← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 96

Sashe 57

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinta har yafi na Mubina rawa Yaya Kubra ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Doctor kun taɓa shawarta yi masa transplant?"

"A nan matsalar take. Ya ce min shi kaɗai ne mai rhesus negative blood group a gidan. Dalilin da yasa yaƙi sanar da kowa kenan."

"Wannan ai ba dalili bane. Ya ma aka yi shi kaÉ—ai yake da negative? Wane blood group ne?"

Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba. Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection. Bata zata abin ya kai haka ba. Kamal, Happiness ɗinsu da ciwon ƙoda wadda take gab da daina aiki gabaɗaya.

Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta ƙarewa masoyinta, shi yayarsa take yi.

Abin da yake faruwa babba ne. Ƙoda ba abar sayarwa bace. Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba. Duk da tana da yaƙinin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba'in a shirye da su bayar ba. A ina za su sami ƙoda? A dangi?...abin da kamar wuya. Sannan zancen cigiya ma bai taso ba. Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka kuɗi ya sayi wani ɓangare na jiki ba. Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs ɗinsu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa daɗi da za su iya biyo baya.

"Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor."

A gigice Yaya Kubra ta ce "ta ina hankalina zai kwanta? Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne. A ina ya sami negative don Allah?"

Bayanin wannan ruɗani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa. Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani. Group ɗin jini daban kamar yadda ta sani guda huɗu. A, B, AB da O. Sannan yana ɗauke da wani sinadari da ake kira rhesus. Idan akwai sai wannan blood group ɗin ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-). Abin mamakin shi ne da group ɗin jinin da rhesus ɗin duka a wajen iyaye ake gada. Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi ɗa O+. Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa. Wannan shi ne normal. To a case ɗin Kamal an wayi gari shi kaɗai ne yake ɗauke da jini rhesus negative. Wannan yana nufin ɗaya daga cikin iyayensa yana ɗauke da alamun rhesus negative ɗin a ɓoye. Tunda kowanne abu na jikin ɗan Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi ƙarfi ya nuna kansa (domimant gene). Ɗayan kuma ya zama a ɓoye (recessive gene). To wannan ɓoyayyen zai iya bayyana a jikin ƴaƴan da za su haifa a matsayin mai ƙarfi. A taƙaice dai ɗaya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna ɗauke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace. Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi. Idan yaci ƙaro da ƙa'idar likitanci don Allah ayi min uzuri. Littafin fiction ne dama.)

"Allah Sarki Kamal. Nagode Doctor. In sha Allah zan yi cigiya a family ɗin Hajiya. Don da ace daga ɓangaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi kaɗai ne mai wannan blood group ɗin ba."

"Cigiya kuma? Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita. Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi ƙoda?"

"Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi? Me yasa ki ka faÉ—a min in ba don haka ba?"

"Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba. Cigiya zata iya zama laifi a shari'ance. Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi."

Duk ta inda Yaya Kubra ta ɓullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan. Iyayensa ya kamata su sani. Shi kuma Kamal yaƙi amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi. Ga ciwo, ga kuɗi amma babu mai iya taimakawa. Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa.

"Da na sani Taj na faÉ—awa." Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu. Yadda zai sami lafiya kawai take nema.

"Rufa mana asiri. Gara kowa yaji akan Taj. Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya. Those two are like one soul in two bodies."

Da ƙyar Mubina ta sami kan Yaya Kubra. Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent ɗinsa. Daga nan sai su san abin yi kuma.

***

Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh. Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi. Ta zauna ta kalallame shi da ƙarya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj.

"Mu ne da alhakin sama mata farincikinta. Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata."

"Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in roƙi ya sa ɗansa auren ƴata? Da hankalina fa."

ÆŠaure fuska tayi "to sai ka barta ciwon so ya kasheta ai."

"Ki gaggauta kiranta ta dawo gida kafin ranta ya ɓaci wallahi." Har wani haki yake don ɓacin rai. Rainin hankalin Mami ya yi yawa.

Juyawa ya yi zai fita tayi saurin jefa layarta ta biyan buƙata a baki ta tauna. Kamar an tsayar da ƙafafunsa ya tsaya cak.

"Nace ka kira Alh. Hayatu ka san yadda za ka yi dashi ya amince a aurawa É—ansa Taj Salwa." Ta faÉ—i da izza.

"To. Yanzu ko yaushe?"

"Zauna ka kira yanzu."

Zaman ya yi ya ɗauko waya. Ta miƙa masa wayarta mai ɗauke da numbar Alh. Hayatu ya kwafa ya yi dialing.

"Assalamu alaikum"

Ta jiyo muryar tsohon masoyinta abin begenta har yau. Sake tauna layar tayi ta zarewa Alh. Mukhtar idanu. Jiki na rawa ya amsa sallamar tare da gabatar da kansa.
RAYUWA DA GIƁI 24

Batul Mamman💖

Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ƙaro bata jimawa za ta yi waje ita ma.

Zama ya gyara da ya tuna yadda ya ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ƴar ta ɗorata akan hanya mara ɓullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu'ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya laƙaba masa suna.

Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataɓus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. Ɗansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin ɗan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ƙarfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass.

Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keɓe dashi yana tambayarsa alaƙar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke.

Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad.
"Alhaji wata maganar ka ji?"

"Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?"

Da sauri ya bashi haƙuri tare da amsa tambayar da ya yi masa.
"Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faÉ—a su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buÉ—ewa."

"Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?" Alhaji ya faÉ—i da irin rashin damuwar nan.

Ahmad baya jindaÉ—in yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan Æ´an uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu.

"Sunansa kenan."

"Ya kirani yana roƙon na amince Taj ya aureta."

Maganar ta dake shi sosai "Roƙo kuma Alhaji?"

"Roƙo mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?"

"Zan yi mata magana Alhaji." Ya girgiza kai "Gobe in sha Allah zan mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can." Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo.

"Babu daɗi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faɗa masa na amince. Saƙon da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata ɗaya indai da gaske su ke."
Chapter 57 · 0% Book details