Sashe 35
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi.
"Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani."
"Malam lissafin kuÉ—inka fa zai canja."
Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.
"Ko akwai ciko?"
Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.
"Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan."
Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu.
"Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai?
"Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma."
*
Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda.
Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance É—a a wajen wata da su ke Æ´an maza zar da ita.
"Kawu dama..."
"Matsa na shiga" Taj ya ce da É—an saurayin.
Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.
"Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya.
Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa.
"Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faÉ—i yana kallon uban.
"Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"
Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba.
"Ka fi ƙarfin komai a rayuwata."
"Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?"
Taj ya girgiza kai "baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."
Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai.
"Rashin kunya ka zo ka yi min?"
"Ban isa ba." Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah."
"Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"
"Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki."
Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,
"Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ƙirjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?"
"Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min."
Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi.
"Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?"
"Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya..."
"Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faÉ—awa waÉ—annan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.
"Ina sonta Alhaji." Ya faÉ—a kai tsaye abinsa.
"Ita Æ´ar Habibun?"
"Eh."
"Zo ka zauna"
Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daÉ—e yana tunani kafin ya ce da Taj,
"Ka tafi gida ka jirani."
"Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.
"Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."
Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi.
*
Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi.
Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.
*
Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.
"Wace tsiyar ka ƙulla?"
"Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."
A harzuƙe Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi."
Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci.
Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.
"ÆŠanka ne ya É—auko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."
Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.
"Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a É—aura."
Godiya mara adadi Taj ya yi masa.
"Ba sai ka faÉ—awa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina."
Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko É—ar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.
***
Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin Æ´an biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.
Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.
Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara.
Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa.
"Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta."
Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..."
"Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."
"Hamdiyya."
Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faÉ—awa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An É—aura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu É—ari biyu.
A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya É—uka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.
"Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani."
Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya É—aura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar.
Allahu Akbar
Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.
RAYUWA DA GIÆI 17
Batul Mamman💖
***
"Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba."
Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.
Anti Zinatu ce kaÉ—ai ta san zaman me su ke a É—akin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaÉ—ai ke iya maganinsa.
Hamdi na jin muryarsa ta haÉ—e rai bayan fitar Yaya daga É—akin.
"Wai namiji kenan. Mtsewww."
Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki.
"Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."