Sashe 24
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai bayan fiye da minti ɗaya sannan Abba ya ce ya shigo amma iyakarsa ƙofa. Ai kuwa da saurinsa ya shiga. Aikin daɗewar shekaru wato experience yafi aikin iyawa. Taj yaga abin mamaki a tattare da kuzarin dattijon. Ga tsafta don ko ledar maggi babu a ƙasa. Ƙamshi mai rura wutar yunwa ya cigaba da matse masa hanji.
Fried spaghetti ce yayi musu babu nama a ciki sai busasshen kifi. Ya juye a tray. Sajida ta kawo musu. Sannan ita da Yaya su ka koma falo. Samarin Alh. Hayatu su ka zauna suna zuba santi har su ka cinye.
Da za su tafi ne Taj ya bashi nambar wayarsu rubuce a takarda.
"Don Allah Abba kayi shawara."
"Naji. Ku tafi."
Faɗan nasa bai hana shi raka su har mota ba. Kuma yaƙi tafiya har su ka bar layin. Yana komawa gida ya samu Sajida tana naɗe tabarmar da su ka zauna. A ƙarƙashinta sai ga farar takarda. Ta miƙa masa ya buɗe. Roƙo da magiya ne daga Taj. Sai kuma ƙarin bayani game da restaurant ɗinsa.
"...idan ka amince za ka yi aiki dani, zan kama mana wuri inda za mu yi developing recipe kafin a gama ginin. Bana son yin business É—in da zai rushe kafin yaje ko ina. Ka taimaka min..
Happy Taj"
Da Yaya su ka zauna shawara. Sai dai washegari da kwanakin da su ka biyo baya kullum sai Taj yaje cin abinci. Har su ka yi masa kwano. Tun Abba yana basarwa har dai ya karɓi tayin da yayi masa. Ba kuma komai ya janyo haka ba sai rasa wurin da zai kafa sana'arsa. Duk inda yaje sai an biyo shi da ƙabali da ba'adi wanda shi ya san gaskiyar dai ita ce ɗan daudu ne. Ba sa ma damuwa da jin ko ya daina. A gida idan yace zai yi kuma akwai iyalinsa da ba zai so mutumcinsu ya zube ba.
Haka dai bayan kwanaki yana kai gauro da mari ya ce ya amince. Ya kuma duƙufa addu'ar neman taimakon Allah.
A lokacin kullum Hamdi tayi waya da gida sai anyi mata zancen Taj. Yaya da Æ´an uwanta sunansa a bakinsu raÉ—au. Ita kuwa lamarin bai burgeta ba. Wanda zai zo ya mayar da Abbanta cikin sana'ar girki ba masoyi bane.
Su Taj da su ka tabbatar sun sami kan Abba sai aka fara shirin zuwa wajen Anisa. Lokacin bai fi kwana goma ya rage masa ya koma ba. A motar Kamal su ka tafi. Da yake ya san gari basu wahala ba da bin kwatance ta google map su ka isa gidan.
***
Aikin snacks da Anti ta ce a tanada saboda zuwan su Taj, Hauwa aka bawa. Hajjo tuni ta fesa musu dalilin zuwan nasa. Anisa sai murna. Sai dai anyi rashin sa'a ana gobe ranar tafiya ta kama ta. A waya ta basu haƙuri ta ce amma akwai ɗalibarta da duk abubuwan da su ka zayyano za ta iya ba tare da sun ji bambancin taste ba.
"HaÉ—ani da ita" Anisa ta ce don in ba kayan Luciousbites ba, bata ganewa snacks É—in.
A waya aka gama komai. Hamdi murna da godiya ta dinga yiwa Hauwa. Ita kuma ta dinga roƙonta kada ta kunyata musu brand.
Ƙoƙari kam bakin gwargwado tayi. Meatpie, doughnut da samosa su ke so. Sai coconut infused youghurt. Shi ne kaɗai Hauwan ta aiko mata da shi. Sauran kuwa babu komai a ƙasa dole sai anyi. Bayan ta gama ta kira numbar Anisan da aka bata ta sanar da ita an gama komai.
"To ki bawa mai delivery. Zan turo address."
Nan fa ɗaya. Bata san kowa ba. Anti Labiba ma ta dinga kiran mutanenta amma kowa sai ya ce mai delivery baya kusa. Hamdi ta kuma kiran Anisa. Lokacin ita kuma bata jima da yin waya da Taj ba. Yana ƙara neman kwatance. A yadda ta ƙiyasta bai fi minti goma zai kawo su gidan ba. Gashi babu wanda za ta iya aika. Gari an tashi da rashin mai. Duk wata motar gidansu tana layi sai guda ɗaya ta Daddy.
"Hamdiyya ko za ki É—auko bolt ki kawo min. Zan biyaki kuÉ—in tranport É—in. Fitar ce babu halin yi yanzu."
Hamdi ta faÉ—awa Anti Labiba. Su ka rasa yadda za su yi. Mijin Anti Labiba a wajen gari yake aiki. Ita kuma babu mota. Tayi shahada kawai ta samarwa Hamdi bolt É—in.
RAYUWA DA GIÆI 13
Batul Mamman💖
Kada ku manta da bibiyar shafin Hauwa a instagram [email protected]_ ko nemeta a waya ta wannan layin domin
_09078075182_ odar snacks da nau'ikan youghurt masu daÉ—i.
***
Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haɗu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a ɓangarensu zancen ya sami karɓuwa.
ÆŠakin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal.
"Sai ga Haffiness É—in Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu."
"Har kin ƙara masa wasali a sunan nasa kenan." Taj ya faɗi yana zama akan kafet. Ƙafafunsa ya miƙe da yake jin sun sage saboda zama.
Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana
"Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?"
Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna ɓacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaɗan za a ɗora masa laifi.
Share su ya yi ya kira uwayensa ɗaya bayan ɗaya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan ɗan gyaran da za a ƙarasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo.
"Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness É—in nima ki É—an bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare."
A sukwane ta juyo rai a ɓace "banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?"
"To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba."
Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar.
"Buhun ubanka Tajo."
"Toohhh" Kamal ya kalleta da rashin jindaÉ—i. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba.
"Ɗan uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ƙanwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta."
Kai tsaye Tay ya tambayeta "Me su ka ce?"
Hajjo ta danƙara masa wani irin kallo "me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya."
Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga É—akin nan bai faÉ—i abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce,
"To ni dai gaskiya Hajjo..."
Yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faɗa mata baya son jikarta.
"Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron É—auko zancen aure yake."
"Saboda me? Yana da lalura ne?" Ta soma yi masa kallon ƙurilla.
Ya girgiza kai "a'a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji."
"Alhajin me?" Ta fara sababi "in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ƙud da ƙud. Duk taurin kansa bai isa na faɗa ya faɗa ba."
Kamal ya jinjina kai yana kallon Taj ko zai agaza masa. Shi kuwa shiru ya yi yana kallonsu.
"Nima ba nufina zai ƙi maganar bane. Kawai dai shi Taj yafi son lokacin da zai yi aure ya kasance Alhaji ya daina fushi da shi. Baya son yadda ya kore shi daga gidan kuma ya hana ƴaƴansa shiga su ma."
Hajjo ta jinjina lamarin "da gaskiyarsa kuma. To amma indai auren gida ne irin wannan ai ita Anisan ta san komai. Ga ku duka kuna ta zumuncinku. Su Haj. Gambo ma dai ko da satar hanya na san za su fito ganin jikokinsu."
"Ko kin san zuwan nan har bakin mota Taj ya bishi amma su ka ja mota aka baɗe shi da ƙura? Shi ne ya yi alƙawarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa."
Zancen ya fara shigarta. Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance. A ƙarshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba.
"Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana. Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen. Ba zai wulaƙanta min jika ba."
Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin. Ashe duk ɓaɓatun da yake ita wani angle ɗin daban take kallo. Miƙewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame.
Falo ya koma inda ya yi sa'a babu kowa. Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya.
"This woman is too smart Happy. Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan ɓullo don a kwantar da zancen nan."
Murmushi Taj ya yi "kaÉ—an ma ka gani. Shi yasa na so faÉ—a mata gaskiya. Kai kuma ka hana."
"Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa. Kara wani abu ce"
Kai Taj ya riƙe kawai. Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai. Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu. Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala.
"Kan ne dai?" Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi.