoda ba bisa tilastawa ko cinikayya ba. Cikin Hikimar Allah maigidana ya biya min kuɗin Umara da tanadin shekaru. Sai gashi ina zuwa Allah Ya yi sanadin da naga Kamal a yanayin da nayi imanin ƴan uwansa na gida basu sani ba. Kuma ni kaɗai ce Allah Ya ni'imta da damar taimaka masa a kusa. Lallai Girman Ubangijina ba abin wasa bane. Ya tsara komai daki daki ni wace ce da zan fahimci hakan kuma na juya baya? Na aminta saboda Kamal na zo a wannan rana. Allah Yasa lafiyar ta samu. Ina fata mahaifinka ba zai ƙyamaci rayuwarka da ƙodar miskiniya ba. Abu na biyu kuma idan ban tashi ba don Allah ku faɗawa Abban su Sajida ba a bina bashi kuma ni ma bana bi. Na sallami kowa kafin na taho. Akwai banki a ƙasan gadona. Na tanadin auren Halifana ne. Sajida, Hamdi da Zeenatu don Allah ku haɗa kai ku zama sirrin juna da ƙaninku. Ina yi muku fatan Allah Ya albarka ce ku a duk inda kuke. Allah Ya tsayar da ku duka akan ƙafafuwanku ta yadda babu wanda zai zamewa wani nauyi a gaba balle har ya ƙosa a sami tawayar zumunci. Ku bawa Abbanku goyon baya ya sake aure. Yaya Habibu Allah Ya gatance maka kamar yadda kayi min. -Cikin kuka ta cigaba da magana- bakina ba zai taɓa daina yabonka ba har numfashin ƙarshe. A wajen wasu ka gaza, a wajena kuwa a wannan zamani babu mai martaba da daraja kamar ka. Allah Yasa Habibu ne mijina a lokacin da Allah Ya sabunta min halitta da miƙaƙen jiki a aljanna. A ƙarshe don Allah ku roƙa min gafarar iyayena. Ku cewa Baba ina gaishe shi. Ku bawa Innata haƙuri.) Sai ta ɗan ja hanci (umara na zo ashe bani da rabon ganin ɗakin Allah da ziyarar masoyina. Amma Alhamdulillah. Kamal da zuciya ɗaya zan taimaka maka. Allah Ya bamu alkhairi. Nagode.)
Audio ɗin a nan ya ƙare. Mal. Salisu ya faɗa musu yadda ta sanar dashi zuwanta asibitin. Mubina ta biyo ba tare da ta sani ba.
"Wallahi ban sani ba. Kuma ni bamu yi zancen da ita ba." Mubina ta faÉ—i a ruÉ—e.
"Hikimar Allah aka ce Dr. Mubina. Magana ta ƙare." Inna ta faɗi tana ɗan bubbuga mata baya.
Alh. Hayatu kuwa juyawa yayi zai bar wajen. Ahmad ya bi shi da sauri. Su Hajiya ma tambayarsa au ke yi ina zai je a wannan yanayin.
"Ashe duk baku ji lokacin da ta ce Umra ta zo ba?"
"Mun sani dama. Taj ya so mu jinkirta tahowarmu tunda ita kaɗai ce mu ka ƙi. Ashe saurin da muke yi ita ce maganin komai."
"Ahmad samo min mota na koma hotel na sako harami na."
"Alhaji..." Inna ta soma magana.
"Idan bata tashi ba fa? Umrar zan yi mata. Ai ya halatta ka yiwa wanda bashi da dama ko?" Yayi tambayar ga Mal. Salisu.
"Ana yi."
"Nima zan yi mata" Hajiya ta share hawaye ta miƙe tsaye.
"Nima"
"Nima"
"Nima"
Sai da ya rage Bishir kaɗai sannan Alhaji ya ce ya haƙura kada a bar asibitin babu kowa. Ahmad ma zama ya yi saboda Alhaji ya bashi aikin neman visa da ticket ko nawa za a kashe domin kawo Abba Habibu.
Da su ka fita a mota abin mamaki ga iyalinsa dake baya bai wuce yadda yake ta goge idanunsa da bayan hannu ba. Yau Alh. Hayatu ne yake kuka akan wani ba jininsa ba. Tun yana yi a zuci har ta kasance suna jin shessheƙarsa. Wannan yasa babu wadda bata bayyana nata kukan ba. Direban tasi ɗin yana son tambayarsu amma kasa. Sai haƙuri kawai yake basu.
Jiransu su ka buƙaci yayi su ka shiga hotel ɗin su ka yi haramar Umra kamar yadda yake a tsare cewa mai shiga Makka daga Jeddah nan ne Miqatinsa. Mutum biyar su ka fito a tare. Alh. Hayatu, Haj. Gambo, Mama A'i, Umma Jamila, Inna Abu da Sulaiman Hayatu Sule (Abba) da niyyar yiwa Jinjin ɗin Abba Habibu Umra a ƙasa Mai Tsarki.
_In sha Allah last post ba zai kai Lahadi ba._