← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 96

Sashe 72

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gama rubutun su ka É—ago kai.

"Happy Taj wa ka fi so?"

"Alh. Hayatu Sule Maitakalmi" ya faɗi da murya mai ban tausayi. Inna sunkuyar da kai tayi ta bar su Amma dasu Mama su da share ƙwalla.

"Amarya wa ki ka rubuta?"

Takardar ta É—aga masa (Alhaji) ta rubuta.

Ƴan uwan Taj su ka dinga tafa mata suna murna.

"Wa ki ka fi so amaryar Happy Taj?" MC ya tambayeta.

Da murmushi ta ce "Mamana, Yaya" tana mai kallon inda Yaya take a zaune. Baiwar Allah ita ma ƙwallar ta kama yi.

"Taj wa ka rubuta?"

(Duka iyayenta)

MC ya nuna Hamdi ya ce "a tafawa amarya Hamdiyya."

Wurin ya kaure da hayaniya da murnar mutane. Wurin amsa tambayoyin nan ba ƙaramin kiɗima jama'a suka yi ba tun ma suna tare da masu taimaka musu.

Taj ya fitittike ya ce bai yarda ba.
"Ni fa da gangan na faɗi saboda nayi zaton ba za ta iya amsa nawa ba tunda ban taɓa faɗa mata ba."

MC ya ce "Kaga rigimammen ango" aka bushe da dariya "abin da za ta saka ka kake gudu?"

"Eh wallahi. Na san me wahala za ta saka ni." Ya sha kunu da wasa.

"Wai haka?"

"A'a" ta amsa mischieviously. Kai kana ganin farincikinta ka san amsar bata kai zuci ba.

"To ke mu ke sauraro"

Hamdi ta zaro ido "wai a nan zan faÉ—a?"

"Eh mana" cewar MC

"Iyayenmu fa duk suna nan" ta kalli saitin teburin iyayen nasu a kunyace.

"Ga takarda ki rubuta masa ba sai mun ji ba."

(Don Allah ka daina yi min waƙar India)

Tana bashi ya saka loudspeaker a bakinsa ya karantawa kowa. Aka fara dariya da ya ce a bashi fili.

"Waƙar ƙarshe zan yi irin wadda ake mirginawa a ƙasa ana kuka a gidan boss."

Hamdi duka hannuwa tasa ta rufe fuskarta.

"Na fasa kada tayi mana kuka." Taj ya faÉ—i yana murmushi.

Mutane suna ta dariya. MC ya ce Taj ya faÉ—i wani abu kafin su koma mazauninsu.

"Nagode Allah da Ya bani Hamdiyya Habib Umar. Allah Ya bamu zaman lafiya."

MC ya turawa Hamdi speaker saitinta "ke kuma me za ki ce?"

Ta kalli Taj ta rufe fuska da gefen mayafi "Amin....au mungode zan ce."

"Awwnnnnnnn" É—in mutane kamar ta fasa dodon kunne. Aka dinga tafa musu har su ka zauna.

Mutane sun nishaɗantu matuƙa. Daga nan aka fara rabon abinci wanda a yau ma'aikatan Happy Taj su ka baje kolin basira wajen yin wanda yafi na kullum daɗi. Nau'in girki na gaske kala kala aka yi. Luciousbites da kanta ba saƙo ba kuma ita tayi snacks da kuma daddaɗan youghurt da furarta wanda ake sha ana santi. Juice kuwa sai wanda mutum ya zaɓa.
Babu mutum ɗaya da zai ce ya tafi gida da yunwa. Kowa yaci ya ƙoshi.

Bayan an gama ne DJ ya soma nasa aikin. Anti Zahra tana bawa Hayat ruwa ta hango Ahmad yana yi mata signal. Wayarta yace ta duba. Tana É—auka call É—in Salwa na shigowa. Kira yafi arba'in. A zatonta abin da zai ce ta duba kenan shi yasa ta É—auka.

Salwa ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya "Anti ina ta kira..."

"Banji ba ne Salwa. Ya gida?"

A gadarance ta ce "ina waje tun É—azu. Kin taho da katina?"

Anti Zahra ta kalli Ahmad da har yanzu alamar duba waya yake yi mata da hannu tace "wane katin?"

"Ba a aiko min ba?"

"Ke da kike Bauchi ai ban san za ki zo ba."

Tashi tayi ta bar yaran a wajen ƴan uwanta da suke seat guda ta ƙarasa wajen Ahmad. Waje su ka fita saboda hayaniya.

"Ya zance ki duba waya ki tsaya amsa kira kuma?"

"Sorry, na zata kiran Salwa kake nufin na duba." Ta nuna masa missed calls.

"Ƙyaleta. Nayi miki text nace na taho da Mami bata da lafiya. Gobe zan kai ta asibiti in sha Allah."

"Subhanallah. Shi ne muke nan? Bari na É—auko su Aisha mu tafi."

"Kada ki damu. Salwa na gidan. Bana so mu koma ne kiga baƙi. A can ma ya dace na sanar dake to kuma ban sami nutsuwa ba."

Murmushi tayi masa "babu komai. Amma Salwa fa ta ce min tana waje."

"Waje kuma?"

"Eh, kati take so in..."

"Koma ciki."

Yayi maganar yana sauko matattakalar da za ta sada shi da hanyar fita. A waje ya ganta tsaye can gefe ta rakuɓe kamar wata almajira. Duk sauron wajen nan ya tabbata ya gama cinyeta. Ta ɗan bashi tausayi amma bai nuna mata ba.

"Taho mu je."

Masu gadin suna ganin shi su ka bata hanya ta wuce. Magana ta so yi masa amma babu fuska. Da sauri sauri ya ding tafiya sai da su ka shiga hall É—in sannan ya nuna mata inda ango da amarya suke.

Taj da Hamdi ke tsaye a filin rawa taƙi motsi. Ya riƙe hannayenta yana magana tana dariya. Ce mata yake ko dai ta saki jikinta ko ya kama break dance yanzun nan.

"Kin gani Salwa? Ke ya fara sani kafin Hamdiyya. Da yana sonki da kece a tsaye a can. Don Allah ki samawa kanki lafiya ki jira naki mijin."

"Na haƙura Yaya. Tafiya ma zan yi." Ta ce kamar gaske.

"Jirani a nan in faÉ—awa Zahra. Nan da kamar 15 minutes sai mu tafi."

Yana barin wajen tayi gaba. Ido rufe ta nufi inda su Taj su ke. Sun bar rawar sai hotuna da ake ta ɗauka. Tun kafin ta ƙarasa inda suke Hamdi ta hangota. Gabanta ya kama faɗuwa sai ta soma karanta Ayatul kursiyyu. Salwa na zuwa ta shige tsakaninsu ko sallama babu.

"Ya Taj ayi mana hoto."

Yadda kafaɗarta take gugar tasa ko Hamdi da suke tsaye tun dazu bata yi wannan tsayuwar dashi ba. Matsawa yayi da sauri yana a'ziyya a zuci sai ji yayi ta riƙe masa hannu. Wani maiƙo maiƙo da danshin da ya yi zaton na gumi ne daga hannun nata duk ta shafa masa.

Idanun Hamdi a take su ka rikiɗe sai dai ganin idon mutane sai ta daure zuciyarta. Taj na jan hannunsa ya fara jin ciwon kai Salwa sai ta sake ƙarfin riƙon.

Basu san daga ina ba kawai sai wani hannun su ka ji ya kama hannayensu dake haÉ—e ya raba.

"Zan ci mutumcinki Salwa akan yarona kin ji ko."

A matuƙar tsorace Salwa ta dubi Inna. Hanjin cikinta su ka kaɗa. Layar da take shirin sakawa a baki ta tauna sannan ta umarce shi da ya biyota ta saɓule ba tare da ta sani ba. Barin wurin tayi da wani irin sauri. Tana tafiya Inna ta duƙa da sunan Allah a bakinta ta ɗauki layar. Sunan ɗanta ta gani ɓaro ɓaro a jiki. Ta haɗa ido da Hamdi da taga komai ta matsa kusa da ita.

"Kama shi ku zauna. Zan faÉ—awa Amma a rufe taron haka."

Kai Hamdi ta gyaɗa. Ta riƙo Taj da idanunsa su ka birkice. Bayan sun zauna tana ta tofa masa addu'a a fakaice ya dawo daidai. Ya ce ta tashi ya kaita gida.

"Su Yaya fa?"

"Bishir zai kai su. I need alone time with you."

"Na'am?"

"Nace muje na kama mana hotel."

"Wallahi ba haka ka ce ba." Ta faÉ—a a tsorace.

Dariya ya yi mata "Ki ka ce baki ji ba."

"Da wasa nake."

"Matsoraciya."

Addu'ar rufe taro aka yi. Kowa ya tashi cikin murna da jindaÉ—in wannan biki mai ban sha'awa. Baballe ya É—auki Zee, Safwan ya É—auki Sajida sannan Taj ya tafi da Hamdi.

Ahmad da Anti Zahra kuwa mamakin duniya ne ya kama su da su ka shiga gida su ka tarar ana bushashar cin shinkafa dafaduka da farfesun kifi wanda É—aya daga cikin Æ´aÆ´an Anti Zabba'u ta dafa.
RAYUWA DA GIƁI 28

Batul Mamman💖

This page is sponsored by SAFFADEMPORIUM the world of amazing scents. Kun san da wuya na tallata abin da ban sani ba. To jama'a akan saffademporium ni É—in jiyau ce kuma ganau. Ido ya gani, hanci ya shaida! Safiyya Ummu Abdoul our one and only Chairlady ta Fikra Writers Association ita ce mamallakiyarsa. Komai na Fikra kuwa daban yake. Akwai Raudha turaren carpet da kujeru, Naeema airfreshner, oils zafafa guda biyar, turaren kaya na maza da mata. Khumra masu tsayawa a rai da kuma turaren wuta.

Za ku iya samunta a manhajar instagram @saffademporium ko wannan layin 07010137848.
Sayen nagari...mayar da ƙamshi gida!

~~~~~~~~

Kun kira
Kun turo saƙo
Kun zo dubiya har asibiti
Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo idan ba kyakkyawar addu'a da fatan alkhairi ba?

A yayinda da nake post babu abin da yake yi min daɗi sama da kyawawan addu'o'in biyan buƙata da ku ke yi min. Wannan addu'ar ita ce babban abin dake ƙarfafa min gwiwar typing ko da jikina baya min daɗi domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba. A yau ina mai ƙara godiya ga Allah da ku bakiɗaya. Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min. Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku.

Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nishaɗi. In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba. Sai kun ƙara haƙuri saboda yanayi ya ƙara canjawa. Ga ƙaramin goyo, yara, ɗawainiyar gida da aiki. Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho. In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah.

SonSo

***

Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh. Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki. Nan kuwa kaf ɗinsu ahalin gidan ne. Babu bare ko ɗaya sai masu aiki. Ƴaƴansa ne da jikoki. Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba. Falon kamar ba zai ɗaukesu ba saboda yawa. Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi.

"Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin É—akuna tun wuri aje a kwashe. Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe." Cewar Ummukulsum ga jikokin. Ita ce babbar Æ´ar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus Æ´ar ajin su Hamdi.

"Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba..."
Chapter 72 · 0% Book details