← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 96

Sashe 22

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda ya yi maganar a tausashe ta ƙarasa ɗaki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faɗuwar gaba. Shin magana ya yaɓa mata ko kuwa ya sauko ne?

Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira da Ahmad. Daga kitchen ta leƙo bayan ta tura tana kallonsa ya duba saƙon, ya kuma rubuta reply. Da wani irin sauri ta koma ciki ta buɗe. Nata ta fara bi inda ta rubuta masa saƙo kamar haka.

(Ya Taj nagode kuma ina mai sake baka haƙuri. If I am forgiven please give me a chance to be your friend.)

Shi kuma ya rubuta wannan amsar.

(Kada ki matsawa kan ki da son neman wani relationship dani bayan already akwai. Ƙanwar Yaya Ahmad ƙanwar Taj ce.)

Ranar da ƙyar ta gama girki. Saƙon dake cikin amsarsa ya fito ɓaro ɓaro. A matsayin ƙanwa kaɗai ya ɗauketa. Daga yau za ta gwada cire shi daga zuciyarta. Sai dai abin da wuya domin son bai yi shawara da ita ba ya yi mata kamun kazar kuku.

***

FaÉ—a Yaya take kamar ta ari baki a waya. Sajida da Zee su ka matsu ta gama ta basu labarin me ya faru. Sun dai fahimci Hamdi ce tayi wani laifin. Ita kuma Anti Labiba da su ke wayar banda dariya babu abin da take yi.

"Abin dariya ki ka ɗauki abinnan Labiba? Wace ƴar arziƙin ce za ta guji girki kamar ba mace ba?"

"Yaya ki barni da ita don Allah. Na faɗa miki ne fa kawai saboda kada ku ji shiru bata dawo ba. Zan ɗan riƙeta ne in sauke mata gammon da ta ɗauka." Cewar Labiban tana murmushi.

Yaya ta gyara zama tana hararar masu matsowa jikinta don son jin me ake cewa "amma fa samun wuri ne. Bata taɓa gwada min wannan shegantakar a nan ba. Iyaka dai in tana gida girki ya faɗo kanta tayi ta cika tana batsewa kenan. Ita a dole bata son sana'ar uban da yake wahaltawa rayuwarta."

Haƙuri Anti Labiba ta bata "ki barni da ita kawai Yaya. Girki kuma tunda ta iya ai magana ta ƙare."

A haka su ka yi sallama bayan ta sake roƙon alfarmar kada Yaya ta yiwa Hamdi magana idan sun yi waya. Ƙarfe uku bayan yaranta biyu sun tafi islamiyya ya rage jaririyar da take goyo da yayarta mai shekara biyu da rabi. Ta fito abinta cikin shiri ta sami Hamdi a falo tana kallo.

"Hamdi zan fita amma ba jimawa zan yi sosai ba. Ga kaza can na fito da ita ki yi pepper chicken kafin na dawo. Sai ki haÉ—a coleslaw. Na riga na dafa jallof É—in shinkafa."

Jin abin da ta ce ba shiri ta kashe TV É—in.
"Anti ni zan girka?"

"Kina nufin zancen da mu ka yi jiya da gaske ki ke?" Anti Labiba ta ƙanƙance idanu.

"Anti wallahi ni..."

"In fasa fitar kenan komai mahimmancinta in ƙarasa girki ko?"

"A'a Anti. Amma naga tattali ma yana da kyau. Tunda anci kifi da rana a bar kazar sai gobe."

Ƙiris ya rage Anti Labiba ta fashe da dariya. Fuskar Hamdi na nuni da cewa da gaske take. Lallai idan ta biye mata ba za ta sami biyan buƙata ba.

"Abbansu ne ya aikeni. Gashi kuma yana hanya tare da abokinsa. Na zata ke me fitar dani kunya ce..." ta sauke mayafinta "nagode da ki ka nuna min ban isa ba."

Jikin Hamdi rawa ya fara. Bata son ayi fushi da ita ko kaɗan. Musamman mai kyautata mata. Da sauri ta bar falon ko kallon Antin ta ta bata kuma yi ba ta shige kitchen. Anti Labiba ta ƙunshe dariyarta ta fice.

Bata zame ko ina ba sai bayan National Military Cemetary da an ɗan wuce National Stadium a nan cikin umguwarsu Karon majigi. Wurin aminiyarta Hauwa taje don nan ne take da tabbacin za ta juyawa jin kunya baya. Daga bakin ƙofa su ka rungume juna saboda sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba.

"Sannu da zumunci Labiba. Ina ta waƙar sake zuwa ganin baby amma kwanakin nan orders suna neman fin ƙarfina." Cewar Hauwa tana karɓar goyon Anti Labiba.

"Mu ai haka muke so. ÆŠan kasuwa baya kiran yawa. Ki dai ce kasuwa tayi albarka ki kuma godewa Allah."

"Alhamdulillah ala kulli hal."

Hira su ka ɗan taɓa sannan Labiba ta faɗi abin da ya kawota.

"Ni kuwa kina É—aukar É—alibai ki koyar dasu?"

"Ban fara ba amma na gama duka shirye shiryen da ya dace. Nan da Æ´an kwanaki za ki ji sanarwa."

Anti Labiba ta saki jiki "Masha Allah. Nayi sara akan gaɓa. Dama ƙanwata nake son kawo miki. So nake ta goge sosai a harkar snacks ɗin nan ita ma."

Hauwa ta ce "akan ƙanwarki ki ke tambayar class dama? Ai kin san ko bana yi dole na koya mata."

"Allah Ya ƙaro kasuwa. Nagode sosai."

"Babu komai. Ai yiwa kai ne."

Hirarsu su ka cigaba da yi inda Labiba take ta koÉ—a daÉ—in kayan ciye ciyen da Hauwa ta ajiye mata. Da za ta tafi ta sayi frozen samosa.

*

Da yake babu wani abu da zai ɗauke mata hankali, bata wani jima ba ta gama ta gyare kitchen ɗin. Tana jin an taɓa ƙofa kuwa ta soma murmushin neman shiri. Ita kuma Anti Labiba sai da ta zo bakin ƙofa ta daina fara'a. Fuska a cinkishe ta shiga gida.

Hamdi ta shiga damuwa. A irin miskilancinta ɗaki za ta tafi amma ita shaida ce. Ganin ɓacin ran Anti Labiba na nufin anyi mata abin da ya ɓata mata rai sosai.

"Anti zo ki gani. Na gama."

"To an gode." Ta bata amsa ko kallonta bata yi ba.

Fuskarta canjawa tayi kamar tayi kuka ta ce "Allah na daina Anti. Ki yi haƙuri."

Ledar pack É—in samosan ta bata ta ce ta soya. Wannan karon ko kaÉ—an bata nuna komai na rashin jindaÉ—i a fuskarta ba. Da ta gama Anti Labiba ta ce ta ci ta faÉ—a mata ko da daÉ—i.

Tunda ta gutsira ta kama murmushi.

"Yayi miki?"

"Da daÉ—i sosai."

Sai lokacin Anti Labiba ta saki fuska ita ma tayi murmushi.

"So nake ki koma gida da sana'ar hannu. In sha Allah nan da kwana huÉ—u za ki fara zuwa wurin Hauwa koyon waÉ—annan abubuwan."

Farinciki sosai ta gani a tare da Hamdi. Ta dinga dariyar yadda ta canja lokaci guda.

A zahiri tana yiwa ƙannen nata uzuri idan su ka nuna ƙyamar wani abu na Abbansu. Maganar gaskiya duk kirkinsa akwai abin da fa dole ya tsayawa mutum a rai. Ƴaƴa yawanci babu ruwansu da talauci ko arziƙin iyayensu. Indai akwai jinƙai da kulawa a tsakaninsu za ka ga suna ƙaunar abinsu da zuciya ɗaya. Amma duk lokacin da kaga ƴaƴa na kunyar nuna iyayen a wasu wuraren, za ka samu nakasu ta wanni fannin. Inma dai daga ɓangaren ƴaƴan in aka samu marasa godiyar Allah, ko kuma daga iyayen idan sun shuka wani abin da zai kunyata yaransu.

Ga dai shekaru sun ja. Amma har yanzu kallo É—aya ya ishi mai idanu gane waye Abba Habibu. Irin haka ne abin da ake gudu. Kayi abu ka barshi amma tasirinsa ya gagara barin rayuwarka komai tsahon lokaci.

***

Kwana biyu Kamal ya ɗauke ƙafa daga gidan Ahmad. Taj ya ƙule iya ƙulewa. Kuma ya naɗe ƙafa ba ya zuwa site ɗin aikinsu. Kamal ɗin kaɗai ke zuwa ya wuni yana monitoring komai. A rana ta uku ne ya gaji da gudun rigimar da za su yi da Taj akan zuwansa gidan Abba yaje gidan Ahmad ɗin. Bari ya yi sai gabanin azahar lokacin da ya tabbatar yayan nasu yana wajen aiki sannan yaje.

Babu kowa a gidan sai Taj da Zahra dake kitchen. Fitowa tayi su ka gaisa sannan yaje ƙofar ɗakin Taj. A rufe take, ya yi sallama sannan aka buɗe.

Taj bai jira shi ba ya koma ya zauna akan gado ya cigaba da aikin da yake a laptop É—insa.

"Wai nan gaba kake dani?" Kamal ya faÉ—i da sanyin jiki.

"Kai zan tambaya da ka daina zuwa gidan nan." Taj ya mayar masa rai a ɓace.

Tausayinsa Kamal yake ji. Bayan abubuwan da yake rayuwa yana haƙuri da rashinsu, baya jin zai juri wani abu ko yaya yake ya haɗa su rigima ba. Zai fara bashi haƙuri sai aka kira Taj ɗin.

Abinka da sabonsu na rashin ɓoyewa juna komai. Gaisawa kawai su ka yi da Amma ta sako zancen Anisa. Ya kunna speaker ya yafito Kamal da hannu.

"Taj kana ji na kuwa?"

"Ina ji yanzu Amma. Me kike cewa?"

"Maganar Anisa. Kai baka ce min komai ba. Na share don ina zaton sai ka dawo za mu yi magana. To jiya Hajjo ta kira ta ce za ka wulaƙanta mata jika. Idan ba ka so ka faɗa ta samo mata wani."

Hannu Kamal ya dinga juyawa yana son sanin me take nufi.

"Amma da kin bari na dawo dai."

"Ai ka san halinta. Yanzu sai ta juya zancen. Ba ka son Anisan ne?"

Ƴar dariya ya yi daga ji bata kai zuci ba. Baya son karɓar abin da zai zame masa matsala don ko babu Hamdiyya shi bai taɓa kallonta a matsayin da ya wuce ƙanwa ba. Idan kuma ya ce baya so nan ma duk wanda ya san tarihinsa sai ya zage shi.

"Wa zai ƙi mace kamarta?"

"Wannan wace irin amsa ce?"
Chapter 22 · 0% Book details