← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 96

Sashe 30

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Taj ta karaÉ—e wurin ta speaker a daidai lokacin da su ke shiga.
RAYUWA DA GIƁI 15

Batul Mamman💖

Sautin amsa sallamar cika wajen ya yi kamar zai fasa kunnuwa. Kusan a lokaci guda Hamdi, Salwa da Anisa su ka toshe kunnuwansu. Sakamakon ƙatuwar sipikar dake kusa dasu wadda ta ƙara ƙarfin sautin. La'akari su ka yi da toshe kunnen da su ka yi a lokaci guda sai su ka kama dariya.

Anisa dakatawa tayi da ta kalli fuskar Æ´an matan dake gabanta. Bata san Salwa ba, amma ta so ta tuna Hamdi. Ita ma Hamdin sai aka yi dace ta kalleta a lokacin. Mamaki ne ya kama ta domin kuwa babu yadda za ayi ta ce ta manta kamanni da sunan Anisa.

Girarta ce ta É—age tana mai yi mata kallon sani ta ce "Anisan Abuja?"

Gaban Anisa ya yi wani mahaukacin faÉ—uwa. Ba wai son ganin Hamdin ne bata yi ba. Abin da ya kawota taron buÉ—e restaurant É—in Taj wanda bata manta ba shi ya dinga rarrashinta a waya har su ka isa inda take a lokacin nan. Kada dai irin abin da take karantawa a social media a ce vendor tayi snatching miji ko saurayin costumer ne zai sameta?

Hamdi kuwa tunda gari ya waye sai yanzu tayi dariyar da ta kai mata zuci. Fuskarta ta haskaka da farincikin da yake ranta.

"Allah Sarki. Naji daÉ—in sake ganinki. Lokacin da mu ka haÉ—u bani da waya. Daga baya da nayi kuma Anti Labiba ta ce ashe bata yi saving number É—inki ba."

Da ƙyar Anisa ta haɗiyi yawu ta ƙirƙiri murmushi. Yanayinta na rashin nutsuwa duka a idon Salwa. Har ta kai ta matsu da son sanin me ya kawo wannan canji a tare da Anisan. Zuwan Sajida da Zee wajen ne ya taimakawa Anisa ta samu ta daina murmushin dolen da take ta yi.

"Hamdi zo mu zauna ga seat Yaya Kamal ya ce sai an gama speech za a buÉ—e ko'ina a shiga."

"Har Kamal kin sani?" Anisa ta ce a gigice, sai kuma tayi saurin canja zancen da taga suna kallonta da rashin fahimta "kuna da alaƙa da Kamal?"

Hamdi bata da amsar bayarwa don Kamal ɗin ma bata taɓa gani ba. Sunansa kawai ta sani. Ta kalli Sajida tana jiran tayi bayani sai jin baƙuwar murya tayi tana yiwa Zee magana.

"Abba Habibu ya shigo kuwa Zee? Taj ke tambayar...."

Kasa ƙarasa magana yayi. Ya tsaya kallon Hamdi ba shiri da irin mamakin da ta gama na ganin Anisa. Ya kalleta, ya kalli Sajida da Zee sannan ya yi magana.

"Ke ce Hamdi?"

Murmushi tayi da kunyar tuna abubuwan da tayi a gabansu wannan ranar.

"Ina wuni?"

"Ba zan amsa ba don naga alama da gangan ki ka dinga wasan ɓuya don kada mu haɗu." Ya kalli saman stage inda Taj ya juya musu baya yana magana "bari Happy ya gama speech ya zo ya ga mai kukan bolt."

Ba don hayaniya ba da sai kowa yaji sautin wucewar wani abu kamar dutse da ya tokarewa Anisa wuya tun É—azu. Maganganun Kamal sun tsefe mata zargin da zuciya ta fara kitsa mata. Ba kunya ta saki fuska tana dariya harda cewa,

"Ai kuwa na san zai yi mamaki."

Kamal kuma ya dubi Sajida bayan ya gabatar musu da Salwa a matsayin ɗaya daga cikin ƙannensa.

"Na jima ina son tuna inda na taɓa ganin mai kama daku na kasa. Da yake ban ma riƙe sunanta ba lokacin haɗuwarmu a Abuja shi yasa ban taɓa alaƙanta ku ba."

"Ikon Allah kenan. Muma fa ta bamu labarin haÉ—uwar taku." Sajida ta faÉ—i tana kallon yadda duk wani haske na fuskar Hamdi ya É—auke kamar an É—auke wuta.

Taɓota tayi sai tayi firgigit ta dubi Kamal ta sake kallon saman stage inda Taj yake tsaye. Dutsen da ya bar ƙirjin Anisa ashe nata ya koma. Ya haɗe mata da wani irin ɗaci na tsagwaron disappointment. Kallon mutumin da ta kasa cirewa daga ranta har rana irin ta yau a matsayin Happy Taj kawai take yi. Ubangidan Abbanta wanda take baƙincikin shigowarsa cikin rayuwarsu da ƙara ingiza mata uba ya cigaba da girki. Daina jindaɗin komai tayi a wajen sai tsananin son ta ganta ƙudundune akan katifarta a ƙuryar ɗaki. Ƙafafunta su ka koma tamkar leda don ji tayi kamar ba za su ɗauketa ba.

"Hamdi lafiya kuwa?"

Anisa ce tayi tambayar ganin ta dafe kai gami da runtse idanu.

Ƙaryar da ta fara zuwa kanta tayi musu.
"Jiri nake ji. Haka kawai kaina ya soma ciwo."

Da tausayawa Kamal ya kalleta "muje in sama miki inda za ki huta ba tare da hayaniya ba."

"Gida zan tafi" ta faÉ—i tana mai danne kukan da taji ya taso mata. Abin takaici bata ma sani ba kukan na mene ne yake barazanar kunyata ta a gaban mutane.

"Yanzu wajen nan fita ma aiki ne. Ki huta É—in dai zai fi. Maybe kema ba mai son taro da hayaniya bace kamar Happy."

Kwatanta ta da Happy ɗinnan ƙara mata ciwo ya yi a zuci. Kamal ya ce su Zee su zauna zai je ya dawo. Sajida ta so bin su ya nuna gara ta zauna da ƙannenta. Zai nemi mai zama da Hamdi har taji sauƙi ta fito.

Suna tafiya Salwa ta gallawa Anisa harara irin wadda ake cewa aikin banza harara a duhu domin babu wanda ya kula. Sai ta ja tsaki da ƙarfi sannan ta bar wajen. Babu abin da bata sani ba game da Anisa a cikin gidan Ahmad. Hirar su ka yi da su Taj a waya a gaban Zahra. Ita kuma saboda yadda take ganin Salwa taƙi haƙura dashi shi ne ta faɗa mata anyi masa mata a gidan Amma.

Su Zahra da sauran Æ´an gidansu Taj ta tafi nema. Ita ma Anisa ta tafi wajen su Anti. Zee da su Sajida ma su ka koma daga gaba inda za su ji kalmomin godiya da Taj yake yiwa duk wanda ya zo.

*

Ta wata ƙofar baya Kamal ya buɗewa Hamdi ainihin ginin Happy Taj. Wani ni'imtaccen sanyi da ƙamshi mai kwantar da hankali ya baƙunceta. Mantawa tayi da ciwon kai ta zuba ido tana kallon yadda aka ƙawata wajen kamar ba a Kano ba. Kodayake dama bata taɓa zuwa wajen da ya kama ƙafar wannan a kyau da tsari ba.

Sama ya su ka hau. A nan taga banda jerin tebura da kujerun masu cin abinci akwai ƙofofi a rufe. Ƙofa ɗaya ya buɗe mata ya tsaya daga gefe.

"Akwai ruwa da juice a fridge. Ga key sai ki rufe ta ciki. Idan kin ji ƙarfi za ki iya fitowa kawai ki ƙulle." Kujera ya nuna mata ta cushion mai irin ɗuma-ɗuman nan a can gefe da pillow na alfarma "ki kwanta a can. Ko kina so zan turo wata cikin ma'aikatanmu ta taya ki zama?"

"A'a nagode" ta sake kallon wajen "ni da ka barni na tafi gida ma."

"Not an option. Kina fita ƴan uwanki za su bi ki. Kinga kin shiga haƙƙinsu ko?"

Murmushi yayi ita ma ta mayar masa. Bata ga alamun samun nasara a tare da shi ba. Yana tafiya ta ƙulle ƙofar ta zare muƙullin tana juya shi a yatsanta ta haye kujerar ta kwanta. A gaban kujerar akwai two seater da one seater ɗinta a gefen hagu da dama. Tsakiya teburin gilas ne wato center table akan lallausan kafet sai TV da tarkacen kallo a kan wata irin tv stand ta alfarma mai kallo ƙofa. Ɓangaren lungu ya shige ta yadda ba a ganin mene ne akan kujerar sai an zagayo gabanta.

Da yake a office É—in ba a jin hayaniya sosai shiyasa wajen ya yi mata shiru. Tunanin yadda aka yi mutumin da ta gani a makarantarsu ya zama Taj É—in da ya karaÉ—e bakunan Æ´an gidansu ta fara. Sai dai bai je ko'ina ba bacci ya yi awon gaba da ita saboda daÉ—in waje. Gajiyar jiya da yau da su ka kusa kwana yin meatpie da samosa ce ta dirar mata gadan-gadan.

*

Taro ya yi taro. Iyaye da yara, matasa da dattijai kowa ka gani nishaɗi da farinciki kawai yake yi in banda Salwa. Tunda ta ga Anisa taji komai ya rikice mata. Yarinyar bata da makusa ko kaɗan. Daɗinta ɗaya shine gani da tayi ta fita haske nesa ba kusa ba. Anisa black beauty ce. Idanu dara dara da hanci mai tsini. Sai ɗan bakinta madaidaici. Ita kuwa irin fararen nan ne da mazan Kano a wancan lokacin su ke fatan samu ko da mayya ce. Maminsu tana da haske bakin gwargwado. Amma mahaifinsu bafullatani ne fari tas daga garin Dambam. Ƴaƴansa duka babu baƙi. Ga kwantaccen gashi da kyawun fuska. Ɗan murmushi tayi. Babu yadda za ayi Taj ya tsallaketa ya so wata Anisa. Da wannan yaƙinin ta saki ranta aka cigaba da sha'ani cikin walwala.

Kamal ɓangaren boutique ɗinsa ya nufa inda ake ta ruwan ciniki. Shi da yaran shagon babu wanda ya sami kansa balle ayi batun nutsuwa. Tuni ya manta da Hamdi da ya kai office ɗin Taj.

Ana kiran la'asar mutane su ka fara gangarawa kyakkyawan masallacin dake kusa da garden É—in wurin. Wani hafizin matashi Taj ya samu zai dinga limanci a wajen. Saboda haka ko babu niyar siyayya sawu ba zai É—auke ba ga Æ´an unguwa da su ka sami masallaci mai kyau irin wannan.

Yana jin kiran sallar ya so tafiya yin alwala amma abu ya gagara. Kitchen É—in nasu ya rikice da aiki duk da sun gama tanadin abinci kafin a fara zuwa. Ba shi ya sami kansa ba sai biyar saura.

"Subhanallah" ya furta hankalinsa na tashi "Abba ku ƙarasa zan je nayi sallah." Ya ce da Abba Habibu da ya naɗa Sous Chef, wato mataimakinsa.

Masallaci ya yi niyyar tafiya sai yayi tunanin mutane za su tare shi. Musamman ƴan uwansa da su ke ta son ayi hoto. Ciki ya koma. Ya hau sama da bibbiyu. Nan ma a cike yake da mutane. Ɗakunan taronsu ne kaɗai a rufe. Ƙofar office ɗinsa wanda Hamdi bata kula da label ɗinsa ba da za su shiga an rubuta EXECUTIVE CHEF.
Chapter 30 · 0% Book details