Sashe 84
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna tsokamarsa wai bashi da kunya da ya faÉ—i haka a gaban iyaye ya ce su ma basu da ita da su ka kawo zancen ya sake kwana. Aka gama wasa da dariya su ka fito. A hanya ya fara faÉ—awa Ahmad damuwarsa akan Kamal.
"Gabana har faÉ—uwa yake yi idan ya faÉ—o min a rai. Gani nake kamar ba wani ciwon allery."
Ahmad yayi ta maza sosai da ya iya daurewa ya cije yadda Taj ba zai gane ba.
"Ka tambaye shi?"
"Ina É—auko maganar yake neman hanyar canjata."
"Kada ka sa komai a ranka. Zan binciko maka."
Ajiyar zuciya Taj yayi "nagode Yaya."
Shiru su ka É—anyi kafin Ahmad ya É—auko zancen Salwa.
"Naji duk abin da tayi. Kayi haƙuri. Yau na so ta koma Bauchi amma ban sami zama ba."
Katse shi yayi "Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen. Ƙanwarka ce. Nima kuma ƙaninka ne. Na san babu sani ko goyon bayanka saboda haka kada ka ja zancen nan ko ka bani haƙuri. Ita ce ma zan bawa saboda ƙin karɓar tayinta da nayi."
Samun gidan yawa irin na Alh. Hayatu mai tattare da haɗin kan iyali ba abu ne mai wahala ba. Na farko mutum ya zaɓo mata nagari sannan ya tafiyar da mu'amalar gidansa a bisa tsarin shari'ar musulunci. Na ƙarshe kuma ya dage da addua. Saɓani a yau da kullum dole ne. Amma a ƙalla wasu abubuwan da dama sai dai kaji ana faɗi ba dai a gidanka ba.
A farfajiyar gidan su ka haÉ—u da sauran Æ´an uwansu da tsiraran abokai. Sai Safwan da Baballe. Ahmad ya ce ba zai shiga ba a matsayinsa na wan ango. Su Kamal ne su ka raka shi ciki.
"Ya Taj ina ledar kazar amarya? Ko tana mota?"
Abba ne ya yi tambayar kafin su bar bakin motocin. Taj ya tsaya turus, wallahi ya manta ana wannan siyayyar. Bai taɓa raka ango ba amma Kamal ya faɗa masa.
"Subhanallahi...zo ka siyo min." Ya zira hannu a aljihu.
"Gashi na siyo" Kamal ya É—ago ledoji biyu daga gaban motarsa.
Rungume shi Taj yaje ya yi.
"What will I ever do without you?"
"Sake ni dalla kada ka sani kuka" Kamal ya ture shi. Taj yaƙi saki. Bishir da wani cousin ɗinsu harda ƴar ƙwalla.
"Ya aka yi ka san ban saya ba?"
"Wallahi jiki na ne kawai ya bani."
Murmushi suka yi sannan Taj ma ya karanto addu'a kafin ya shiga gidansa karo na farko a matsayin mijin aure.
A falo su ka sami ƴan matan amarya da amaryarsu a tsakiya an lulluɓeta da laffayar jikinta. Tana ji ana gaishe gaishe an barta da faɗuwar gaba. Ta kama hannun Sajida tayi masa kyakkyawan riƙo kamar za ta tsinke mata shi.
Addu'a da fatan alkhairi aka yi musu a mutumce. Babu wannan rashin kunyar rungume rungumen sabbin aure da ake a gaban mutane. Ko kuma maganganu na rashin É—a'a tsakanin angwaye da amare. Da aka gama Safwan ya ce ya kamata su tashi haka nan. WaÉ—anda za a kai gida su fito a kai su.
"Ni dai ina da abin cewa guda É—aya kacal. Happy..." Taj ya kalli Kamal.
"Mrs Happy..." Hamdi ma ta É—aga kai a hankali amma bata buÉ—e fuska ba.
"Duk abin da za ku yi, ku ji tsoron Allah. Ku yiwa juna uzuri kuma ku kyautatawa juna zato."
Yanzu dai bata yi kuka sosai ba da zasu tafi sai hawaye. Taj ya fita ya raka su sannan ya rufo ƙofa ya dawo.
Hamdi tana nan bata motsa ba. Ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Gabanta ya kama dukan tara tara. Yau da anyi an gama. Inda take yanzu gidansu ne ita da Taj. Magana take jira ya yi ko wani motsi duk taji shiru. Ba zato taji saukar abu a gefenta. Ta ɗaga kai da sauri, kafin ta buɗe fuskar Taj yasa hannu ya haɗe gaban laffar ta saitin fuskarta.
"Ni zan buɗe. Kada ki ɓata min tafiyar tarihin wannan daren."
Komawa tayi jiki babu kuzari ta zauna da ta gane babbar rigarsa ce ya ajiye a kusa da ita.
Rage tsayi yayi a gabanta ya ce "Zan taɓaki Hamdi. Kin bani dama?"
"Na'am?" Hamdi taji wata baƙuwar murya ta fito daga bakinta ma'abociyar tsoro.
"Na fahimci a tsorace kike ne shi yasa na faÉ—a miki."
Kafin ta sake yin magana taji hannuwansa a duka kafaɗunta ya tayar da ita. Sannan ya kama laffayar ya soma warwareta har ta ƙare. Ya kalleta daga sama har ƙasa ya godewa Allah a ransa.
Babu zato daga gareta kawai taji ya janyota jikinsa ya sanya hannuwanta a gefe da gefen cikinsa sannan ya rungumeta. Sun ɗauki lokaci a haka kowa yana fama da yanayin da ya shiga kafin ya ɗago haɓarta yana kallon idanunta.
"Mun shirya Hamdi? Kin daina fushin?"
"Ba fushi nake ba."
"Har akan maganar É—azu?"
"ÆŠazu gaskiyata na faÉ—a maka ai" ta É—an kawar da kai.
"Kina nufin yau ni da gwaurayen da su ka fita daga gidan nan bamu da bambanci?"
So tayi ta haÉ—e fuska don ya san mahimmancin abin da ta faÉ—a amma wannan maganar sai da tasa ta yin murmushi.
Sannan ta ce "Haka ne."
Hannunta ya riƙe su ka zauna "su rungumi pillow nima na runguma kenan fa?"
"Uhmm" ta amsa kunya na kamata.
Taj ya kalleta da kyau ya ɓata rai "ke Allah kuwa da sake. Sadaki fa na biya."
Da dabara ta É—ora hannu a kan bakinta don kada yaga dariyar da take neman yi.
"Aka biya maka dai." maganar ta fito kamar ba daga bakinta ba.
Ƙayataccen murmushi ya yi "Lallai, kin ce wani abu. Zan tuna miki a lokacin da baki zato." Ledojin da Kamal ya ajiye akan centre table ya buɗe "zo mu ci abinci. Kuma kada ki ce kin ƙoshi."
"Ƙoshi kuma? Yunwa fa nake ji."
Ƙasa ta zamo abinta ta zauna. Taj ya shagala da kallonta ta nuna masa ledojin da ido.
"Ba za ki taimaka min ba?"
"Amarya nake. Yau É—aya ina zaune kayi min komai."
"Burina ma kullum na taimaka miki." Ya wuce kitchen ya samo tray da kofuna.
Tana zaune ya buÉ—e ledojin ya ajiye tray É—in a tsakiyarsu. Akwai youghurt da juice, sai snacks irin su doughnut, croissant da pizza. Ga kwali madaidaici a ciki akwai cake da aka rubuta beautiful beginning Happy and Mrs Happy.
"Allah Sarki Happiness mai sona da gaskiya." Taj ya yi magana yana kallon Hamdi a kaikaice.
Ta gane da biyu yayi magana shi yasa ta ce "Wallahi kuwa, Allah dai ya ƙaro aminci."
Taj ya yi ƙwafa kawai ya buɗe ledar gasashshiyar kaza da gurasa.
"Wanne za ki ci?"
"Mene ne wannan?" Ta nuna croissant É—in.
"Abincin maza ne." Ya tsokaneta.
Yana rufe baki ta É—auka ta gutsira harda lumshe ido ta ce da daÉ—i.
"Na ce miki na maza ne."
"Nima ai ta mazan ce"
Hamdi is just too cute. Yadda take maganar kaÉ—ai ya gama hargitsa masa tunani.
"Har mu nawa?"
"Ga Abbana, ga Halifa sannan..."
Ya zuba mata idanu. Dole taji kunya ta saki murmushi.
"Sannan kuma ga Happy nawa."
"Happy naki." Ya maimaita da murmushin jindaÉ—in. Ture tray É—in ya yi ya dawo kusa da ita kamar zai mayar da ita jikinsa ya ce "saboda Allah da gaske kike to akan maganar nan?"
"Da gaske nake."
"Amma in banda ke wa yake kama wani da laifin da ba nasa ba?" Ya marairaice mata.
Yadda komai tayi yake taɓa masa zuciya bai san ita ma haka yake a wajenta ba.
Haɓarta ta ɗora akan tafin hannunta ɗaya tana kallonsa ta ce "Yanzu ya kake so ayi?"
Kalmomi neman ɓace masa suka yi saboda har cikin zuciyarsa yake jinta.
"Stop acting all coy..."
"Meye coy?" Tambayar ma a yangance tayi ta.
Ba kuma wani abu bane yasa take yi masa haka sai don kada ya É—auki zafi akan shawarar da ta yankewa zamansu. Soyayyarsa tana jinta kamar da ita ta rayu. Æata masa rai is the last thing on her mind. To amma me zai faru idan zama yayi zama sai kawai Alhaji ya yiwa Abbanta abin da zata ji haÆ™urinta ya Æ™are? Idan wataran ta kasa riÆ™e bakinta ta rama fa? Da wane ido za su kalli juna ita da Taj?
"Acting all lovey dovey,.. and shy...and bold, and...."
"This?" Hamdi ta saƙala hannuwanta a wuyansa.
Gabaɗaya su ka tafi. Sai da ya kaita kan kafet ɗin. Fuskokinsu na kallon juna. Numfashinsu na gauraya sannan zuƙatansu na bugawa lokaci guda.
"Hamdiyya"
"Taaajjj" sunansa ya fito da wani irin shauƙi kwatankwacin yadda ya kirata.
"Duk abin da za ki yi, ki ji tsoron Allah kada ki É—auki alhakina."
Murmushi mai kama da dariya tayi "Ba zan É—auka ba."
Tausayi ya bata ta danno wuyansa ya ƙara yin ƙasa. Ta ɗago kanta a hankali su ka haɗu. Bata sani ba ko don yau a gidansu suke babu fargabar da yake barinta da ita ta tunanin wani zai gansu. Sakin jiki tayi ta bari yana kissing ɗinta kamar ranar ya fara. Sai da zancen ya fara fin ƙarfinta ta shiga neman ƙwatar kanta.
"Yunwa...yunwa nake ji Allah."
Ƙarfin hali ya yi ya sake turo mata tray ɗin da su ka ture da ƙafa. Kallon duk motsinta yake yi ta rufe ido.
"Ni gaskiya kunyarka nake ji. Ka daina kallona."
"Ji min gulma. Ki gama tumurmu..."
Hannu tasa ta toshe masa baki "ba ni bace."
Taj ya kama dariya "haka ne. Mrs Happy ce."
Ƙin kallonsa tayi. Saboda kunyar da ta rufar mata bata san ta loda abinci da yawa a gabanta ba.
"Ni fa ba ci zanyi ba." Ya yi maganar yana bin gefen kunnenta da wuya da bakinsa.
"Nima na ƙoshi." Ta matsar da tray ɗin. Abin da yake mata ya toshe duka senses ɗinta.
"Cikinki duk ya cushe ko? Tashi kawai muje mu kwanta." Ya tayar da ita jikinsa.
Harararsa tayi tana magana da shagwaɓa "Amma dai a tarihin angwaye kai ne ka fara hana matarka cin abinci ranar da aka kawota. Duk labarin da nake ji tura musu abinci ake yi ko basa so."
"Cewa za ki yi duk na fi sauran son matata. Ba zan takuraki ba but I promise you komai dare ki ka ji yunwa ki tada ni. Zan kawo miki abinci."