Sashe 20
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?"
A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba.
Gidan su ka bi shi. Daga soron ya É—aga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga Æ´ar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace.
"Abba yi haƙuri ban ji ba ne."
Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai.
"Tabarma za ki kawo da ruwa."
Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa.
"Kamar yadda É—an uwana ya faÉ—a maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka."
"Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya."
Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?"
"Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal ya yi saurin katse shi.
"Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska.
"Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faÉ—a maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin."
Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?
Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj.
"Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara."
KuÉ—i Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri.
"Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin."
"Happy!"
Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau.
"Kayi haƙuri don Allah. Bari mu tafi."
Taj ya ɓata fuska "Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness."
Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ƴar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma haƙuri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faɗa kaca-kaca.
"So kake Alhaji ya mutu da baƙincikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daɗi?"
"Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?"
"Sai ka taimaka masa da kuÉ—i." Kamal ya ce har zuciyarsa.
"Are you serious? Yanzu da aiki da kuÉ—i wanne ya fi?"
Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi.
"Masifaffe." Taj ya furta yana harar motar.
*
Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. Ƙarya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin baƙinciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau ɗaya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda ɗan ƙorafi.
"Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daÉ—ewa za ki yi ba gara duka time É—in ki ya zama na family."
Ji tayi kamar ya faÉ—a mata magana. Ta daure ta ce "Ba ka cikin family É—ina kenan?"
"In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki."
Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce "me za ka saka?"
"Ƙanwata Salwa. Yadda nake saving sunan ƴan gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata" Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce "bari na barki ki huta haka. Sai da safe."
Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karɓi girkin dare. Zahra tana ta faɗa mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haɗa juice ɗin abarba, mangwaro da ɗanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi.
Bayan tayi sallar la'asar ta shiga ɗakin Taj. Yana ƙullewa idan zai fita amma baya taɓa zare key ɗin. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su buƙaci shiga idan baya nan.
"Salwa me ki ke nema a nan?" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buɗe ƙofar.
Tsintsiya ta sameta tana gyarawa É—auri. Tana ganinta tayi murmushi.
"Anti Zahra gyara É—akin zan yi."
Curiosity yasa Zahra ta ɗan leƙa. Baya buƙatar wani gyara na a zo a gani.
"Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga É—akinsa."
"Yau É—aya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri."
Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haÉ—a komai ta wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. ÆŠaki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa 'uhmmm'. Yau ko É—akin miji ne aka yiwa haka ai dole ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu.
Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta saka da ƙaramin mayafi ta zauna a falo tana ta ƙamshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. Jindaɗin yadda take kula da shi zai kwaɗaita masa mallakarta a matsayin matar aure.
Wuraren ƙarfe biyar da rabi Taj ɗin ya shigo da sauran fushin faɗansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da Ahmad. Ya ɗauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita.
Ya dakata da tafiya "Har hutun ya ƙare? Ko dai kin dawo birnin da yafi ƙauyenku?" Ya ce da ita da zolaya.
Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda taji cewa Taj ya kusa komawa bane.
Da Aisha ya shige ɗaki a kafaɗarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami ɗakin. Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha'awa. Ya shiga toilet nan ma ƙamshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taɓa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa ɗaya ya tabbatar dai a wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya ɗauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri.
"Anti Zahra waye ya gyara min É—aki ne?"
Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da kai. Sauƙin hali irin na Taj bai hana shi nuna ɓacin rai ba kuwa.
"Ke ki ka wanke min underwear?"
Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce "underwear kuma?"
Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro.
Taj ya murtuke fuska.
"You shouldn't have. Next time please kada ki taɓa min." Ya duƙa ya miƙawa Zahra ɗiyarta sannan ya dubi Ahmad "Yaya zan ɗan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo."
Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige É—aki.
Ai kuwa kamar jira yake ya soma faÉ—a.
"Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?"
Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faÉ—an yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu.
"Ba tun yau na kula kina son Taj ba..." sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taɓe baki "wanda bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba."
"Yaya..."
Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faÉ—a mata gaskiya ba.
"Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, Æ´ar matar da ya saka zai faranta masa rai?"
A tsorace ta kalle shi "Yaya ni meye laifina?"