Sashe 13
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗokin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da mintuna kaɗan ya bashi mamaki. Belt ɗin da aka ce fasinjoji su ɗaura ya gyara gami da leƙa tagar jirgin. Garin Kano yake gani da tsakar rana ƙarfe biyu da rabi. Tsirarun bishiyoyi da yalwar ciyayin damina sai gine gine marasa tsayi ba kamar inda ya baro ba. Tayoyin jirgin na dira ƙasa sabon yanayi ya baƙunce shi na farinciki da tarin fargaba. Uwayensa da ƴan uwa tun a waya su ke nuna farincikinsu. Alhaji ne damuwarsa. Zai karɓe shi ko kuwa yanzu ma zai cigaba da nuna masa ƙyama kamar wanda yake aikin saɓon Allah?
*
Kafin kowa ya kula wata matashiya dake tsaye tare da iyalan Alh. Hayatu Sule ta hango Taj ta cikin ƙofar gilas. Kyakkyawan saurayi ne wanda duk hangen mace indai ta same shi ta sake ɗaga ido neman wani dole a sanyata a sahun marasa wadatar zuci. Yana kama da ƴan uwansa amma akwai wani abu dake tattare dashi wanda ya bambanta shi dasu da take iya gani. Ba hasken fata bane domin wasu cikin ƴan uwan nasa sun fi shi haske. Haiba da cikar halittarsa su ne suka fi komai ɗaukar hankalinta. Tana can duniyar saƙe saƙe bata kula da yadda ƴan uwan nasa da ƴaƴansu su ka bar wurin ba domin tararsa sai daga baya.
Idanu kansu su ka dawo ganin yadda ake pasin-pasin wajen rungumar Taj. Gashi taron mata don Ahmad da Kamal ne kaÉ—ai maza in ka cire jikokin gidan da ba wani sabo suka yi dashi sama da waya ba. Bishir da Abba su na makaranta.
"Aunty Salwa mu je mana."
Wani yaro ne ya yi maganar yana jan hannun matashiyar budurwar da Taj ya sacewa zuciya farat É—aya. Murmushin jin kunyar kanta tayi ta kama hannun yaron su ka matsa kusa dasu. Yaron ya saki hannunta ya koma wajen Ahmad yana cewa ya É—aga shi zai ga Uncle Taj.
"Daddy ni bai ganni ba. ÆŠaga ni sama."
Kamal ne ya ɗaga yaron ya miƙawa Taj. Ya karɓe shi ya rungume yana sumbatar kumatunsa.
"Babana da kansa."
Yaron ya girgiza kai "Uncle Taj sunana Hayat."
"Ba Hayatu ba?" Taj ya ce da alamun mamakin da yasa yaron saurin cewa "Hayat yafi daÉ—i."
Dariya kowa yayi sannan Ahmad ya É—an turo budurwar nan gaba.
"Ga Salwa ku gaisa."
Taj ya sakar mata murmushi domin kuwa ƙanwar yayansa Ahmad ce da su ka haɗa uwa. A yanzu haka sakamakon karatu da ya kawota Kano daga Bauchi garin da mahaifiyar tasa ta sake aure shi ne take zaune a gidansa. Shekararta ta biyu kenan a Kano kuma iyalin Alh. Hayatu har matansa basu nuna mata wani abu da zai sosa zuciyarta ba. Ƙanwar ɗansu ita ma ƴarsu ce.
Shi Ahmad matarsa É—aya da yara biyu. Hayat da ake kira da sunansa bisa umarnin Alhaji sai jaririyar da ko arba'in É—inta ba ayi ba mai sunan Mama wato Aisha.
ÆŠunguma su ka yi a motoci huÉ—u su ka nufi gida. Mazan motarsu É—aya su kaÉ—ai. Kamal ya yiwa Taj bayanin cewa sun canja shawara zai zauna a gidan Ahmad har lokacin komawarsa.
Jikinsa a sanyaye ya tambaye su "Alhaji ya ce kada na zauna masa a gida ne?"
"A'a" Ahmad ya faÉ—i da sauri.
"Yaya ka faɗa masa gaskiya mana." Cewar Kamal dake tuƙi "ɓoyewar bata da wani amfani."
"FaÉ—a min me ya ce Happiness."
Tiryan tiryan kuwa Kamal ya faɗa masa yadda Alhaji yaje ɓangarensu har ɗaki ya ce yaga saƙon Taj na tahowa buɗe gidan abinci. Ba zai hanasu mu'amala da ɗan uwansu ba amma indai da niyyar cigaba da saɓa masa ya dawo ya nemi wurin kwana.
"Amma ya amince ka shiga gidan ka gaishe da su Hajiya. Kawai dai kada ka bari ku haÉ—u."
"Zan zauna a hotel."
Dukkaninsu kallonsa su ka yi. Ba kuma don abin da ya ce ba, yadda muryarsa ta fito kai ka san ba ƙaramar dauriya ya yi ba. A shaƙe take da wani irin rauni daga zuciyarsa.
"A gidana za ka zauna. Tun jiya nasa Salwa ta gyara maka É—aki." Ahmad dake baya ya zura hannu gaban motar ya É—an bubbuga masa kafaÉ—a.
"Ba zan zauna na takura iyalinka ba. Infact mutumcina ma zai zube. Kawai bamu taɓa haɗuwa ba sai da aka koreni daga gida for the second time."
Dariya Kamal ya yi "zaman hotel É—in ba matsala bane amma ba mutumcin aljihunka bane gaskiya a garin da kake da gidan Æ´an uwa sama da hamsin da za su so zamanka tare dasu."
Kamar shi ya kar zomon, Taj ya É—aure fuska ya ce masa "kawai ka faÉ—i abin da yake ranka. Kana tsoron kada naje ace na fara bin mata ko?"
"Ba a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai kai da kake kan tsini idan ka ƙara da kwanan hotel ban san yaya za ku kwashe da Alhaji ba."
"Allah ni ba É—an isk* bane. Saboda tsoron kada Alhaji ya yi min baki watarana na lalace ko girlfriend na kasa yi." Taj ya amsa defensively.
"Daga budurwa sai lalacewa Taj?" Cewar Ahmad, shi da Kamal su na dariya.
Shi kuma Kamal ya ce "dama me za kayi da busassun turawan nan da ba su da gaba da baya?"
Haɓa Taj ya riƙe yana kallonsa kafin ya ce "Yaya kaji irin zancen banzan da Happiness yake yi ko? He is long overdue for marriage."
"Da za ku yi auren maybe da ka samu daidaitawa da Alhaji."
Hirar tasu sai ta koma ta dacewar Kamal da Taj su nemi mata su yi aure haka nan. Da haka su ka isa gida. Sai dai kafin maigadi ya buÉ—e musu gate motar Alhaji ta tsaya a bayan tasu.
"Alhaji ne" Ahmad ya faÉ—awa Taj.
Zuciyarsa ya ƙarfafa ya fita daga motar duk da tunin da yayunsa ke yi masa akan gargaɗin Alhajin na baya son ganinsa. Da sassarfa ya isa bakin motar da gilasanta duka baƙaƙe ne. Ba a sauke ko ɗaya ba a ciki amma ya tabbatar daga cikin ana ganinsa. Direba ke tuƙin motar amma da dishi-dishi yana iya hango Alhaji zaune a baya. Ya taka har bakin tagar ɓangaren nasa ya durƙusa cike da girmamawa.
"Sannu da zuwa Alhaji."
Tun a hanya jikinsa dama ya bashi zai ga ɗan nasa. Tunaninsa ne ma ya hana shi gama uzurin da ya fitar dashi. Yanzu da yake ganinsa kewar Taj ɗin ta mamaye zuciyarsa. Idanunsa su ka tara ƙwallar da yake jin abin kunya ne a ganshi da ita. Saboda haka bai ɓata lokaci ba wurin umartar direbansa da ya yi ribas su bar wurin.
"Alhaji ka daure ka saurari yaron nan don Allah."
"Koma na ce!"
Direba ya so yin musu Alhajin ya manta da dattijantakar mutumin ya daka masa tsawa. Wannan yasa shi danna accelerator bayan yasa giya a ribas da ƙarfi. Ƙura kuwa ta tashi ta baɗe Taj da yake durƙushe har lokacin bai motsa ba.
Ba shi ya tashi ba duk da magiyar su Kamal da wasu cikin matan da su ka riga su dawowa daga airport. Anyi a idonsu ne saboda an buÉ—e gate. Kuma dama Kamal na yin horn su ka firfito tare da iyayensu.
Ahmad ne ya ɗaga shi zai shiga dashi gidan ya cije ƙafarsa.
"Mu je gidan naka."
"Kaga su Umma fa a tsaye. Mu ƙarasa ku gaisa sai mu tafi."
Kai a sunkuye Taj ya girgiza kai.
"Wallahi ba zan shiga gidan nan ba sai ranar da mai shi ya kirani ciki da kansa."
Motar ya kama zai buɗe Kamal yayi saurin danna lock da muƙullin hannunsa.
"Kada kayi taurin kai. Don Allah ka shiga ciki."
Kai Taj ya ɗaga ya hango Salwa a tsaye tare da sauran. Bai yarda ya haɗa ido da kowa cikin matan gidan ba ya ƙwala mata kira.
"Salwa..."
Gabanta ya faɗi, zuciyarta tayi wani irin bugu. Sai kuma wani irin ɗumi mai daɗi ya lulluɓe mata jiki da ta tuna sunanta kaɗai Taj ya ambata a wannan yanayin da yake ciki. Ƙafafunta kusan da ikon kansu su ka ƙaraso da ita gabansa.
"Kai ni gidan Yaya a rickshaw (haka ake kiran adaidaita sahu a India)."
Alamun rashin fahimta ya gani a tare da ita ya nuno mata guda da ya shigo layin nasu.
Kai Ahmad ya girgiza domin hanata sannan ya umarci Kamal da buɗe motar. Da kansa ya tura Taj baya ganin ƙanin nasa ƙiris yake jira ya saki ƙwallar da ta rufe masa idanu.
"Kai shi gida zan taho."
Haka kawai ya ce da Kamal ya buÉ—e gaba ya ce da Salwa ta É—auki Hayat su bi shi. Suna tafiya shi da sauran suka koma ciki.
"Korarsa ya sake yi?" Umma ta tambaya da kukanta.
"A'a. Ku shirya mu je gidana ku gan shi."
"Me ya faru Ahmad?"
Mama da Hajiya duka kuka su ke yi. Inna kuwa jingina tayi da ƙofar shiga gidan ta runtse idanunta. Da yake duk da mayafi su ka fito Ahmad buɗe motarsa da ya bari a gidan ya yi ya ce su shiga.
"Alhaji zai yi faÉ—a Ahmad."
Da mamaki mai haÉ—e da É—imbin takaici Mama ta kalli Inna da tayi maganar baki buÉ—e.
"Sau tari damuwar uwa da jajircewarta na taimakawa wurin ragewa Æ´aÆ´a raÉ—aÉ—in hukuncin uba. Kina tsammanin akwai riba idan duka ku biyun kun juya masa baya? Ko kuwa kina ganin yin hakan wata gwaninta ce da Alhaji zai yaba?"
Umma dama tafi kowa zafi kuma maganarta indai akan gaskiya ne ba kasafai take taunata ba.
Jiki ba ƙwari Inna ta ce "ba haka bane."
Umma ta ce "to yaya ne? Sama da shekara goma rabon da ɗanki ya sanya ki a ido zahiri. Banda ma Allah Yasa Takwara (da yake haka su ke kiran juna da Amma) jajirtacciya ce da tuni ɗannan ya bi duniya. Uwa da uba a raye amma kun bar masa wawakeken giɓi mai wuyar cikewa. Baku san ku yabi ƙoƙarinsa ko kuyi masa faɗan kuskure ba."
"Kiyi haƙuri don Allah" Inna ta ce tana kuka sosai.