← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 96

Sashe 66

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shakka babu uban Kantin Kwari da kewaye." ÆŠayan ya É—aga hannu yana jinjina masa

"Ka san na faɗa muku akwai wata alaƙa tsakanina da shi."

"Ƙwarai kuwa. Saboda ka ce kuna da dangantaka. Lokacin kuma mu duka bamu shirya barin kasuwa mu zauna a nan ba mu ka bashi. Yanzu gashi cikin ikon Allah ya mallaki kaso ashirin da takwas cikin ɗari. Kasuwa tayi albarka, shi yasa mu ka bari ya zama partner ɗinmu." Na farkon ya yi bayani a taƙaice.

Alhaji ya gyaɗa kai yana tuno wasu ƴan shekaru a baya. Lokacin Ahmad bai yi aure ba amma idan ka ganshi tamkar mai mata huɗu da ƴaƴa goma. Ya fige tamkar kazar mayu. Kullum yana rama ga zafin nema kai ka ce wani yake ciyarwa. Matan gidansu su ka shiga damuwa. Alhaji ya tsananta bincike domin a lokacin Ahmad ƙin faɗa masa gaskiya yayi. Ashe karayar arziƙi ce ta sami Alh. Mukhtar. Mami ta taso shi a gaba. Ashana wannan idan suna buƙata sai ta kira Ahmad. Ita bata yarda tayi rayuwa daidai da samun mijinta ba a lokacin. Ta ƙuntatawa yaron iyakar ƙuntata. Duk wata kadara da Alhaji ya mallaka masa ya sayar ya bata kuɗin. Idan babu yawa tayi ta bala'i da kiran za ta tsine masa.

Ranar da Alhaji ya san gaskiya sai da ya yiwa ɗansa hawaye saboda tsabar tausayinsa da yaji. Gashi kuma ya san cewa ba huruminsa bane raba ɗa da uwa. Shi yasa bai taɓa hana Inna mu'amala da Taj ba. Gidansa kawai ya hana shi shiga. To dama ya san da maganar buɗe kamfanin robobin. A wurinsa ma su ka ranci kuɗin. Shi ne ya basu shawarar ɗauko wanda ya yi boko sosai wato Alh. Mukhtar aka yi masa MD. Yana fara samu Mami ta sakarwa Ahmad mara. Babu wanda ya san maganar nan har yau.

"Ku kaini ofishinsa. Ina son magana dashi."

Da rawar jiki su ka yi gaba. Har yanzu akwai wajen kaso talatin da biyar na kuÉ—in da ya ranta musu da basu gama biya ba. Hankalinsu in ya yi dubu to a tashe yake.

Sun isa ofishin MD inda Alh. Mukhtar na ganinsu shi ma ya tashi da rawar jikin ganin iyayen gidansa. Aka gaisa su ka zauna. Ya miƙowa Alh. Hayatu hannu yaga babu fuska ko alamar zai karɓa. Ba shiri ya ja da baya.

"Wurinka Alhaji ya zo. Ka gane shi ko?"

"A'a" Alh. Mukhtar ya faÉ—i da gaskiyarsa "sai dai fuskar kamar na san mai irinta."

Muryar nan ta Alhaji a dake ta fito ya ce "ÆŠana Ahmad Hayatu Sule Maitakalmi ko?"

Idanu Alh. Mukhtar ya zaro "Alh. Hayatu? Kai ne? Ikon Allah."

ÆŠaya daga cikin Alhazan da su ka zo tare Alhaji ya cewa ya yi bayanin matsayinsa a garesu. Tiryan tiryan kuwa ya yi duk da sun cika da mamaki. Bayan ya gama kana ganin Alh. Mukhtar ka san ya gama rikicewa don gumin da yake ko ruwan sama albarka. Alhaji ya ce waÉ—ancan biyun su É—an basu wuri. Su na fita ya soma faÉ—a.

"A lokacin matarka ta so sabauta rayuwar É—ana. Shi yasa na ajiyeka a nan domin in kare Ahmad. To yau kuma an wayi gari taje tayi abin da ta saba tana neman shiga tsakanin wani É—an nawa da matarsa." Ya yi maganar cikin É—aga murya.

"Alhaji ban sani ba wallahi..."

"Ta yaya za ayi ka sani bayan kaima juyaka take yi?"

"Kada kasa su koreni. Ina da Æ´aÆ´a wallahi." Ya ce hankalinsa na neman gushewa.

"Ka ce ni Hayatu na ce ta karya asirin. Ita ko wani nata sun yi kaɗan su tarwatsa rayuwar zuri'ata. Taj ba ɗanta bane. Idan na ƙyaleta akan Ahmad saboda haƙƙin uwa ne. Amma muddin ta sake shiga rayuwar wani nawa wallahi sai ta ɗanɗani kuɗarta. Ni da kake gani kaza ne akan ƴaƴana. Ina iya taka abuna idan sun min ba daidai ba domin su gyara. Amma idan wani ya kamanta zai sha tsatstsaga har sai anga jini. Ina fata ka fahimceni."

Jikin Alh. Mukhtar babu inda baya rawa. Bai taba ganin mutum mai ban tsoro da kwarjini kamar Alh. Hayatu ba.

"Na gane. Don Allah ka yi haƙuri."

Alh. Hayatu ya tashi "ina son ganin canji a tattare da Taj kafin sati mai zuwa. Ta karya koma me tayi don ta sanni farin sani. Akwai irin abin da bana yafewa. Taɓa min ƴaƴa yana sahun gaba. Sannan ka tashi tsaye kamar kowanne magidanci ka nemi tsari daga sihirice sihircen marasa tsoron Allah."

Ko kallon Alh. Mukhtar bai sake yi ba ya fita. A waje ya yi sallama da alhazawan nan ya kama hanyar Kano ko ruwan garin bai sha ba. Sallah kawai su ka yi su ka tafi.

***

Abu na maza, babu wanda ya yi tunanin raini ko surutu akan gidan Abba Habibu. Irin abin da mata za su yi ta gutsiri tsoma ana cewa me ya kai shi auren wadda bata kama ƙafar arziƙinsa da na iyayensa ba. Ahmad da Kamal sun zo. Sai ƙanin Inna da kuma ƙannen Alhaji guda biyu. Irin tarbar arziƙin da Abba ya yi musu ba ƙaramin daɗi su ka ji ba. Sun riga sun san ko waye, ba a ɓoyewa kowa ba. Ga amininsa Baba Maje, sai ƙaninsa Abdulƙadir da wasu ƴan uwansu maza da su ka lallabo su ka dawo rayuwarsa bayan ganin luɗufin da yake samu.

Abinci ne na gani da fađa su Ƴar Ficika su ka yi. Kuma kamar yadda ya yi alƙawari tuntuni ko hanyar gidan basu zo ba shi da yaransa. Baba Maje ya yi rawar gani ya kawo dubu ashirin a bayar tukwici. Abdulƙadir ma ya kawo sha biyar. Abba ya cike ya zama hamsin. Ƴan kawo lefe kuma su ka ƙi karɓa. Sai da Abba ya ce rainawa su ka yi saboda sun gan shi a haka. Ba shiri su ka karɓa aka rabu a mutumce.

Ko rabin awa basu yi da tafiya ba gidan ya soma cika da Æ´an kallon kaya. Gashi Zee bata nan. Sajida ce kaÉ—ai take ta fama. Sai ga Iyaa ta zo da Siyama da Ummi. Ta kuma umarcesu da taimakawa Sajida wajen saka ido akan kayan da kuma aikin buÉ—ewa mutane.

Ƙiris ya rage Ummi ta haɗiyi zuciya ta bar duniya. Dama Baballe ne ya taho dasu a motarsa. Dolenta ta taho. Yawan akwatunan da irin kayan da ta gani ya birkita mata lissafi. Zuwa yanzu ma dai sakin aure ya kamata su ji anyi. Maimakon haka sai wannan uban kaya kamar za a buɗe shago. Dole ma ta kira Salwa idan sun koma gida.

Abin baƙinciki yadda Iyaa ta ɗora mata aikin kula da wata ƙaramar jaka da aka shaƙare da sarƙoƙin gwal, awarwaraye, zobba da kuma sarƙoƙi na fashion masu matuƙar tsada. Sai da Iyaa ta ƙirga komai harda sanya Siyama ɗauka a hoto sannan ta miƙa mata.

"Ko kwali ne ya ɓata to ku ɓata tare. Ki kula dasu sosai. A nunawa mutane arziƙin Hamdi amma a kula da masu ɗan hali da mahassada."

Ummi za ta iya rantsuwar maganar mahaifiyarta da harshen damo ta fito. Bata sani ba ko tsagwaron baƙincikin da take ji a zuciyarta Iyaa ta gani. Haka nan ta karɓi jakar ba don tana so ba. Irin baƙincikin da take ji ba wai so take ta mallaki kayan ko ta sace ba. Ita da ace za su ɓace ko su ƙone ƙurmus Hamdi ta rasa da ko miliyan biyar aka damƙa mata ba za ta yi farinciki kamar haka ba.

*
Bayan tafiyar Alh. Hayatu, karatun ta nutsu Alh. Mukhtar ya yiwa kansa. Ya dinga haɗa ɗaya da biyu yana lissafin yadda yake aikata abubuwa da yawa bisa umarnin Mami kuma ba a son ransa ba. Ya yarda hannunka mai sanda Alhaji ya yi masa da zancensa na ƙarshe. Ji dai maganar Taj ɗin da ta ce dole ya auri Salwa. Gashi takanas akan yaron mahaifinsa ya zo ya yanka masa gargaɗi mai kyau.

Rasa tudun dafawa yayi ya kira babbar ƴarsa da wani tunsni ya zo masa. A gidan take shekara talatin da huɗu duk wanda ya zo da maganar aure da kansa yake gudu. Ita da duka sauran ƴan matan gidan su huɗu da samari biyu babu uwayensu mata biyu da yake aure kafin zuwan Mami sun fita ta ƙarfin tsiya. Ƴaƴan Mami a gidan huɗu ne. Salwa da ƙannenta maza biyu.

"Bushra ki ce da Mami wai na kira ban sameta ba. Kowa ya fita daga gidan zan turo mai feshin maganin sauro. Ke kuma ki zauna ki jirani. Idan akwai aikin yi ko share share bayan an gama sai ki yi."

Saƙon nasa ta faɗawa Mamin da umarninsa na ta zauna tayi aiki. Mami ta saki murmushi. Yadda ta farraƙa shi da ƴaƴan yana burgeta. Gashi yau ko tishin tauna layar bata yi ba amma ya aikata da kansa. Salwa ta kira su ka fita. Samarin dama basa nan. Ita kuma Bushra ta sanar da ƴan uwanta duk su ka tafi maƙota. Ba a jima ba Alh. Mukhtar ya dawo.

"FaÉ—a min gaskiya Bushra, Mami tana da kayan asiri a gidan nan?"

Rawa jikinta ya fara. Idanunta su ka ƙara girma don tsoro da firgici.

A ƙagauce ya ce "Ba mu da lokaci. Ki faɗa min idan akwai."

Kai ta gyaÉ—a. Ya ce idan ta san inda su ke maza ta nuna masa.

"Ban sani ba. Sai dai mu duba."

Babbar rigarsa ya ajiye a kan kujera ya ce ta saki jiki su yi aiki da sauri. Ai kuwa yaga zafin nama. Duk gidan sun gaji da rayuwar da Mami ta ƙaƙaba musu.
Chapter 66 · 0% Book details