← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 96

Sashe 12

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina za ki baki jera min ba?"

Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin. Ƴan ɗakin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah. Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta ɗebo mata ruwa. Ta amsa kawai ta fita.

Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu. Da haɗa hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso. An soma yayyafi ga iska mai ƙarfi. Saboda haka akwatin da jakar sun yi buɗu-buɗu. Zuciyarta a ƙuntace ta tafi nasu hostel ɗin. Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dunƙule jikinta tana kuka. Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko ɗago kai bata yi ba. Sai wata ce da taga yadda ta dinga ɗiban kayan Ummi ta basu amsa.

"Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa."

Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta faÉ—a musu me ta gani. Abin bai yi musu daÉ—i ba domin kuwa Hamdi bata rigima.

"Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya."

Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama. Su ka taru su ka gama ɗebe mata albarka (mu guji irin waɗannan laifukan da bama ɗaukarsu a bakin komai. Babu wani haƙƙi abin rainawa) sannan su ka watse.

RAYUWA DA GIƁI 7

Batul Mamman💖

Sanarwa
In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma'a.

***

Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran ɗalibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita ɗin dai take nema. Wanki harda na su pant ita take mata. Su ɗebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taɓa faɗin wata kalmar neman sauƙi ba. Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba.

Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu ƴan kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC. Kowa ya duƙufa da karatu ba ji ba gani. Waɗanda basu ɗauki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi.

Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa. Abin ka da lokacin zafi. Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai. Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dauɗa wanda zai iya sati bai kwanta ba. Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba. Ga ɗan karen zafi ana ta zufa. Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin ruwa har bakwai a bayanta. Yara sai murna. Aka umarci malamai da su kula da ɗaliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu. Sannan an ja musu kunne babu mai ƙarɓar ruwa sau biyu. Kuma bokiti biyu kaɗai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa.

Layi layi aka jera ɗaliban na ajujuwansu. A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da huɗu a layinsu. Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta. Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata. Ta ɗauki bokatan hagu da dama ta wuce ɗaki. Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel ɗin ta hango Ummi da ƙawayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya. Fuska a haɗe Ummin ta tarbeta da ta ƙarasa.

"Kin daÉ—e a layi gaskiya. Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?"

Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta alƙawarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba. Jikinta gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mata. Ga ƙishi ga yunwa.

"Ban iya ba."

"Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci."

Wata zaƙaƙura ta ce "Ummi kin ce fa nima za ki sa ta ɗebo min."

"Ki bari ta juye min mana." Ta cewa wadda tayi maganar a wulaƙance.

Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sarƙe hannu a ƙirji.

Rai a ɓace ta ce mata "Ɗauki mu tafi mana."

"Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu. Har ticking suna ake yi."

"To sai ki san yadda za ki yi. Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji."

Hamdi ta rasa daga ina take jin wani ƙwarin gwiwa kawai ta ce "naga kamar baki gane ba. Wannan ruwana ne. Ki je ki ɗebo naki."

Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa ƙirji "dani kike? Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka ɓata min rai?"

Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo É—in ba.

"Kin daÉ—e baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba."

"Kanbu, dani kike?" Ummi ta faɗi cike da mamaki. Sai kuma ta fasa faɗan ta ce ƙawayenta su ɗauko bokitin.

Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar durƙusawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta.

"Wallahi ba zan baki ruwan nan ba."

Mamakin me Hamdi ta taka a yau ne ya kama Ummi. Taga gara ta nuna mata idan tace za ta yi abu lallai babu fashi. Waya ta ɗauko daga aljihun wandonta na kayan prep. Gaban Hamdi na faɗuwa amma idonta yau ya ƙeƙashe. Tana ji kamar kowa muryar Abbanta ta ƙarade wurin. Kan kace meye wannan ɗalibai sun taru suna jin bayanin Ummi na cewa wannan zuƙeƙiyar muryar fa ta mahaifin Hamdiyya Habib ne wanda ya kasance ɗan daudu. Aka dinga tururuwar leƙa bidiyon ana cewa ga kama nan.

Kallon Hamdi aka fara ana zunɗe tayi kamar bata jinsu duk yadda ranta ke suya ta duƙa za ta ɗauke ruwan sai taji Ummi tayi wata maganar da ranta ba zai iya ɗauka ba.

"Mamanta kuwa cangal ce mai ƙafa ɗaya da kwata" ta cilla ƙafa ɗaya ta banƙaro ƙirji ɓari ɗaya "idan tana tafiya sai ka rantse Awilo ne zai yi rawar waƙarsa."

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Hamdi ta iya faɗi don dariyar da aka tuntsire da ita a yayinda Ummi ke kwatanta tafiyar Yaya ta mugun baƙanta mata rai. Sakin bokiti guda tayi ta ɗaga ɗayan da hannu biyu ta juye shi tas akan Ummi. Kowa kuma sai ya bar abin da yake yi aka tsaya kallo.

Ummi bata gama dawowa hayyacinta ba Hamdi ta cakumi wuyanta ta soma kai mata duka. Dambe sosai ya ɓarke a tsakaninsu inda Hamdi ta dinga tumurmusata da ƙasa. Tunda kayanta a jiƙe suke sai jikin ya yi futu-futu kamar an tonota daga rami. Ƙawayen Ummi da suka ji ta fara neman ceto ne su ka ƙwaceta sannan su ka yiwa Hamdi taron dangi. Mutum uku ne su ka danneta a ƙasa suna duka. Ƴan hostel ɗinsu na ganin haka su ma suka saka hannu wurin kai mata ɗauki. Wurin ya hargitse aka dinga ɓarin ruwa ana doke doke.

Prefects ma basu iya yin komai ba sai malamai da aka kira. Duk wadda take waje a lokacin da ƴan kallo da ƴan dambe aka tasa ƙeyarsu sai ofishin Principal.

Baiwar Allah ji tayi kamar ta fasa ihu da taga yadda yaran nan su ka ɓannatar da ruwan da ta wahala wurin nemowa. Ba'asi guda ta nema shi ne su waye su ka fara faɗan. Aka nuna Hamdi da Ummi. Ta karɓi bulala kuwa ta zane musu jiki ta zauna tana haki. Mataimakinta ne ya karɓi shari'ar saboda abin mamaki yau Hamdi yake gani kuma wai ita ta fara faɗan. Duk yadda aka yi a sanin da ya yiwa shaiɗanci na Ummi ya san laifin ba zai wuce nata ba.

Masu tarar aradu da ka ya haɗa da displine master sannan ya zauna sauraron abin da ya haɗa yan matan. Ummi ta kitsa ƙarya da gsskiyarta ita kuwa Hamdi ko tari bata yi ba. Mutumin nan ya kaɗa ya raya amma ƙememe taƙi magana. Sai ajiyar zuciya kawai take saukewa. Waje ya tura su ya tattauna da malamai. Kowa ya riga ya san halin Ummi da Hamdi. Duk da haka tunda Principal tayi rantsuwa ya ce a dubo lambobin iyayensu a sanar dasu ana nemansu washegari Juma'a. Duk wanda bai zo ba ƴarsa ba za ta yi jarabawar da za a fara ranar litinin ba.

Hamdi a yau ko a jikinta. Ta riga ta sanyawa zuciyarta ɓoyon uba bashi da wata fa'ida. Da tun farko ma an san shi Ummi bata isa tayi amfani da wannan damar akanta ba.

A ɓangaren Ummi ne dai hankalinta ya nemi gushewa. Ƙaryarta ce za ta ƙare nannda ƴan awanni. Kiran iyayenta ba baƙon abu bane ko kaɗan. Inda gizo ke saƙar dai shi ne wani Sugar Daddy ɗinta ne yake zuwa a matsayin kawunta. Wai ita marainiya ce. Baba Maje da ke kawota kuma yaron kawun nata ne. Har ila yau baban nata yana karɓar wayarta duk ranar komawa makaranta tun da aka bata wayar. Wadda take amfani da ita ba tare da sanin hukumar makarantar ba wata ƙawarta take bawa ajiya. Babbar waya ce da wani saurayin daban ya saya mata. Tun kafin a dawo taje gidansu yarinyar ta tura wannan bidiyo ɗin da ta yiwa Abban Hamdi. Idan ta kuskura ta bari aka kira wani ba mahaifinta ba Hamdi za ta sami damar da ta zarce wadda ta samu ta cusguna mata. Gumin da ya tsatstsafo mata ta yarfe kafin ta tashi da rawar jiki taje ta sanar da Vice Principal numbar da zai kira a madadin wadda su ke da ita.

***
Chapter 12 · 0% Book details