Sashe 52
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ÆŠakin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaÉ—ai zaune akan abin sallah. Suna shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta É—aga hannuwa tana addu'a, Hamdi sai ta É—aga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin.
Umma ta zolayeta da cewa "Wato kin ji ina roƙa muku ƴan bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta cewa amin ko?"
Kunya kamar ta nutse "Allah ban san ita kike yi ba."
"Janye Amin É—in za ki yi?"
"Eh" Hamdi ta faÉ—i da sauri, kunya duk ta ishe ta.
"Yanzu addu'ar tawa ce ba kya so?"
Sake daburcewa tayi ta ce "A'a ban janye ba. Yi haƙuri don Allah"
Umma tayi dariya sosai.
"Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna."
Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu ɓaraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ƴaƴa tunda ba a raba siblings da ƴan rigingimunsu. Amma dai duk inda aka je aka dawo su ɗin tsintsiya ne masu maɗauri guda.
"Hamdiyya don Allah ki riƙe mijinki riƙon da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraɗa kunya."
"In sha Allahu Umma."
"Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaɗai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake so kuma ke ya zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ƙi ji. Ki gani, ki ƙi gani. Babu wata rayuwar auren da take ɗari bisa ɗari. Amma indai kun riƙe juna amana za a sami nutsuwa da rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure."
Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita ɗakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ƴan uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba'in da ɗoriya suna gina ƴaƴansu akan turba mai ɓullewa. Ba za su taɓa maraba da abin da zai kawo rabuwar kai tsakaninsu ba.
"Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki. Haka ne?"
Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaÉ—a a hankali.
Hajiya ta dafa kafaÉ—arta da kulawa "Inna ce kaÉ—ai cikinmu bata sani ba sai kuma Æ´an uwanku da shi Taj É—in. Ko kin faÉ—a masa?"
"A'a."
"Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ƴan uwansa su ka karɓeki hannu bibbiyu. Innarsa da danginta kuwa ..." ta kasa ƙarasawa. Haƙiƙa wannan karon akan Taj yayyen Inna da ƙannenta da su ke duk maza sai ɓarin kuɗi suke yi.
Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an É—auke musu. Lefen da Æ´an uwansa ke haÉ—awa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin babansa haka su ma can yake yi musu.
Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ce
"Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar."
"Hamdiyya addu'a nake so ki yi. Ki roƙi Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai ɓaci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arziƙi bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa'adin zaman ne bai ƙare ba amma da tabi ta ƴan uwanta da ta daɗe a gida."
"Subhanallahi" Hamdi ta faÉ—i cike da tsoro.
"Ƙwarai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama...Haj. A'i da ki yi sallah a ɗakinta ma tafiya za ta yi. Saboda kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki." Ya dubi Hamdi da kyau "a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da muka ɓata muna gina ƴaƴanmu akan soyayyar juna da zumunci?"
Murya na rawa Hamdi ta ce "Hajiya aikin ya yi min nauyi."
"Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa."
"Abbana...Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?"
"Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri'arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki."
"To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?" Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me su ke so taƙamaimai.
"Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ƙare kafiya da taurin kai" Hajiya ta faɗi tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi.
"Duk ya bi ya ɓata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane ɗansa da baban naki da yake ƙi basu ragu da komai ba akan sana'arsu. Allah Yasa kin fahimceni."
"Na gane Hajiya. Amma..."
"Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai haƙuri bai iya fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. Ƴaƴa ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya zamu yi?"
Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana ɗaya su ke yi mata. Ina ita ina ɗaukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taɓa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani.
Hajiya tashi tayi ta ce mata su je É—akin Inna. Sun sameta da yawancin Æ´an matan jikokin nasu. Zolayarta su ke son rai tana biye musu.
"Ku zo ku fita." Hajiya ta nuna musu ƙofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat ɗin Ahmad da ya dage ba zai fita ba.
"Ƙyale shi Hajiya" Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi "iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha. Nawa kawai tuni ne akan ki riƙe maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taɓa haɗaku kuwa?"
"A'a" Hamdi ta bata amsa
"Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haÉ—uwar wajen biki ba tunda an riga an É—aura." Ta nunawa Hamdi kujera "Zauna ba a rasa abin faÉ—a miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba." Cewar Hajiya ga Inna.
Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran É—akunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido.
"Kina da zaɓin kalar kayan ɗakin da ki ke so?"
Tambayar a bazata ta zo mata. Ta É—aga kai daga sunkuyon da tayi.
"A'a."
"Taso ki gani" Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take santinsa a zuciyarta.
Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A É—ofane ta zauna. Inna ta buÉ—e catalogue ta É—ora mata a cinya.
"Buɗe ki zaɓi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaɓarwa mijinki."
Yawu ta haɗiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Wannan fa ita ta haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ƙarshenta sai ta ɓallata.
"Hamdi"
Ita kaɗai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya đan sake.
Inna ta cigaba da magana "kin shiga ɗakuna uku na surukai. Nan kuma ɗakin na mamanki ne. Don Allah ki ɗaukeni a matsayinta domin hakan ne kaɗai zai bani damar yi miki riƙon ƴar cikina."
Cikin rashin jindaɗi Hamdi ta ce "Ki yi haƙuri."
"Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau."
Hamdi ta miƙa mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu'a da su ka haifi matar da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ƴar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji ɗar a zuciyarta ba.
"Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ƴan uwana su ke ɓoyewa game da sharaɗin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ƙarshen auren ba ballantana su cigaba da ɗora zarginsu. Hatta ƴan uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ƙanƙani ne zai faru a ɗorawa babanku laifi. Idan kuwa ta ɓangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu."
Darasi mai girma Inna ta ɗora mata, saɓanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan shekarunta taji kamar an ƙara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ƙwarin gwiwa sosai.
"Taj yana son ki. Ki sa ya ƙara ƙaunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami tangarɗa daga yinsa ba don Allah."
Bayan ta gama ɗaukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a'a. Tunanin da aka barta dashi yafi ƙarfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni.