Sashe 71
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To nima dai idan bata fito ba tabbas babu inda zani tunda amaryar tayi rantsuwar ba za ta fito ba."
"Barni da ita. Yanzu zan kira in yi mata faɗa." Cewar Abba yana ƙara kaurara murya don ya ƙara mata kwarjini.
Taj ya ce "Abba me ɓoyon zai ƙara ko ya rage? Waye bai san ƴarka nake aure ba? Wa kuma kuke son ɓoyewa kanku? Kuna jin gata ne kuke yi musu? Mushirikai da fasiƙan iyaye ake gudun nunawa. Amma idan kuna yin haka nan gaba sai sun fi ku jin kunyar a ganku tare. Kunga sai ayi ta rubuta musu zunubin rashin kyautatawa iyaye."
"Kai Tajo, me yayi zafi?" Inna Luba ta ce a tsorace "ke tashi ki shirya ku tafi."
"Ke fa Inna?" Taj ya É—aga mata gira "nawa kakannin babu. Ki zo ki wakilci kowa."
"Ja'iri, to bari nasa kaya. Dama wannan ƴar ce ta hana ni zuwa amma na so bin su wallahi" ta miƙe da murnarta.
Murmushi Abba ya yi. Yaya da Inna Luba su ka shiga ɗaki. Basu daɗe ba kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Yaya lace ɗin da Mama ta aiko ta ce mata ankon manya ne ta saka. Kai kana ganinta banda lalurar ƙafa da ba ƙaramar mace za ayi ba. Fuska dai kam Masha Allah. Akwai kyau irin na Katsinawa wanda ƴaƴanta su ka haɗa da na Simagade su ka fito gwanin ban sha'awa.
***
Ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyar daidai Amma ta kira Taj ya ce mata suna wajen parking.
"Bari a sauko da amaryar sai ku shigo."
"Amma tare muke da Yaya."
"Tun ɗazu nake lalubenta cikin baƙi. Gani nan fitowa."
Da kanta taje wajen motar ta riƙo Yaya su ka shigo. Mama na hangota daga wajen zaman iyaye ta tada Umma su ka ƙarasa. Hajiya ma ta ce da Inna lallai ta tashi. Tunda aka ce Taj ne ya kawota ta san tana tattare da jin nauyin shiga jama'a ne. Mutane sun fara kallon Yaya ana ƙusƙus da faɗin uwar amarya ce sai aka ga matan Alh. Hayatu Sule masu aji sun je inda take suna yi mata maraba. Kayansu ita da matan da Amma iri ɗaya. Sannan su duka har ƙasa su ka gaishe da Inna Luba. Wannan abu yasa duk mai abin faɗa ta haɗiye kayanta. Dukkan alamu sun nuna su ɗin suna cikin farinciki da son juna. Gutsiri tsomar ƴan gayya bata da tasiri.
A ɓangaren amarya kuma ƴaƴan Amma wato Ihsan da Amira da kuma Anisa sun haɗu da masu ƙananun shekaru cikin ƴan gidansu Taj da Anti Zahra sai kuma Sajida da Zee wajen rako amarya. Gabaɗaya matan doguwar riga su ka saka ta wani yadi sky blue da ɗigon fari da pale yellow wadda aka yiwa wani irin ɗinkin bubu mai kyau. Umarnin Hajiya Gambo kenan. Duk wata jininsu da tayi ɗinki mai fitar da shape a gida zata ci bikinta. Babu head sai rolling da su ka yi da pale yellow ɗin yadi mai santsi. Babu yadda za ayi ka gansu basu burgeka ba. Modesty and elegance at its peak!
Amarya Hamdiyya kuwa gown ɗinta fara mai dogon hannu kuma wadatacciya. Bata bi jikinta ta tona sirrin wanda ya bada sadaki a gaban kowa da kowa ba. A kanta anyi mata ɗauri da net silver wanda aka ɗorawa wani abin ado mai duwatsu sky blue na gashi ya kwanta ta ɓari ɗaya. Daga tsakiyar ɗaurin inda gashinta yake a suturce aka ɗora farin net dogo har ƙasa. Wuyanta sarƙar farin gwal ce. Sai clutch bag ɗinta da takalmi mai tsini sky blue. Tayi kyau har ta gaji.
Ƙasa suka sauko sannan aka zo bakin ƙofa aka jera yadda za a shigo. Kallo ɗaya Anisa ta yiwa Hamdi tunda sai yau su ka iso ta ganeta.
"Mai kukan uber?" Ta faÉ—a ba tare da wani tunani ba.
Hamdi ta ɗago su ka haɗa ido. Ta saki murmushi mai ban sha'awa. Haka kawai sai Anisa taji ƙuncin zuciyarta ya kau. Ta matsa kusa da ita tayi musu selfie sannan aka ce su tsaya kamar yadda aka tsara musu.
Matan layi layi suka yi hagu da dama har layi shida. Sai Hamdi a tsaye. A bayanta kuma Bishir da Abba. Sai kuma Kamal da Ahmad a bayansu. Sanye su ke da yadi pale yellow da aka yiwa ɗinki ma hannu da ya wuce gwiwar hannu da kaɗan. Daga hula har zuwa takalmi komai nasu iri ɗaya in banda agogo. Hamdi tayi zaton tafiya za su fara yi don hankalinta a tashe yake tun a nan ga hasken flash ana ta ɗaukar hoto. Ƙofar hall ɗin aka buɗe ta soma jin sanyi da ƙamshin wajen na buso ta sai ji tayi hannuwa sun kama nata da gentle riƙo. Tsigar jikinta tashi tayi da tsoro da kuma gane hannun waye. Tsayuwarsa kaɗai a kusa da ita ta sanya sanyin nan ya ragu don kansa. Ta ɗaga kai su ka haɗa ido.
Kayan jikinsa sky blue ne harda babbar riga irin wadda ake yi ta zamani ba burum-burum ɗinnan ba. Shi ma hannun rigarsa ta ciki ƙarami ne kamar na ƴan uwansa. Ya sanya hula da takalmi cover shoe navy blue mai duhu sosai. Gashin baki da gemunsa da basu cika yawa ba sun sha gyara.
"Ya Rabbi, har na fara tsoron ko ni kaÉ—ai zan shiga" Hamdi ta faÉ—i a hankali tana kawar da kai don kallon nasa babu rissina a ciki.
"Ina tare dake kowanne taku. Ki daina jin tsoro." Ya bata amsa a kunnenta.
Hannunta zai saki yaji ta kuma damƙe nasa.
"Don Allah ka riƙeni har mu zauna. Zan iya faɗuwa da takalmin nan." Ta marairaice masa idanu har lokacin tana magana a hankali don kada na gabansu ko baya su ji.
"Awwwnnnn, zuciyata" Taj ya dafe ƙirji kuma da gaske yadda tayi ɗin ya shige shi ne sosai.
Fari tayi da ido tana harararsa "A nan É—in ma sai kayi?"
"Kin gama dani ne Mrs Ha..."
Wani abu su ka ji kamar harbin bindiga da ya katse masa magana. Sai kuma muryar MC yana sanar da shigowar ango da amarya da umarnin kada kowa ya bar wurin zamansa da sunan ɗaukar hoto. Wani irin kiɗan taushi ne yake tashi babu waƙa a yayinda suke shigowa wajen cikin nutsuwa. Matan dake gaba basu mai rawa sai ɗan kwanon hannunsu mai fulawoyi masu kyau da su ke ta watsawa sama.
Da su ka iso gaba Yaya ta ƙyallara idanu ta hango ƴan matanta, bata san lokacin da idanunta su ka tara ƙwalla ba. Ta dinga hamdala a zuciyarta. Ashe Inna Luba ma hakan take a wajenta. Sai dai ita bata iya ɓoye nata hawayen ba. Jikokin kenan sai Halifa cikon na huɗu. Sai kuwa na yayarta abar alfaharinta har kullum. Amma dai jininta da take da cikakken iko dasu waɗannan ne. Da kanta ta dinga bin ƴan uwan Yaya wato ƴqƴan abokiyar zamanta mazansu da matansu a samu mai zuwa bikin nan amma yadda su ka ƙi zuwa na Sajida wannan ma ƙi su ka yi. Ta roƙi maigidanta ko sau ɗaya ne ya yi musu magana ko ya zo ƴarsa taji daɗi ya ce ba zai taɓa murna don ƴaƴan ɗan daudu sun yi aure ba. Su je can su ƙarata. Godiya kawai take ga Allah domin bai haɗa mata zuri'a da lalatattun mutane ba. Dukiyar bata tsole mata ido ba. Girmamawar daga surukan ƴaƴan shi ne komai a wajenta.
A teburin gefensu Iyaa ce da su Ummi, sai kuma surukar Sajida da ƙannen Safwan. Shi da Baballe suna can ɓangaren maza.
Amarya da ango sun sami waje sun zauna sannan Æ´an rakiyar su ka koma nasu waje. Aka shiga cikin taro ka'in da na'in.
An fara da addu'a daga bakin babbar baƙuwa Malama Maimuna. Bayan ta gama aka ce ta faɗi kalmomi biyu zuwa uku na shawara ga ango da amarya.
"Tajuddin da Hamdiyya. Abu É—aya zan faÉ—a muku. Duk abin da za ku yi ku tuna cewa kowa cikinku mai kiwo ne kuma abin tambaya akan kiwon da Allah Ya bashi. Duk wanda ya tozarta amanar Allah sai Ya tanadi amsar bayarwa."
MC ya karɓi mike ya ce "wannan fa damu duka take. In kin san satar fita kika yi ki ka zo nan babu ruwanmu. Kai kuma mai shirin samun sabuwar budurwa a nan domin ka ci zarafin ta gida ta hanyar kwaye mata baya kana tona mata asiri to kai ma dai ahir ɗinka."
Dariya aka yi sannan ya ce ina Hajiya Amina aminiyar Inna. Tasowa tayi ita ma ya buƙaci kalmar shawararta.
"Kada ku yarda soyayya ta sanyaku saɓawa Mahalicci. A komai na rayuwa ba a yiwa umarnin da ya saɓawa Allah biyayya ga kowa."
Godiya aka yi musu sannan MC ya É—ora. Agendarsu ta gaba ita ce gasar da aka shiryawa team É—in ango da amarya. Tambayoyi ne da za su amsa game da juna. Aka sanya kujeru biyu suna kallon juna su ka zauna. A team É—in ango akwai Sajida, Zee da Halifa.
Team ɗin amarya kuma Yaya Hajiyayye da ta ce ta fi kowa sanin duka ƙannenta, Kamal da Ihsan ɗin Amma.
"Ba zan tambayeku birthday É—in juna ba."
Ya raba musu takardu guda goma. Kowa a takardarsa zai rubuta amsa da taimakon team members É—insa. Wanda ya yi na É—aya zai sa wanda ya faÉ—i yin duk abin da yake so.
Ƴan biki aka kasa zaune aka kasa tsaye da ganin wannan sabon salon. Kowa ya zata rawa za a sha yadda aka saba ana liƙi a gaban DJ.
MC ya ce "a rubuta min cikakken kwanan watan ranar da ku ka fara haÉ—uwa a cikin sakan talatin."
(12/08/2021)
Kusan tare su ka É—aga takardunsu kafin lokaci ya cika.
Kemara ta É—auka aka haska a manya manyan talabijin dake manne a jikin bangon hall É—in ta kowacce kusurwa.
Daga nan ya dinga yi musu tambayoyi akan juna. Kamal, Yaya Hajiyayye da Ihsan da ta rayu da Taj kafin tayi aure a US sun taimakawa Hamdi sosai. Kazalika su Sajida. Aka gama tambayoyi suna kunnen doki.
"Dole a sami na É—aya da na biyu fa. Team members ku koma ku zauna a barsu su kara su kaÉ—ai."
"Banda ke Hamdiyya, wa Taj yafi so? Kai ma banda kai wa tafi so?"