← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 96

Sashe 11

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Da kaɗan da kaɗan zance ya zaga zuri'ar gidan kowa ya san me yake faruwa. Wasu na goyon bayan Taj wasu na ganin laifinsa. Inna da Mama sun fi kowa shiga tashin hankali. Sai Kamal da ya kwanta ciwo sosai. Alhaji kuwa tunda Amma tace za ta ɗauke shi ya san sai abin da Allah Yayi. Bai fasa ganin laifin Mama ba akan zama mutum ta farko wajen haɗa shi da ƴan uwansa da kuma raba shi da ɗansa. Irin abubuwan da ya dinga yi mata sai da ya kaita ga yin yaji. Tana ficewa kuwa Inna ma ta kama gabanta. Butulci ne zai sa ta cigaba da miƙe ƙafa a gidan da mai son ɗanta ta kasa zama. Hajiya da Umma da basu tafi ba ba daɗinsu Alhaji yake ji ba. Abu sai da ya kai anyi zama na musamman da dangin kowannensu. An sasanta dai amma tunda Taj ya bar gidan kaso mai yawa na walwalar gidan ya kau.

***

Tafiya Amerika yana buƙatar visa da dogon cike ciken takardu wanda Amma take ganin ɓacin lokaci ne. Saboda haka ta nemi visar India da passport ɗinta na ƴar ƙasa na Amerika. Nan da nan ta samu. Cikin sati biyu suka bar ƙasar. Dama Abuja ta koma dashi. Ita ta kai shi makaranta ta jira komai ya kammala bisa tsari. Zai cigaba da aikinsa a wurin Paaji a duk ranar da bashi da lecture kamar yadda ya yi lokacin degree ɗinsa na farko.

Da za ta tafi ta kawo kuÉ—i ta bashi.
"Kada ka kunyata ni. Kada kuma kayi abin da zai ƙara girmama rigimar Yaya Hayatu da Yaya Babba. Ka kiyayi duk wani abu da Allah baya so. Shi kuma ba zai bari ka taɓe ba."

Rufe ido ya yi yana kuka. Ta dungure masa kai "meye haka? Da Yaya Hayatu zai ga wannan kukan ai cewa zai yi abin da yake gudu ya faru."

Dariyar dole Taj ya yi. Ta rungume shi tana rarrashi. Duk da yaji bambarakwai amma sai hakan ya sanyaya masa zuciya.

"Bana son ragwanta. In shagwaɓa ce dai I will indulge you amma ragon namiji baya burgeni kaji ko?"

Murmushi yayi. A rayuwarsa zai iya ƙirga sau nawa ya haɗu da Amma. Ya san tana da kirki amma bai san halayenta irin waɗanda yake gani yanzu ba. Uwa da uba ya samu a dunkule a tare da ita. Ta ƙarfafa masa gwiwa sosai sannan ta faɗa masa zata yi ƙoƙari kafin lokacin hutu tayi duk abin da ya dace domin ya sami visa.

Wannan shi ne mafarin zaman Taj a Amerika. Ƴaƴan Amma sun yi aure. Su suna Minnesota babbar Anisa kuma tana aure a Florida. Iman kuma a Lagos take zaune da mijinta. Yayinda maigidan yake yawo tsakanin Nigeria wurin amaryar da ya yi bayan ya yi ritaya da Amerika.

Sai ya kasance bayan Taj ya gama karatu shi da ita ne a gidan kodayaushe. Sun shaƙu matuƙa. Tana aikinta shima yana yi awani restaurant da ya yi fice a abincin Asia da Afrika. A wurin ma'aikatan wurin ya koyo nau'ikan abincin gargajiya na Nigeria na ƙabilu daban daban. Cikin ɗan lokaci ya yi suna sosai. Takanas aka zo aka gayyace shi gasar da ta ciwo masa wasu maƙudan kuɗaɗe bayan ya sami nasarar yin na biyu. Da kuɗin da kuma tanadinsa tun na India yake son buɗe mall a Kano.

Rashin zuwansa gida bai hana shi mu'amala da ƴan uwansa da iyaye ba. Musamman yanzu da aka sami cigaban hanyoyin sadarwa. Suna yawan bidiyo call ana ganin juna musamman yayin aure da haihuwa. Alhaji ne kaɗai baya ɗaukar wayarsa har yanzu. Amma ta tilasta masa tura masa saƙon gaisuwa kullum rana ta Allah na kar ta kwana. Sai dai da yake zuciya bata da ƙashi, ya riƙe uban a zuciyarsa. Ya ɗora masa alhakin raba shi da ahalinsa. Da nesanta fuskarsa da ta mahaifiyarsa. Shi yasa ya ƙudurcewa ransa ba zai sake taka gidansu ba sai Alhaji ya neme shi da kansa.

***

Hutu ya ƙare lafiya. Ranar da ƴan makarantar kwana za su koma Hamdi bata samu ta runtsa ba. Tana fama da tararrabin yadda Ummi za ta kwance mata zani a kasuwa. Duk siyayyar da Abbanta ya yi mata babu abin da ya burgeta. Rashin fara'arta ya dami Yaya har sai da ta kai ga yi mata magana kafin Abba ya kaita tasha.

"Sai da aski ya zo gaban goshi nake ganin alamun rashin son komawa a tare dake Hamdi."

Zee ma ta ce "Ya Hamdi ko kukan bodin za ki fara a term ɗin ƙarshe? In faɗawa Abba a dawo dake makarantarmu?"

Duka Hamdi ta kai mata da wasa a ƙoƙarinta na danne damuwarta. Bayan fitar Zee daga falon Yaya ta muskuta kusa da ita.

"Hamdiyya."

"Na'am" ta amsa a raunane.

"Na san baki so zuwan iyalin Maje gidan nan ba tunda aka zo da Ummi."

A zabure ta kalli Yayan da tsananin mamaki. Ita kuwa tayi murmushi.

"Kina mamakin yadda aka yi na sani?"

Ta gyaÉ—a kai.

"Kin guji gida saboda kada a san waye mahaifinki. Yanzu kuma gashi an zo an ganshi har gidan kina tsoron kada asirinki ya tonu."

"Yaya..." ta soma faÉ—i cike da kunya.

"Ki koyi son abin da Allah Ya baki sai Ya ninka miki da wanda baki zata ba."

Yawu ta haÉ—iya "to."

Yaya ta cigaba da cewa "Ban taɓa nadamar auren mahaifinku ba saboda bai bani wannan dalilin ba. Irin kulawar da muke samu daga gare shi wasu masu kuɗin sai sun yi kishi da mu. Zaman lafiya yafi zama ɗan sarki. Hamdi sandar hannunka da ita kake duka kin ji. Hangen ta hannun wani ba naki bane don baki sani ba ko duk ƙaya ce ko bata ma da ƙwari."

Numfashi ta sauke ta sadda kai ƙasa ta bawa Yaya haƙuri. Ita kuwa da yake ba mace bace mai riƙo ko son ayi ta nanata zance sai cewa tayi a bar maganar.

To a haka Abba ya dawo shabiyun rana ya sanar dasu Baba Maje na nan tafe zai kai su makaranta tare da Ummi. Ya ƙare da faɗin,

"Tare zamu tafi."

Albarkacin Yaya dake zaune a wurin da nasihar da tayi mata É—azu ne kawai ya hanata fasa ihu. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji daÉ—i. Addu'a kawai ta kama yi Allah Ya kawo sanadin da zai fasa binsu don gudun kada ya dinga sakin baki a gaban Ummi.

Addu'arta ta ƙarbu domin an fara zuba kayanta a motar Baba Maje sai ga wani dattijo yana sallama da Abba. Kana ganinsa baka buƙatar ƙarin bayani za ka gane ba mutumin kirki bane. Shadda ce yellow shar a jikinsa tana uban ƙyalli ga hula ya harbo gaban goshi irin na tsofaffin ƴan duniya. Taunar cingam yake cakakal-cakakal yana karkaɗa muƙullin mota. Ga wata uwar yatsina yana faman yi a yayinda idanunsa ke ƙarewa layin gidan kallo.

"Maje anya ba za ku tafi ba kuwa? Ban san me ya kawo shi ba amma ina jin ba abu bane da zamu ƙare da wuri."

"Ba dai abokin sana'arka bane ko?" Baba Maje ya tambaya don yanayin mutumin babu sha'awar son kusanci da shi.

"Agent É—in wanda nake hayar gidan abincina ne."

"To ko dai mu jira?" Baba Maje ya sake cewa da Æ´ar damuwar yadda yaga abokin nasa kamar baya cikin nutsuwa.

"A'a, ku tafi kawai."

Godiya ya yi masa akan biyowa É—aukar Hamdi sannan ya juya wajen mutumin su kuma su ka shiga mota.

Akan hanyarsu Baba Maje yayi ta ƙoƙarin haɗa hira tsakanin Ummi da Hamdi. Da yake Ummi akwai wayo sai ta fishi jan Hamdin a jiki. Ya kuwa ji daɗin hakan sosai.

Abba da baƙonsa kuwa ba komai su ka tattauna ba illa ƙarin kuɗin haya da aka yiwa gidan abincin nasa. Kuɗin ya yi biyun abin da yake biya. Ya fara roƙon alfarma mutumin ya ce sai dai ya tashi. Dama kuma ya samo mai biyan wannan farashin ne. Ya kuma san babu yadda za ayi Abba ya biya. Shi ne ya zo masa da dabara.

"Idan na tashi yaya zan yi da iyalina? Don Allah ka rage min wani abu."

"Sati biyu zan iya baka ka tattare komatsanka ka tashi. Idan kuma kuÉ—in sun samu kafin nan sai ka kawo a sabunta kwantiragi."

Yana gama faɗin haka ya shige motarsa ya tada ƙura ya bar unguwar. Abba ya koma gida da sanyin jiki ya labartawa Yaya halin da ake ciki.

***

"Ki fara kai min nawa kayan ɗaki don akwai abin da nake buƙata yanzu a ciki."

Ko minti biyar Baba Maje bai yi da barinsu da kayansu da za su kwashe su kai hostel ba Ummi ta rikiÉ—a ta koma annobar Æ´an FGC.

Wani irin kallon mamaki Hamdi ta bita da shi "ban gane ba."

"Au...kin daina jin hausa ne saboda mun shigo school? To jirani a nan. Zan aiko miki da yaren da za ki fahimta." Da tafiyarta ta ƙasaita ta wuce ta bar Hamdi a tsaye.

Ita kuma ganin ta tafi ta fara ɗaukar kayanta ta nufi hostel ɗinsu. Tana ajiyewa ta koma da sauri domin ɗebo sauran sakamakon garin da hadari saboda damina da ta tsaya sosai. Da isarta ta iske wata yarinya da ta tabbatar cikin ƴan koran Ummi take. Wata tsadaddiyar waya ta fito da ita daga ƙasan hijab ta yafito Hamdi da hannu. Da taga bata matso ba kawai sai ta danna wayar. Nan da nan wurin ya karaɗe da muryar Abba inda yake cewa (Altine kece haka? Ikon Allah) da muryar nan tasa da ko ita ƴarsa bata so.

Hankalinta ya yi masifar tashi. A take ta jiƙe da wani irin gumi. Ta miƙa hannu a firgice za ta karɓe wayar sai yarinyar ta ja da baya.

"Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani"

"To" ta amsa da sauri tare da duƙawa ta fara ɗaukar kayan.

Yarinyar ta yatsina fuska "no, ta ce da É—ai-É—ai za ki É—auka."

"To" Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki.

Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku. Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel ɗin su Ummi. Bata ganta ba sai da ta kai ledar ƙarshe ta sameta zaune akan gadonta.
Chapter 11 · 0% Book details