Sashe 95
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taj ya saki fuska yana murmushi. "Allah ko Mrs Happy?"
"Kana musu ne?" Ta kashe masa iso.
Aikin da take yi ya nemi rabata da shi taki yarda tana yi masa dariya. Yanayin damuwar da ya shiga ya kau. Ya koma tsakaninsu sai tsokanar juna.
"Wannan akwatin kin haÉ—a shi ya kai sau goma."
"Ba fa zan damu ba idan ka tsoka ne ni akan wannan tafiyar. Kuma baka ga komai ba. Rawar kai sai na saka harami." Ta tashi tana buÉ—a kafaÉ—a "kai dai Allah Ya kai mu."
"Amin."
***
Daga airport ya kamata su raba tafiya da Mubina. Su Yaya Madina za su fara tafiya ita kuma cikin Jeddah za ta ƙarasa asibitin da Kamal yake mai suna King Abdul Aziz Medical City. Yadda ta dinga bin Yaya tana taimaka mata da abubuwa duk da cewa abokan tafiyarta ma suna ƙoƙari duk sai ya dami Yaya. Jikinta ya bata akwai wata a ƙasa. Kafin tayi tambayar ne Mubina ta ce za ta shiga banɗaki. Yaya sai ta nemi su jira domin su yi sallama.
Zuciya cike da tunani da fargaba Mubina ta shiga banɗaki. Ta shige guda ta rufe kanta kawai ta fashe da kuka. Duk yadda take son Kamal ta sani cewa idan Yaya mahaifiyarta ce ba za ta yi na'am kai tsaye ta bada ƙodarta ba. Uwa fa aka ce. Ina adalci da sanin ya kamata idanta ingiza wadda bata sani ba tayi abu saboda nata son zuciyar?
"Allah Ka yafe ni" ta faÉ—a tana sake goge hawaye.
Tana buɗe ƙofar tayi ido huɗu da Yaya.
"Lafiya dai ko Mubina? Na ji ki shiru."
Murmushi ta kama yi na dole "abu ne ya shigar min ido. Kin gan shi yayi ja ko? Mu je na É—auki kayana kada na sa ku yi dare a hanya."
"To" Yaya ta ce ba don ta yarda ba.
Da su ka fito taxi Mubina ta shiga. Yaya na kallo motar kawai taji wani abu ya tsungule ta. Jakarta ta hannu ce kawai a jikinta ta dubi matan tawagar tasu ta ce musu tana zuwa.
"Maman Sajida ina za ki?"
"Ku wuce Madinan don Allah. Zan same ku da yardar Allah."
Suna ta tsayar da ita amma ina. Da irin nata saurin ta shiga tasin gabanta ta nuna masa wadda Mubina ke ciki tana shirin barin harabar airport É—in.
"Haza sayyara" ta nuna motar, shi kuwa ya gane ya gyaÉ—a kai "to yalla-yalla, ta'al-ta'al. Kuá¸i, uhmmm, riyalai haqibatun" ta jijjiga masa jakarta.
Bawan Allah damuwar da ya gani a tare da ita ta ishe shi. Kuma duk daƙiƙancin mutum dole ya gane me ta faɗa. Zama ya ce tayi ya kwashi mota su ka bi su Mubina.
Tafiya kamar ba za ta ƙare ba. Wajen minti talatin sannan motar ta tsaya a bakin asibitin. Yaya ta bari sai da Mubina ta shige ta wajen wata ƙofar gilas da wani yaro mai fuskar Taj yake tsaye yana jiranta sannan ta bi bayansu. Haka kawai ta dinga jin faɗuwar gaba. Tana tafiya basu ganta ba har su ka shiga lift. Nan fa ake yinta. Na farko bata taɓa shiga ba kuma bata san inda za su je ba. Ita a tunaninta ma ƙofar ɗaki ce. Ta tsaya a jiki ta fara ƙwanƙwasawa sai ga wani mutum. Ya tsayar da lift ɗin taga ƙofa ta buɗe amma basa ciki.
"Ya Hayyu Ya Qayyumu. Ina su ka ɓace kuma?"
Kamar daga sama sai taji kuka a bayanta. Juyawar nan da za ta yi taga Hajiya ce a birkice. Babu ɓata lokaci sai ta shiga tunda Hajiyar ma ya shiga kuma san bata lura da ita ba. Addu'a take yi tana wani irin kuka. Alhaji da kansa ya yi kiranta ya ce ta dawo jikin Kamal babu daɗi.
"Allah na gatan bawa. Ya Rabbi ga Kamal. Ubangijina ka ƙara rufa min asiri akan ƙaddarar rayuwa. Allah kada in yi saɓo. Ka taimakeni Ya Rabbi. Wayyo Allah. Allah Ka dubi Kamal."
Yaya ta gama sarewa da lamarin nan. Me ya sami Kamal wanda su Taj basu sani ba? Tayi imanin babu abin da zai zaunar da Taj yana raha a gida bayan lalurar da same shi da ya san É—an uwansa yana wani hali.
Da sassarfa Hajiya ta fita daga lift ita ma Yaya tabi bayanta. Don ma tana ɗan jiri saboda rashin sabo. Ƙofar ɗakin a buɗe take. Tana hango Kamal a kwance da likitoci a kansa. Fuskarsa ɓoye cikin abin shaƙar iska. Don dai taji Hajiya ta ambace shi ne ta gane shi. A ƙofar ɗakin Yaya Kubra ce ta rungume Alhaji tana kuka. Inna, Umma da Mama kowacce fuska jiƙe da hawaye. Mubina kuwa gefen bango ta samu tana wani irin kuka a hankali. Bata yi tunanin ƙarasawa garesu ba. Ta tuna kalaman Mubina ne kawai. Wani likita na fitowa daga ɗakin Yaya ta bishi da sauri. Hankalinsa a tashe kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tausaya mata. Saurin da take yi da ƙafarta a haka ya san akwai wahala.
Yaya ta nuna É—akin ta sake haÉ—o larabcinta na islamiyya a karo na biyu.
"Haka gurfa..." ya gyaÉ—a kai "to ma haza Kamal?"
Likitan ya kalleta yana son yi mata bayani amma sauri yake yi. Juyawa yayi sai ta kuma kiransa. Da ya juyo zai nuna mata inda za ta je reception idan taimako take nema sai ta miƙa masa takardar nan da aka rubuta jininta.
"O netif (negative)" ta nuna ƙirjinta "Kamal ahali (ɗan uwanta ne)."
"Alhamdulillah" ya fara cewa zai koma É—akin ta girgiza kai.
"Hausa...a nemo mai yi min Hausa."
"Hausa? Nigeria? Kano?"
"Nace maka ahali ai su É—in" ta kuma nuno É—akin.
Ya gyaɗa kai kuwa ya ce ta biyo shi. Suna tafe yana buge bugen waya. Bata san cigiyar mai jin hausa yake yi ba. Ba a wahala ba ya samu. Mai shara ne amma ya tadi gida. Ba shi da nisa dai. Wuri mai kyau aka bata ta zauna har mutumin ya zo. Ɗan Katsina ne yake aiki a nan. Shi likitan ya faɗawa ya tambayeta alaƙarsu. Sun yi mamakin wai wan mijin ƴarta ne Nan da nan ta faɗa. Sai ya sanar da shi ciwon Kamal da abin da yake buƙata. Yaya ta dafe ƙirji da fari. Sai kuma kawai ta fashe da kuka tana faɗin,
"Allah Hakimu. Allah Hakimu." Daga ƙarshe ta ɗauko wayarta ta nuna nambar Abba Habibu ta ce a kira shi. Likitan da kansa ya kira.
Yana ganin baƙuwar namba ta Saudiyya ya ɗauka. A kiɗime yake sosai. Abokan tafiyar sun kira gida sun ce a faɗa masa abin da ya faru. Bai riga ya sanar da su Sajida ba amma ya gama gigicewa.
"Ina kika je? Kin jefa ni a wani irin tashin hankali."
"Allah Ya huci zuciyarka Yayana Habibu. Tuba nake Abban Sajida."
Murmushi ya yi "yanzu kina ina?"
"Asibiti."
"Baki da lafiya ne?" Ya sake tashin hankalinsa
"A'a, alfarma nake nema domin babu lokaci."
"Kin fara tsorata ni. Me ya faru?"
"Yaya Habibu mijin Jinjin miskiniyar Allah. Da uwata da ubana Allah Ya gatance rayuta da iyayenka. Kirari nake maka mijina a duniya da ƙiyama. Ƙanin Zeenatu uban Zeenatu ɗawisun zuciyata. Domin isa da alfarmar Mai Duka kayi min lamuni in share hawayen wata uwa kamar yadda Allah Ya share mana ranar auren yaran nan"
"Me kike so?" Ya ce da tsinkakkiyar zuciya.
"Ceton rai zan yi!"
"Kiyi min magana yadda zan gane."
"Wallahi ba zan iya ba. Amma ina so ka sani cewa ikon Allah ne ya kawoni ba tanadinmu ba. Komai da yake faruwa damu daga tsarin Mai Kowa da Komai ne."
"Jikina rawa yake yi. Idan na hanaki za ki haƙura?"
"Sosai kuwa. Amma ina da yaƙinin cewa kai ɗin kafi kowa kyawun zuciya a duka mutanen da na sani. Duk abin da za kayi domin ka taimaki wani kana yi. Shi yasa Allah ba Ya barin kowa yaga bayan ka."
"Khadija." Ya kirata da sunanta na gaskiya.
"Yayana." Ta amsa da dakakkiyar murya don bata son komai ya karyar mata da zuciya.
"Ki kira ni idan kin gama. Tsoro mai girma ya shiga zuciyata. Amma naji ba zan iya hanaki ko mene ne ba. Allah Ya baki ikon yin taimakon ba tare da kin wahala ba."
"Amin."
Sallama su ka yi ta ce ta shirya. Likitan ya kira hukumar asibiti ya sanar. Komai cikin gaggawa ake yi saboda Kamal ya kai wata gaɓa mai sammatsi. Aka gama cike ciken takardu sannan aka bata form ta cike da taimakon mai sharar nan da yake karanta mata ya fassara.
Daga nan lab aka je aka yiwa Yaya dukkan wani gwaji na dacewa. Sakamakon da aka samu sai shukura. Likitan ya ce su je wajen su Alhaji ta ce a'a. Kawai a zo ayi. ÆŠaki VIP aka bata ta zauna kafin a shiryo Kamal. Tana zama ta dubi mai sharar nan. ÆŠan dattijo ne kamar Abba Habibu.
"Yaya sunan ka ne Malam?"
"Salisu."
"To Mal. Salisu recoder nake so ka kunno min a waya zan yi magana. Idan an fito daga aikin ka kunnawa su Alh. Hayatu."
A wayarsa ya kunna ya bata. Ta kara a bakinta ta soma magana. Kalaman da take yi sun shige shi fiye da tunani har ta kai yana zubar da ƙwalla.
*
A ƙofar ɗakin su ka dinga zubewa suna sujjadar godiya ga Allah. Likita ya ce an sami donor amma ba a bari sun san waye ba. Mubina sai da ta tuno Yaya. Sai tayi murmushi tana godiya ga Allah da bata yi mata magana ba.
Kamal bai san a inda yake ba har aka gama komai aka shiga tiyata. Kamar wasa sai da su ka kwashi awa huÉ—u ana abu É—aya sannan aka kammala. Addu'a kam da shi da Yaya duk sun sha ta sosai.
*
ICU aka gangara su su biyun domin kulawa ta musamman sannan wanda ya jagoranci aikin ya zo ya sami su Alhaji. Fuskokinsu duka babu nutsuwa. Yana tsayuwa su ka taso gabansa.
"Alhamdulillah, it was a success."
Kowa sai hamdala da ajiyar zuciya suna rungume junansu.
"What about the donor?" Alhaji ya yi tambayar dake gabansa.
"He" likitan ya nuna Mal. Salisu yana murmushi "will explain."