← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 96

Sashe 39

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala. Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai. Tana can ɗakin Halifa ta rufe ƙofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani. Dukan ne goma da ɗari ba ma ashirin ba. Ita ta sani sarai cewa haɗuwar farko ta kamu da son Taj. Irin son nan mai shigar farat ɗaya. A haɗuwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take. Sai gashi haɗuwa ta uku da ya dace su yi musayar zuƙata ya zo ba a yadda take so ba. Tarin ƙaunar da take masa take ta bi iska saboda sana'arsa. Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana'ar da tafi tsana. Me namiji zai yi da girki don Allah? Ita mace da tun ƙuruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa. Komai manya za su ce game da aure da maganar ɗa'ami suke farawa ko su ƙare. Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya...sannan uwa uba girki. Shi fa girkin nan sai an ƙara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa. Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa. Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam. Ya riga ya ƙwace abin tinƙahon da taƙamar. To ita me za ta yi? Shara da wanke-wanke?

Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima. Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi.

"Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba." Ta faÉ—awa zuciyarta.

Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta. Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane. Salin alin za su rabu. Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba. Duniya ma sai tayi mata dariya. Abin da tafi gudu da ƙi ace shi ne a tare da ita muddin rai? Inaaaa!

Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida. Ana ta taron yinin Sajida. Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su faɗi lokacin da su ke so su tare. A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita kaɗai. Sai ta kalli Zee ɗin. Idanunta luhu luhu sun kumbura. Tayi zuru zuru ba a buƙatar likita wurin gane bata da lafiya. Tausayin ƙanwar ya kama ta. Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah. Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba.

Da su ka shiga É—aki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce "Allah Sarki Zee. Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki. Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane."

Zee ta sake fashewa da kuka "kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko? Yaya zan yi?"

"Ki kwantar da hankalinki. Bawa bai isa ya ƙetare ƙaddararsa ba. Wani ba ya auren matar wani. Yanayin yadda aka yi auren kaɗai ya ishe ki ishara."

Kasaƙe Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana.

"Ke baki da matsala kenan da auren? Kodayake me zai sa ki ƙi Taj? Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school ɗinku ba da na haƙura." Wayarta ta miƙawa Hamdi "kin gani. Tun ɗazu yake ta turo min message."

Saƙonnin har guda shida duk abu guda biyu su ke ɗauke da shi. Na farko haƙuri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta. Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu. Sonta yake. Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma.

Murmushi sosai Hamdi tayi. Bata taɓa sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu. Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta. Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa. Ai dole ma ta rabu da Taj. Ko don rashin irin wannan text ɗin na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida ɗazu yana ƙara bata haƙurin abin da ya faru.

"Allah Zee kada ki tada hankali da yawa. Na san irin auren nan babu daÉ—i. Amma ki godewa Allah da mai sonki aka haÉ—aki. Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna. Yawan kukan zai sa su ji babu daÉ—i."

Sajida ce ta shiga ɗakin a lokacin. Ta kalli ƙannen nata tana murmushi.

"Su Hamdi malaman aure. Irin wannan huÉ—uba haka? Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?"

Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi. Wannan aure ba da ita ba. Ba dai za ta iya labartawa Æ´an uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu.

"Gani nayi an riga an ɗaura. Gara mu haƙura kawai. Kukan ciwo zai sa mata."

"Da gaskiyarki. Amma ni ke ce damuwata. Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu. Yau kuma an ɗaura naga kin yi saurin haƙura kamar ba ke ce ki ka suma ba ɗazu... Don Allah mene ne tsakaninki da shi?"

Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata. Tana son gilla musu ƙarya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa. Allah ne Ya taimaketa ƴan matan danginsu su ka shigo ɗakin ana tsokanar amare. A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu ƙawayen kurkusa da su ke shawara dasu. Su ne dai ƙawayen juna sai cousins ɗinsu.

Gabanin Magriba da baƙi su ka sarara ne Hamdi ta shige ƙuryar ɗakinta da wayar Sajida da tata a hannu. Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu'o'in neman nasara ta kira shi.

***

"Happy kana ganin ka kyauta kuwa? Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce."

Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je ɗaukan Abba su je wurin Alhaji. Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau. Rigar tasa kaɗan ya rage ta ƙarasa gwiwa. Hannunta kuma ya ɗan zarce gwiwar hannu kaɗan. Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane. Hula ya ɗora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba. Ya yi kyau sosai. Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal.

"Ya kake so nayi da ita? Me ma nayi mata? Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text É—in da take yawan yi min ba zan kula ba."

"Na sani. Amma yanzu da ta shige É—aki tun É—azu ya dace ka kirata ka É—an rarrasheta."

Taj ya ware idanu "in yi me? So ka ke tayi zaton aurenta zan yi? Gaskiya Happiness ka rage sauƙin kai. Zai iya kai ka ya baro."

"To ko Yayan ka ɗan yiwa magana mana. Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane. Please." Kamal ya ce da damuwa. Baya son rigima irin wannan ta cikin gida. Su duka ƙannen Ahmad ne. Amma ana iya samun dalilin da zai sa Ahmad ɗin ya zaɓi ɓangare guda ya ƙuntatawa ɗayan.

"Yanzu dai bani key mu je. In na dawo zan yi masa magana in sha Allah."

Da murmushi Kamal ya ce "ko kai fa." Sai kuma ya sako wani zancen "Goben dai za ka tafi Abuja?"

"In sha Allahu. In Amma ta tsine min tas za ta bini. Gara naje na daidaita da uwata."

"Ba ka yi fushi ba dai da na ce ba zani ba ko?" Kamal ya faɗi yana sosa ƙeya.

Ƙwafa Taj ya yi "Kaf ɗinku na san zaman da nake da ku. In matan suna da mazaje ai ku za ku iya zuwa. Amma har Naja da Rukky dake Abuja duk sun zame wai babu mai zuwa rakani."

"Naja fa ta ce za ta turo a É—aukoka daga airport."

"Wannan ma laifi zai zama a wajen Amma. Cewa za ta yi wato har na fara neman Æ´an uwana na barta."

"Allah Ya fito da kai lafiya. Daga nan zan taya ka addu'a. In kaje dai ka gaishe da Anisa." Yana dariya ya yi maganar.

Wata kwafar Taj yayi don ya san tsokanarsa yake. Shi ya tuƙa motar. Suna hanya yaji wayarsa tana ta ringing. Idan kiran ya katse a sake binsa da wani. Bai ɗauka ba sai da ya tsaya a danja kafin a bada hannu. Baƙuwar lamba ya gani. Kira har huɗu a jere dole ya bi.

Hamdi na ganin sunansa da hasken waya ko ringing bata fara ba ta É—auka.

"Assalam alaikum wa rahmatullah" ta faɗi da ladabin da ya bawa Taj mamaki. Shi da ya sa rai da tsiwa da rashin kunya. Har ya gama tanadin yadda zai ɓullo mata. Sai gashi tana yi masa gaisuwa irin wannan. Haka kawai zuciyarsa ta hana shi soma murna. Gara yaji da me ta zo. Hamdi ce fa. Wadda ta faɗa masa ƙiri ƙiri bata son sana'arsa.

Basarwa ya yi ya ce "Wa alaikum salam. Wa ke magana?"

"Ya Taj ni ce. Hamdi ce. Don Allah magana nake so mu yi" Ta wani ƙara sauke murya ita a dole mutuniyar kirki.

"Ina tuƙi yanzu. Idan na tsaya zan kira ki in sha Allah." Duk da idan ya so zai iya sanya earpod ɗinsa ya amsa wayar, jikinsa ya bashi dalilinta na nemansa. Shi yasa ya katse mata hanzari.

"To babu komai. Nagode. Nagode. Zan jira ka don Allah."

Jira ya yi ta kashe wayar kafin ya soma dariya. Ya labartawa Kamal rigimarsu ta ranar buÉ—e Happy Taj da kuma randa ya koma gidan.

"To dai mata sai da lallaɓawa. In kana son shawo kanta sai ka ajiye taka rigimar."

"Ashe ba za mu daidaita ba. Kallo É—aya nayi mata na gane rigimammiya ce. Tana yi min zan rama don gidan abin ta zo."

Da takaici Kamal ya kalle shi "Kai Happy. Matarka ce fa kuma yarinya ba abokiyar faÉ—a ba. Ko ina sai ka nuna hali ne?"

"Take takenta kamar cewa za ta yi na saketa. Haka jikina yake bani. Ni kuma wallahi sonta nake kamar babu sauran mata a duniya." Ya ƙare magana yana kanne ido.
Chapter 39 · 0% Book details