Sashe 26
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko a jikin Hamdi. Burinta kawai a isa gida. Ƙafafunta sun kasa zama waje guda. Komawa gidan tayi mata nisa saboda uzurinta. Finally bayan ta gama gumi su ka shiga estate ɗin su Anti Labiba. A guje ta fita da Kamal ya tsaya. Ta sake barin takalma da wayar da dama Taj bai miƙa mata ba.
Anisa ta bita cikin gidan su kuma suna waje. Anti Labiba da yara sun taso da murnarsu ta wuce su ta shige banÉ—aki. Bata ma kula harda maigidan ba sai da ta gama ta fito.
"Washhh Allah na." Ta furta da ta dawo hayyacinta. Sai kuma ta rungume Antin tana kuka.
"Mene ne na kuka kuma? Ba gashi kin dawo ba."
Ta kalli maigidan da su ke kira Uncle.
"Na zata ba zan sake ganinku ba."
"Ke dai anyi matsoraciya." Cewar Anti Labiba tana dariya.
"Ko nice fa zan tsorata. Bata san wuri ba kuma an bi hanya daban." Anisa ta kare mata.
Murmushi ta yiwa Anisan gami da bata haƙurin rashin cika alƙawarin kai kaya.
"Wa yake ta kaya baiwar Allah? Ai tunda dai kin dawo gida nima buƙatata ta biya."
Kiran sallar magrib aka fara Anisan ta ce tare su ke da yayyenta. Uncle da kansa ya fita ya kira su cikin falo domin su yi sallah bayan an kai musu ruwa sun yi alwala a waje.
Suna idarwa Anisa ta ce za su tafi. Anti Labiba dake kitchen tana haɗa zoɓo ta hana. Sai da ta haɗa komai ta kawo ta nemi Hamdi a falon ta rasa. Maigidanta ta tambaya ina take ya ce ai tun shigowar su sallah bai ganta ba.
ÆŠaki Anti Labiba ta bita. Ta sameta zaune a bakin gado da zumbulelen hijabinta.
"Ki zo ki sake yi musu godiya za su tafi."
"Anti rawar fitsari fa na dinga yi a motar. Ni dai wallahi ba za ni ba."
"Harda saurin rantsuwa?"
"Baki ganni bane" ta faÉ—i tana takaicin abin da tayi.
Falon ta dawo bata san Hamdin na bayanta ba. A bayan labule ta maƙale ta ɗan leƙo da kanta. Hira Uncle yake da su Taj inda a nan su ka gane su ɗin duka ƴan Kano ne. Ya nemi su dinga zumunci domin an zama ɗaya.
Ta bayan labulen ta sake haÉ—a ido da Taj domin yaga tsayuwarta tun farko. Baki ta buÉ—e don da wannan kallon ta gane shi. Zuciyarta ma bata manta ba saboda irin harbawar da tayi da sauri. Ta sanya hannu ta rufe bakinta. Za ta gudu taji muryarsa da ta gane tun a wayarsu ta É—azu.
"Kamal bani key na É—auko mata takalma da wayarta."
Anti Labiba ta waiga ta hango shatinta a labulen.
"Zo ki je ki karɓo mana. Ko sai ya biyoki dasu kuma?"
Sumi-sumi ta fito kai a ƙasa. Kamal ya tsaya bawa Uncle numbar wayarsa. Ita kuma Anisa santin zoɓo take tana kuma wasa da yaran gidan.
Da faɗuwar gaba ta isa bakin motar. Taj ya buɗe ya ɗauko mata takalman da wayar. Maimakon ya miƙa mata sai ya jingina da motar yana kallonta.
"Kin gane ni yanzu ko?"
Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.
"Ashe nan ki ka gudu shi yasa ban ganki ba."
Kallonsa tayi a fakaice "nema na kake yi?"
"Na san inda zan same ki Hamdi. Kawai ganinki ne ban yi ba a wajen."
Shi mai maganar da ita da ake yiwa duk jikinsu tamkar anyi musu duka. Zuƙatansu ke aikin wucin gadi na tsananin murnar sake haɗuwar bazata irin wannan.
"Ina? Makaranta?"
"A gida."
Daina ɓoye fuskarta tayi. Ta kalle shi da mamaki. Muryoyin su Anisa yaji sai ya bata kayanta.
"Sai mun haÉ—u a Kano. Take care."
Motar ya shiga amma bai rufe ba har su ka iso. Hamdi ta sake yi musu godiya sannan su ka shiga mota su ka tafi.
Daren ranar mutumin da bata san sunansa ba ne ya cika mata zuciya da tunani. Bata da wani aiki sai murmushin da bata san lokacin da yake zuwa ba.
A ɓangaren Taj kuma suna yin sallar isha ya ce bacci zai yi. Abincin da Anisa ta dafa Kamal ne kawai ya ci. Shi kuma ya sanya snacks ɗin Hamdi a gaba. A take ya yanke shawarar sanyata a ɓangaren snacks ɗin restaurant ɗin shi wanda Kamal ya yiwa suna da HAPPY TAJ. Kuma ba shi kaɗai ba. Kowa ya ci sai yaba daɗin kayan.
Wayar da su ka dinga magana É—azu ya kira sai yaji muryar direban motar. Ba yadda ya iya. Godiya kawai ya sake yi masa ya katse kiran. Kenan ba da wayarta su ke magana ba? Yayi guntun tsaki. Babu matsala tunda samunta ba zai yi masa wahala ba. Zuciyarsa wasai ya kwanta.
*
Tun asuba Taj ya faÉ—awa Kamal cewa a yau za su koma Kano. Zai yi magana da Anisa kafin su tafi.
Ba musu ya amince " gara haka don zamanmu ma zai iya sanyawa ayi tunanin wata soyayya ku ke bugawa fa."
Da yake da wurwuri ta tashi ta haÉ—a musu breakfast. Shi ya taimaka masa wurin samun ganinta da wuri.
Ta zauna a falo ta sunkuyar da kai ƙasa. Gabaɗaya sai ya dinga jin babu daɗi. Hajjo taje kawai ta sanya mata rai.
"Anisa."
"Na'am Yaya."
"Kinji haÉ—in da Hajjo take son yi mana ko?" Kai ta gyaÉ—a da murmushinta.
"Bani da abin cewa game da karamcin gidan nan naku sai godiya. Anyi min komai a lokacin da na rasa soyayyar mahaifina."
Ta dube shi da tausayawa "kayi haƙuri. Komai zai daidaita in sha Allah."
"Haka nake fata. Amma saboda halin da nake ciki Anisa bana son yin aure yanzu."
A razane ta dube shi. Gabanta na faÉ—uwa kada ya ce baya sonta. A ransa hakan yake son faÉ—a ko don ta bawa wasu dama. Amma yana gudun me zai je ya dawo.
"Ina son lokacin aurena Alhaji ya halarta ba don anyi masa dole ba. Idan na sami ƴaƴa in kai masa ya yi huɗuba yadda yake yiwa ƴaƴan ƴan uwana. Ya kuma sanyawa abin da na samu suna." Yaja numfashi "hakan ba zai samu ba yanzu saboda bai haƙura ba."
"Kana nufin na nemi wani kenan?"
Ta tambaye shi da sanyin jikin da ya sanya masa tausayinta.
"Ina nufin mu bi komai a sannu sannan mu nemi zaɓin Allah. Bana son in yi miki alƙawarin da ba zan iya cikawa ba."
Murmushi tayi ga ƙwalla ta taru a idanunta "na fahimceka, zan kuma cigaba da yi maka addu'a."
"Nagode" yaji zuciyarsa maimakon ta rage nauyi ƙarawa tayi. Reaction ɗin Anisa na sauƙin kai ya kwaɓa masa lamari. Shawarar Kamal ta biyu zai bi. Ba zai yarda ya nuna mata kulawar da za ta saka rai da samunsa ba. Amma abin da kamar wuya domin Hajjo ba za ta sakar masa mara ya sha iska ba. Shi ya san da wannan.
***
Sati guda ya ƙara a Kano ya tattara ya tafi. Ayyuka ne har biyu su ka taso masa na bukuwan manya wanda suka ƙi yarda su nemi wani chef ɗin duk da baya nan. Sun tsara abubuwa da dama da Abba kafin tafiyar tasa.
"Ka cigaba da training É—in yaranka kafin na dawo. Idan sun yi passing test É—ina zan yi retaining É—insu."
Abba ya ce "shagon fa?"
"Ku cigaba da girkinku kafin a ƙarasa wancan."
Gidan Abba Habibu kowa ya yi farinciki da cigaban da ya samu. Wurin yanzu yafi na da komai da komai. Hamdi ce kaÉ—ai da labari yaje mata ba kunya ta ce ko waye Taj É—innan bai burgeta ba. Idan taimako zai yi ai da ya samarwa Abba wata sana'ar. Kuma da yake a idanunta wani matashin É—an daudun take gani, sai taji duk ta tsane shi tun kafin su haÉ—u. Haka kawai ya zo ya yi amfani da halin rashin da suke fama dashi wanda ya hanata shiga jami'a ya sake dulmiya mata uba.
Har ta dawo Kano bayan wata uku da ko sau ɗaya bawan Allahn nan da ya gama da zuciyarta bai nemeta ba. Tun tana damuwa don ta sa rai za ta sake ji daga gare shi har ta haƙura. Sana'ar snacks ta kama ka'in da na'in wadda kuma Allah Ya sanyawa albarka. A ɗan tsukin wajejensu tayi suna. Biki ko suna kowa Hamdi yake kai wa aikin kayan fulawa. Kuma tana yi Abba ya sayar mata a wurinsu. Kafin wani lokaci sai ya zamana su uku suke yi. Zee ta fi ƙwarewa a yin youghurt kamar ita Luciousbites ta koyawa. Abinsu gwanin ban sha'awa.
Taj yana yawan kira ya gaishe da Yaya. Wani lokacin ta wayar Sajida. Idan aka yi mata tayin gaisawa da shi sai tayi ta zillewa. Idan Yaya bata wurin kuwa wasu lokutan har tsiwarta yana ji ta wayar Sajida. Har mamakinta yake yi. Idan ance masa tana da baki haka zai ƙaryata saboda shi dai da fuskar salihai ya ganta.
Su kuma ƴan uwan nata komai su ka ji game da shi ko a hira ne sai sun faɗa mata. Idan aka ce Kamal ya zo kuwa bata yarda su haɗu. Ita fa komai nasa akai kasuwa kawai. Ranar da Zee ta ce mata ya iya indiyanci babu irin shaƙiyancin da bata yi ba. Da aka kwana biyu ya kira wayar Yaya sai ta ɗauka. Amma bata saka a kunne ba. Kawai domin yaji haushi ya fita daga rayuwar gidansu tayi magana.
"Yaya ga Salman Khan É—inku ya kira."
Taj ya kawar da wayar daga bakinsa ya gama dariya sannan ya maƙe murya ya kirata.
"Hamdiyya."
Tsigar jikinta ta tashi. Muryar bata yi irin ta mata sosai ba tunda bai saba ba. Amma dai ya kamanta don ji tayi kamar ta yar da wayar.
"Aap kaise hain?"
"Na'am?" Ta ce da takaici. Ƙila ma har rawa da waƙa ya iya.
Ya sake maimaita tambayar wadda take nufin 'yaya kike?'
Ta taɓe baki "zindagi choringe...ba dai shi ne indiyancin ba?" Ta shiga falo da sauri "Yaya ungo wayarki Taj ɗinku ne."
"Zan ci mutumcinki akan yaron nan Hamdiyya. Ke da zaki ganshi sai kin raina kanki." Yaya ta faÉ—i ba tare da sanin Hamdin ta É—aga kiran ba.
Zee ta ƙara da cewa "ƙila ma ta ce tana son shi."
"Wuce nan wallahi. Wanda nake so namijin gaske ne."