← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 96

Sashe 90

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin bata jima da sauka daga adaidaita sahu a bakin gate ɗin gidan Taj ba. Ta fiddo wayar taga sunan mai kiran sai kawai ta mayar cikin jaka ta buga gate ɗin. Zuciyarta wani irin zillo tayi da maigadi ya buɗe mata ta shiga bayan ta tabbatar masa da cewa ita ƙanwar maigidan ce.

"Allah Sarki. Gaskiya kuna da yawa Masha Allah. Jiya wasu sun zo. Yau ma kinga mota can..." ya nuna mata motar gidan Yaya Hajiyayye "ta Æ´an uwanku da su ka riga ki isowa."

Wani abu Salwa taji a ranta. Kamar ta juya ta koma. Sai ta tuna da aikin da aka tabbatar mata da zai kama shi. Ta saki murmushi. A gaban Æ´an uwansa shi ne wuri mafi dacewa da ya kamata ya nuna soyayyarsa gareta. Da wannan tunanin ta shiga gidan gaba gaÉ—i.
RAYUWA DA GIƁI 34

Batul Mamman💖

*
Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar.

"Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaÉ—ai ce ban san da tafiyar ba?"

"Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani." Taj ya faɗa da damuwa a tare da shi "kamar wani abu ake ɓoyewa."

"Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai ɓoye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta."

"Amma ta kasa faÉ—a a Home group?"

Waya Yaya Hajiyayye ta É—auko ta dubi Taj "zan yi sanarwa yanzu. Duk mai Æ´an matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su."

"Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa."

"Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?" Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son ɓata lokaci idan aka ce za ayi abu.

Taj ya bata amsa da cewa "Alfarma na nema" yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu.

Basu gama hirar ba Salwa ta ƙwanƙwasa ƙofa. Taj ya tashi zai buɗe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen.

Ita kuwa Firdaus hannun ƙofar ta kama da murnarta tana cewa "Ko ƴan gidanmu ne?"

Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taɓa ganinta da ita ba.

"Anti Salwa ke kaÉ—ai? Ina Anti Zahra da su Hayat?"

"Ni kaÉ—ai ce. Ya Taj yana nan?"

"Eh, shigo ciki."

Ƙamshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita.

"Ya Taj ina wuni?" Tayi magana da wata zuƙaƙƙiyar murya.

"Lafiya ƙalau."

"Ka ganni sai yau ko?"

Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce "mun yi dake za ki zo ne?"

Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce "Noooo, I thought you want to see me. Miss me?"

"Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba." Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara "akwai wani abu a tsakaninku ne?"

Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri.
"Me ki ka gani?"

"Me ta zo yi gidanka a haka?" Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ƙasa.

Danne ɓacin ranta tayi ta ɗauke kai ta dubi Taj.

"Ya Taj a ina za mu yi magana?"

Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ƙofar kitchen ɗin inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faɗa mata baƙuwar da aka yi.

"Ga hanyar É—akinsa can ku je can ku yi."

"Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa." Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara.

Zuciyar Hamdi kamar ta fashe ta juya za ta bar wajen Taj ya damƙo hannunta. Ta ja za ta fizge ya janyota gabaɗaya jikinsa yayi mata wata irin kyakkyawar runguma a gabansu. Ta kuwa fashe da kukan da Anti Labiba ta faɗa mata a gida ana yiwa miji. Da gatanki da tarin soyayya a zuciyarsa ake yinsa don kawai an isa. Kissa adon mata! Da aka faɗa tayi zaton shegantaka ce za ta sa mace kuka babu duka ba zagi daga miji. Ashe ba haka bane. Shi ma kukan yana sanin lokacin zuwansa yayi.

Tayi nasara fiye da tunani. Taj ya shiga tashin hankali sosai. Bayanta kawai yake shafawa yana faÉ—a mata kalaman kwantar da hankali.

Wannan abu ya tayar da hankalin Salwa fiye da ƙima. Me yake faruwa ne? Ya dace zuwa yanzu hankalin Taj ya koma gareta. Ko zuwan nan, tayi ne don son ganin rigimar da take sa ran sun fara.

"Ya Taj..." shiru bai waigo ba, yadda ka san Hamdi ce kaɗai a duniya. Ƙirjinta ya kama hawa da sauka cikin kiɗima ta ce "magana nake fa."

"Kana ji tana kiranka. Ni gidanmu zani. Da na sani ban..." Hamdi ta soma faÉ—i cikin kuka.

Yaya Hajiyayye ta hanata ƙarasawa da cewa "Hamdiyya ki yi haƙuri kinji ko. Taj ya ci albarkacina kada ki yarda ki ɗaga masa hankali akan Salwa. Ƴa na ɗauke ki ba matar ƙani ba. In har na isa to don Allah ki barni da ita."

Hamdi ta É—aga kai ta ture Taj da ta farga da yadda su ke ta ce "Kin isa Yaya. Wallahi kin isa."

"Salwa baki da lafiya ne ko me? Haka kike dama ko kuwa wani abu ne ya same ki?" Yaya Hajiyayye tayi tambayar tana kallon ta.

Kasa magana tayi. Idanunta na bin Hamdi da kallon tsana. At the same time tana jifan Taj da nasa salon kallon na bege. Ta kasa gane ya aka haihu a ragaya. Yardar da tayi da aikin yasa bata kawo haka zai iya faruwa ba. A karo na uku dai ta sake gwada sa'arta ta gani ko akwai dama.

"Ka bani minti biyar mu yi magana Ya Taj. Wurinka na zo don Allah."

Haɓa Yaya Hajiyayye ta kama tsabar mamakin wannan ƙarfin hali. Muryarta a kausashe kuwa ta ce,

"Wuce ciki da matarka yanzun nan." Ta dubi Firdaus "koma kitchen ki kula da girkin." Sannan ta dawo da dubanta ga Salwa "ke kuma kama gabanki yanzun nan kafin in gwada miki ni wace ce."

"Allah na tuba sani kuma na nawa zan yi miki Yaya Hajiyayye? Kishiya ta hanaki zama a gidanki na farko. Alhajinku ya ƙaƙaba wa yaronsa ke aka haifi waɗannan" Salwa ta nuna Firdaus tana yatsina fuska.

Wani kukan kura Firdaus tayi, tayi kan Salwa. Kafin ta kai mata duka Hamdi ta riƙeta da iya ƙarfinta. Firdaus na ƙoƙarin ƙwacewa Taj ya ɗaga hannu zai kai mata mari shi ma Yaya Hajiyayye ta riƙe nasa hannun.

"Jinin Alh. Hayatu da dukan mace? Allah Ya kiyaye."

Maganarta ta farko yaji ta jan hannun Hamdi domin su bar falon. Zamansa tabbas zai janyowa gidansu abin faÉ—a. Da Firdaus ya haÉ—a su ka shiga É—akin Hamdi ya ce su zauna shi kuma ya sake fitowa. Daidai lokacin Yaya Hajiyayye tana yiwa Salwa magana.

"Ki tafi gida Salwa. Wannan abin da kike yi ba zai taɓa baki abin da ki ke nema a mutumce ba."

Taj gaban Salwa ya ƙarasa ya tsaya fuskarsa a murtuke
"Salwa na taɓa cewa ina son ki?"

Shiru tayi. Zuciyarta cike taf da uwar kunya sai dai son zuciya ya riga yaci ƙarfinta. Sunanta kawai da ya kira sau da ya saukar mata da kasala da ƙarin son sa.

"Tunda baki da amsa to ina roƙonki this should realy be the last time. Ina raga miki ne kawai saboda Yaya Ahmad."

'Ko dai shafa masa turaren zan yi in kuma yi masa magana a lokacin?' Salwa ta raya a ranta. Wanda yake hannunta da ta shafa a bakin ƙofar falon ta duba ta hanyar mitstsika yatsunta. Tana ɗaga hannuwa ita kuma Yaya Hajiyayye tayi tunanin rungumarsa za ta yi shi yasa tayi saurin shiga tsakani ta tsinketa da mari tasss. Kunnuwan Salwa sai da su ka ɗauke wuta na wucin gadi.

"Ke jakar ina ce kike ƙoƙarin rungumar baligin namiji mai aure?"

Caraf maganar a kunnuwan Hamdi. Ta yunƙura za ta tashi Firdaus ta ce ko ta fita kada ta saka baki.

"Ki barta da Mama. Wallahi yau ko me take ji dashi ta tara ta samu."

Hannuwa duka biyu riƙe da kumatu su ka sameta. Taj ya kasa kallonta. Zama kawai yayi ya dafe kansa.

"Bata da lafiya Yaya Hajiyayye. Wannan ba abin da mai lafiyayyar ƙwaƙwalwa zai yi bane."

"Babu wani hauka a tare da ita. A nono ta zuƙa kuma in sha Allahu gidanmu nan gani nan bari."

Tana rufe bakinta ta dannawa Ahmad kira.

"Yaya please zan kira ki anjima kaɗan..." rashin samun Salwa a waya ne ya kiɗima shi. Ya rasa wa zai kira ya tafi asibitin. Mami da danginta amma tamkar wadda ta faɗo ita kaɗai saboda baƙin halinta ya kori kowa.

"Ai koma mene ne uzurin indai ba sallah bace to ka saurare ni. Batun wannan yarinyar ne Salwa..."

Katse ta yayi da saurin sa "gidan ki ta zo?"

"Ina fa. Gata a gidan Taj."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yaya Hajiyayye tun É—azu nake kiranta ina nemanta." Ya ce a sanyaye gwanin ban tausayi.

"Ta ina za ta É—auka bayan ta fito yawon zubar da mutumci?"

A tsiwace Salwa ta ce "ni da aure nake son shi ba..."

"Rufe bakin ki" Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da zuciyarta ta kaÉ—a. Firdaus kuwa ta san halin mahaifiyarta dama. Akwai ban dariya da iya zolaya amma kada ka shiga huruminta. Yanzun nan za ta birkice.
Chapter 90 · 0% Book details