Sashe 81
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. ÆŠakin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al'amari.
"Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?"
"Gabaɗaya ta ɓata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa."
Umma kallon Mama tayi da mamaki "kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ƴan biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ƙofar gida."
Hajiya ta murmusa "ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta É—aure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai."
"Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar." Cewar Mama.
Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaÉ—uwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa.
*
"Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?"
Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ƙafar wanda ya ji yanzu ba. Ƙodar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal ɗin.
"Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi."
"Haka su ka yi min bayani da likitan."
"Anya ba ya faÉ—a bane kawai saboda baya son takura kowa?" Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba.
Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin ɗinsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ƙarshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo yaƙi yarda a cire ƙodar kowa a dasa masa.
Wannan tunanin kaÉ—ai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haÉ—a shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost.
Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa'a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ƙasar. Ɗan lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking ɗin asibitoci a ƙasashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ƙodar ake buƙata dole kuma babu mai bayarwa.
Da su ka gama ne Ahmad ya ce "maganar Salwa..."
"Yauwa..." ya tashi "mu je ƙasan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ƙofa."
Gaban Ahmad faÉ—uwa ya yi "Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faÉ—a. Ko a hanyarmu..."
"Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta É—auka to lallai za ta fuskanci fushina."
Hankalinsa ƙara tashi ya yi. Me kuma tayi?
Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa'a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na'ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida.
"Da kun koma kun ɗaukota kuwa" cewar Alhaji yana shafa kan ƙananun jikokinsa "ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida."
"Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada haƙuri" in ji Umma.
Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta durƙusa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin.
"Ni dai ba zan bar magana a cikina ba." Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta "da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin."
Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa "Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara'ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na'am É—innan da auren hands down."
Hararar ƙanwar tasa ya yi ya ce "A'a hands up."
Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ƙwai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ƙara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba.
"Kin ga matar Taj ko?"
Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini.
"Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?"
"Eh" ta gyaÉ—a kai da sauri.
"Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?"
Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba.
"To kada na ji, kada na gani Salwa." Ya juya mata baya "ki je Ahmad ya mayar dake gida."
*
"Yarinyar nan ya nuna min" ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ƙin amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko.
"Wace yarinya?"
Ciki-ciki ta ce "matar Ya Taj."
"You are the least of my problems Salwa so ko ki buɗe baki ki bani amsa ko ki riƙe abinki duk ke ta shafa." Ahmad ya faɗi da faɗa-faɗa.
Yadda su ka yi ta faɗa masa. Ya kalleta yana mai taɓe baki.
"Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaÉ—aya ki ka sauya akan wannan obsession É—in naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza."
Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haÉ—u yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure.
***
GIDAN TAJ DA HAMDI
(Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense)
Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta ɓangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na buƙatar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaɗan ba. Kayan zaƙi na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin Ƴar Ficika da muƙarrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba.
Iyaa kuwa gidan ƙanwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ƙwararriya a harkar kayan kaɗi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu'amala. Tun abin da ya haɗa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daɗa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuɗi da su ka bayar shi ne ta haɗo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haɗawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuɓewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haɗa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi haƙuri sai ta ɗiba saboda daɗin ƙamshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau'in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ƙuliƙuli. Niƙaƙƙiya da kuma markaɗaɗɗiyar gyaɗa (gari da paste), garin ɗanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haɗi da kuma soyayyen man shanu mai daɗin ƙamshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng)
"Altine wannan kaya basu yi yawa ba?" FaÉ—in Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu.
"Ina abin yake Jinjin?"
"Haba dai, wannan yafi ƙarfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi."
Iyaa ta ce "amin Ya Allah."
Sajida aka damƙawa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace.
Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu baƙin fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya haƙurin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ƙara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj.
Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata riƙo na ƴar da ake ji da ita.
"Wallahi babu komai. Da nan da can duk É—aya ne."
"Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?" Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta.
"Ƙwarai kuwa..." sannan Yaya ta taya su murna.
Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a ɗakin yake fitar da ƙamshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya baƙunta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita ɗin ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. Daɗin ƙamshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif.
"Ko kunnawa ba'ayi ba. Na gidan Æ´arku ne."