Sashe 69
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba."
Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buÉ—e lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin Æ´an rakiyarta.
"Nafi ƙarfin zama borar gida."
"Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday."
"Allah Ya kaimu" ta faɗi sannan ta ƙifta masa ido don tsokana.
A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta.
"Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku ɗan ƙara matsowa mana."
Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa É—aya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faÉ—i sai ta É—ora nata hannuwan a kafaÉ—unsa.
"In miki waƙa?" Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ƙaunar juna.
Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka É—auki hoton. Ya yi kyau sosai.
Bayan an gama taro mai ban sha'awa da Firdaus ta koma gida ta dinga ɗora hotunan kamu a status. Kuma wannan hoto shi ne na farkon da Salwa ta fara cin karo dashi. Zuciyarta a take ta ɗauki zafi. Ta juya ta kalli Mami dake kwance tana bacci ga yawu yana dalala ta gefen bakinta. Dole taje Kano ko ta wane hali. Wayarta ta ɗauko ta kira Ahmad ta faɗa masa hatsarin da Mami tayi da roƙonsa akan ya dawo dasu Aminu Kano Teaching Hospital saboda a nan Bauchi babanta yaƙi sakin kuɗi a dubata yadda ya dace (a ƙaryarta). Duk da baban nata ya gargaɗesu da ƴan uwanta da su yi shiru har sai ta farfaɗo saboda bai san me zai cewa Ahmad ɗin ba. Yana kunyar yaron kuma yana tsoron sake ɓatawa Alh. Hayatu rai.
"Me ya sa zai ce kada a faɗa min? Kwananku nawa a asibitin? Shi ne kullum idan na kira ki ke min ƙaryar ƙauye ta tafi" Ahmad ya ce cikin tashin hankali.
"Sharri aka yi mata wai tayi masa asiri."
"Zan kira shi mu yi magana. Ku shirya, idan na zo gobe in sha Allah sai mu taho tare."
RAYUWA DA GIÆI 27
Batul Mamman💖
_For Maryam Yusra because you deserve it! Allah Ya baki lafiya._
(Don Allah duk waɗanda su ka biya kuɗin talla na cikin labari kada su ƙosa. Saboda kun fi son wanda zai fito cikin labarin dole sai an zo gaɓar da zai dace. Ina fatan jinkirin ba zai sa muku damuwa ba. Har kullum ina godiya. SonSo)
***
A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo ɗin. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. Gabaɗaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daɗe. Duk an tafi wajen dinner ɗin Taj da Hamdi. Hatta masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga ɓangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa ɓargo. Sai kayayyyakin ƴaƴansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ƙasa su ka bar nasu.
"Ganɗoki" ya yi murmushi yana mai duƙawa ya ɗauke kwalbar turaren da aka bari a ƙasa.
Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ƙasa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da ɗakunan matansa fa nasa ne. Zuri'arsa ce. Shi kaɗai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba'in. Ga ƴaƴa ga tarin dukiyar da ko yau ya ajiye kasuwanci ba za su buƙaci komai ba a shekara goma masu zuwa.
Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waɗanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arziƙinsa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arziƙinsa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ƴaƴansa babu fasiƙi. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri'a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya ɗauka ƙarfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaɗai ke iyawa.
Sai gashi an wayi gari sun haɗa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ƙwai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ƴaƴan dangi ma suna cin arziƙin ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi ɗabi'un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da ɗan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karɓi wannan aure. Salwa ce ba zai taɓa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar ɗan daudu yafi mushriki a wurinsa.
***
Ƙememe Yaya taƙi shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ƴan uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaɗa aka raya taƙi chanja shawara. Gashi ƴan matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ƙawaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ƙawa tare su ke yi.
Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre ɗin inda a saman wurin ne za a rangaɗa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. Ɗaya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ƙwalisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi baƙi da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la'asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita ɗin Hamdiyya ce ɗiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ƴar wani ƙusa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya.
Anti Labiba ce ta kira Sajida ta faÉ—a mata rigimar da ake yi da Yaya akan ta shirya. Sajida tana ji ta san babu wani kunya ko kawaici da yasa mahaifiyar tasu son zaman gida. A nata tunanin rashin zuwan zai taimaka ya É—ago darajar Æ´aÆ´anta a idon mutane. Bata son yin abin da zai janyo mata ido harma ayi ta ambaton ita ce maman amarya, daga nan wanda bai sani ba a bashi labarin cewa babansu ma tsohon É—an daudu ne.
"Don Allah ba ta wayar Anti."
Harara kala kala Yaya ta gama yiwa Anti Labiba kafin ta karɓa.
"Yaya me yasa ba za ki je ba?"
Caraf a kunnen Hamdi. Ta karɓi wayar ana yi mata ɗauri da wani yadi haɗe da net mai santsi.
"Yaya ba za ki ba?"
Shiru tayi saboda taji yadda muryar Hamdin ta canja.
"Yaya?"
"Ina jin ki. Ga iyayenku nan. Kowa zai je. Me zan je yi ni kuma?"
Zee da Sajida kusa da Hamdi su ka dawo su ka kara kunnuwansu. Kowacce tana iya gane zancen na Yaya akwai damuwa a ciki. Hamdi sai cewa tayi,
"Wallahi Yaya idan baki je ba nima daga nan gida zan taho." Su Zee jinjina mata su ka yi da thumbs up da ta faÉ—i haka.
"Ke ba na son rashin kunya."
"Allah Yaya. Zan zauna a saman nan har sai kin zo."
Sajida ta miƙawa wayarta ta koma aka cigaba da ɗauri. Sai dai ana yi ƙwalla na sauko mata. Mai kwalliya tabi ta tada hankali. Idan kwalliyar ta caɓe ko amarya bata sauka da wuri ba za a sami matsala.
"Za fa ta zo tunda taji kin yi rantsuwar nan." Cewar Sajida.
"Ke ma ai bata je naki ba." Zee ta tunatar da ita.
Ita dai me kwalliya haƙuri ta soma bawa Hamdi ganin wankin hula yana neman kai su dare. Sai da ya rage pins kawai za a saka a jikin mayafi da head ɗin sannan kukan nata ya ƙaru. Daga can ƙasan zuciyarta take yinsa. Ta ƙara jinjinawa uwa a duk inda take. Babu yadda za ayi ace Yaya bata son ganin ƴaƴanta a wajen bikinsu suna walwala kamar kowacce uwa. Amma kawai don kada a aibata mata su saboda yanayin tafiyarta shi ne ta zaɓi zaman gida.
Da bikin Sajida duk sun ɗauka kawaicin uwa ne. Musamman da basu ga mahaifiyar Safwan a wajen event ɗin nasu ba (baban Safwan ya hanata zuwa). Yanzu kuwa jiya komai da iyayen Taj aka yi. Yau ma su ne ƙirjin biki. Sai ace babu mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce.
"Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caɓewa fa." Cewar Zee ta ƙara miƙawa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon.
Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa "bar ni da ita."
Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faÉ—a masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa.
"Saka mata wayar a kunne."
Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata É—in. Da rarrashi ya yi mata magana.
"Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaɗa kai kamar ƙadangaru."
Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah.
"Waƙar bata da hayaniya sai na taya ka."
"Haka ki ka ce?" Ya tambayeta yana murmushi "Wayarki na kusa?"
"Eh"