← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 96

Sashe 38

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ƴan uwana..." ta nuna su Hajiya "daga gida ina roƙon ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaɗai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da ɗana kunya."

"Ɗanki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?" Alhaji ya ma kasa yi mata faɗa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba.

"Ɗana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daɗin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya laƙaba min suna Inna tun da sauran ƙuruciyata." ta faɗi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ƙwalla "a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne haƙƙinsa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata aƙida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba."

Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faÉ—a masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta.

"Zainab."

Dakatawa tayi ta juyo su ka haÉ—a ido da Alhaji.

"Ban yi miki izinin fita yin duka buƙatun da ki ka nema ba. Haka ma ku" ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaɗin wannan abu.

Inna ta goge hawayenta ta kalle shi.

"Samun izinin shi ne kaɗai abin da zai sa na yafe maka rabani da ɗana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saɓawa ba."

Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta É—an jinkirta tashi kallonsa tayi.

"Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito ɗin yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ƙofa ta buɗe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to."

"Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?" Ya faÉ—i da gaske.

Hajiya tayi dariya "ai na faɗa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai ɗaukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A'i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su ɗauko Taj daga wajen Jamila taƙi. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daɗi bace."

Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ƙarfinsa. Abu ɗaya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta ɓalle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota.
RAYUWA DA GIƁI 18

Batul Mamman💖

***

Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs.

"Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha.

Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so É—orawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj."

Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi "kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida."

Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba.

Ya Hajiyayye tana shan zoɓo ta ce "Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Baƙon gidanku ya yi aure yau."

Kallon neman ba'asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa.

"Taj aka É—aurawa aure bayan sallar juma'a."

Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faÉ—i. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba.

Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje.

"Me ya sami Salwa?" Wajen mutum uku su ka tambaya a tare.

Zahra sai ta faÉ—i abin da ya fara zuwa bakinta "ai kuwa samosa ta bari akan wuta."

Da sauri tabi bayanta har ɗaki. Da shigar Salwan ta banko ƙofar da sauri ta murɗa muƙulli. Kan gado ta faɗa ta riƙe ƙirji. Kukan da take tunanin yi yaƙi zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ƙirji.

"Ana wata ga wata" Zahra ta faÉ—i tana juyawa.

Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ƙofar.

"Don Allah ka barta taji da abu É—aya."

"Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?"

Bayansa ta kalla "Rage muryarka don Allah kada a ji."

Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faÉ—a.
"Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faÉ—a mata da wuya Alhaji ya yarda É—ansa ya auri Æ´ar Mami."

Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ƙarawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haɗin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faɗa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki.

Ƙanana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka ɓata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ƴan uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. Ƴarsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaɓin mijin ne idan ta gama.

Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige ɗakinsa ya kwanta. Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ƙudurce a ransa ba zai ɗauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haɗu kawai ayi ta ido da ido.

Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.

"Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ƙwan. Har mun fara shirin biki." Umma ta faɗi tana dariya.

Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah."

Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.

"Bishir kai zan bawa aikin buÉ—e mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waÉ—anda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?"

Murmushi ya yi akan maganarta taƙarshe
"Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buÉ—e kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faÉ—i ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta.

"A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arziƙin Taj ba tun baya gari. Mu da ƴaƴanmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuɗin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwaƙa kawai."

Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaɗai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faɗin me zai kawo daidai ƙarfi.

Wasu don zumuɗi tun kafin a tashi su ka fara faɗin nasu. Haɗin kansu gwanin ban sha'awa. Ɗakin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ƙullewar zumunci tsakanin matan gida da ƴaƴa shi ne mafi girman arziƙin Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ƙarfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.

***

Yawan mutane Æ´an Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa É—azu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya É—aya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka Æ´aÆ´ansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.
Chapter 38 · 0% Book details