Sashe 33
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Meye ma bai faru ba? Ya faÉ—a min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta É—an daudu ne. A ranar na soke maganar. Shi ne ya haÉ—a kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona. Suna ta É“oye É“oye basu san na sani ba. Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen É—aurin auren. Sai yayansa ya shiga maganar" ya nuna babban É—ansa "shi yasa na zo yau. In kun je an É—aura za ku ga abin da zai faru. Zuriata tafi Æ™arfin haÉ—a jini da irinku. Æata gari, lalatattun mutane"
Banda Innalillahi babu abinda Abba ke faɗi. Ƴar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku.
Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da baƙincikin anyi asarar namiji. Haƙuri Abba ya fara bashi ya dakatar da shi. Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu. Ba su yi aune ba Abba ya dire gwiwoyinsa a ƙasa zai fara roƙo mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki.
"Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan."
Da sauri Taj ya kama hannunsa zai ɗaga shi amma yaƙi miƙewa.
"Abba don Allah ka tashi."
"Idan auren nan bai yiwu ba gabaɗaya gidana laifina za su gani. Sajida bata taɓa saurayi ba sai akan shi. Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai. Duniya za ta zage ni. Duniya za ta min dariya.."
Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa "Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha Allahu gobe za ka aurar da Æ´a."
"Taj?" Kamal ya kira shi gabansa na faÉ—uwa.
"Ina son ta Abba. Saboda ita na zo gareka."
Abba Habibu rasa bakin magana ya yi. Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu bai sani ba.
RAYUWA DA GIÆI 16
Batul Mamman 💖
_Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ƴaƴanmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran ƴaƴan bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ƙararsu, kada su kai ƙarar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ƙasarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu roƙi kowa. Ka buɗa mana. Ka albarkaci nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sauƙi da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka. Amin_
***
Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.
"A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."
Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da ɗanyen aikin da Taj ya ɓallo.
"Abba..."
Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.
"Kada ka damu Kamal. Ba zan taɓa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ƙara nesanta uba da ɗansa ba."
Daga Taj har Kamal ba ƙaramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,
"Abba, Alhaji ya daÉ—e da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..."
Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai ƙara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba."
Abba jinjina zumuncin Æ´an uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faÉ—a musu.
"Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko shaƙiƙan da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida haƙuri. Na san za ta yi min uzuri."
"Sai dai idan ni ne baka son bawa Æ´arka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta."
"Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaÉ—an.
"Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode"
Abba zai shige gida Ƴar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.
"Simagade....au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ƙasa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta ɗorawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka."
"A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ƙiyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min."
Ƙofar gidansa ya ƙarasa da sauri don ƙirjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faɗi a wurin. Ƴar Ficika aka sake samun abin yi. Ya ɗora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.
"Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."
"To, to" ya amsa kamar ba É—an cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruÉ—ewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.
Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haÉ—a da É—anyen kai kamar wani É—an ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences.
Horn ɗin mota yaji daidai ƙofar gidan. Ya leƙa Taj ya fito a lokacin.
"Mu kai shi asibiti."
"Ai ka bari a faÉ—awa Yaya ko?"
Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaÉ—a kai. Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron.
"Damuwa ce Yaya. Kada ki ɗaga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti." Ɗaga shi su ka yi Kamal ya ƙarasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.
"Ƴar Ficika kuma ya ce..."
Taj ya gallawa Ƴar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.
"Wallahi ban faÉ—a mata komai ba."
"Me ku ke ɓoye min?" Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai ɗaga masa hankali ya faɗi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.
Gani su ka zasu ɓata lokaci sai kawai Taj ya ce Ƴar Ficika ya faɗa mata in sun tafi.
"Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne kawai zai tashi."
"To, nagode. Idan kun je asibiti ka faɗa min. Sai na kira ƙaninsa ya taho."
Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ƙololuwar tashi. Tana dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan.
*
Asibitin kuɗi Kamal ya kai su amma ba wanda ƴan gidansu su kw zuwa ba. Ana buƙatar file Taj ya buɗe musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci.
Zaman jiran Abdulƙadir ƙaninsa Taj da Kamal su ka yi a ɗakin. Kamal ya dube shi a tsanake.
"Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ƙaryar sonta kake kawai don kafi kowa iya rigima."
"Allah da gaske nake ina sonta Happiness."
"Kai É—in? Ya aka yi ban sani ba?" Ya tambaya don bai gaskata shi ba.
Babu wani juya zance ya ce "Saboda nayi tunanin za ka ƙaryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta."
"Lallai ka iya ganganci. Banda ɓoye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?"
Taj ya yi murmushi "wallahi a next flight za ku ganni."
"Da ni na ce ina sonta fa?" Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na É—an uwansa.
"In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu É—aya wanda mutum É—aya ya kamata ya so ba." Ya haÉ—e kafaÉ—unsa don tsigar jikinsa tashi tayi.
"Next time kada ka ɓoye min abin da ya kamata na sani."
Gira Taj ya É—aga yana Æ´ar dariya ganin Kamal ya É—auki zafi da gsske.
"Bros, faÉ—a min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina."
Fuska Kamal ya É—aure amma da gani ya sauko "Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?"
"Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai."
"Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?"
Taj ya gyaÉ—a kai yana dariya.
"Banda ƙuruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?"
"Inda ake kai matan..."
"Ehemm. Ughhh" Abba ya yi gyaran murya da ƙarfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa wurin da bai kamata kunnuwan uba su ji ba.
Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sauƙi kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ƙara yi musu godiya sannan ya roƙesu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa.