Sashe 14
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Magana ce ta gaskiya. Kin goyi bayan miji kun mayar da yaro marayan ƙarfi da yaji. Yau ko ɗan kafin Fatiha ya kawo muku gida wannan hukuncin ya yi tsauri, balle girki. Mene ne aibun girkin nan ne? Har mamakin ki nake yi idan kina sha'anin gidan nan kamar babu abin da yake faruwa."
"Jamila ya isa haka don Allah. Na tabbata tana da dalilinta na yin duk abin da tayi tunda ita tayi naƙudar Taj. Ta fi mu son sa." Hajiya ma ta gwaɓa tata maganar.
Kukan Inna ya sake tsananta da wannan rashin fahimta da abokan zamanta su ka yi mata. Ita fa tun lokacin da taga auren Mama yana girgiɗi a dalilin Taj hankalinta ya yi mugun tashi. Balle da aka zo sulhun nan ta fahimci ashe su Hajiya ma dake gidan sun daina girki. Wannan dalilin yasa ta sauke dukkanin tijarar da ta tanadarwa Alhaji. Domin tana da tabbacin muddin ya sallameta akan Taj su ma za su gwada masa rashin goyon baya. Ƙarshenta cikin fushi aurensu ya sami matsala. Indai ba butulci ba kuwa irin zaman da su ke yi a gidan bata jin ya kamata ta yi musu sakayya irin wannan.
Zafin da taga sun É—auka ne ya bats damar yi musu wancan bayani yadda za su fahimceta.
"Kuna ganin rayuwar Taj za ta yi albarka idan sanadinsa gidan nan ya wargaje? Fushi irin na Alhaji nayi imanin sallamarmu duka lokaci guda ba zai yi masa wahala ba. Sai dai ya yi nadama daga baya. Sannan gabaÉ—aya yaran gidan nan da wuya su sake yiwa É—an uwansu kallon mutumci. Da farin gashinmu a ka ace muna zawarci."
Allah Sarki. Tana rufe baki Umma ta rungumota.
"Ki yi haƙuri Abullen Alh. Hayatu. Shaiɗan yaso amfani da ɓacin raina ya haddasa mana fitina."
"Sunan da ki ka kira ni dashi na mene ne kuma?"
"Na ƙaunar rigimammen tsohon nan mana."
Dariya su ka ji an kwashe da ita. Shaf sun manta da ƴaƴansu dake wajen a tsaye. Kowa da jan ido an sha kuka suke dariyar daidaitawar iyayen nasu. Da wannan kuma babbar ƴar gidan Yaya Bintu ta sanar da ƴan uwanta cewa babu masifa da za su bari ta shiga gidan sama da rabuwar kawunansu. Don haka kowa ya shirya abin da zai iya domin taimakawa Taj. Haɗin kansu kaɗai zai iya sassautawa mahaifinsu haƙƙin ɗansa da yake ɗauka.
Zaman lafiya aka ce yafi zama ɗan sarki. Alhaji bai san cewa duk cikim alkhairansa na duniya yadda ya gina gidansa shi ne mafi girman arziƙinsa ba. Gashi yana neman ɓata abin sa da hannunsa.
Motar Ahmad su ka shiga ya kaisu gidansa. Sai ga Taj ya manta da dukkanin damuwarsa da ya ganshi tsakanin uwayensa.
***
Abba ya maimaita zancen da yaji daga Vice Principal yafi a ƙirga a zuciyarsa bayan sun gama waya. Abin ne bambarakwai wai namiji da suna Hajara. Ta yaya ma za a ce Hamdi tayi dambe har ta kai rashin zuwansa akan matsalar zai iya jawo mata kora? Hamdi ce fa. Yarinyar da ko a cikin ƴan uwanta lokacin ƙuruciya da wuya a kawo ƙararta.
Damuwar da su ke ciki shi da Yaya akan matsalar tashinsa da aka yi daga wurin sana'a sai ta zama ba komai ba. Fatan wayewar gari kawai yake domin yaje ya ji me yake faruwa. Sai dai kuma hantsi na soma leƙowa yaji wani irin tashin hankali. Da hankalinsa ya riga ya san yadda yaran ke kunyar nuna shi musamman ita Hamdi. Shin za ta yi maraba da amsa kiran nasa ko kuwa?
RAYUWA DA GIÆI 8
Batul Mamman💖
***
Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta.
"Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?"
Kai a ƙasa ta ce "eh."
"Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?"
Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma taƙi magana me zai sa ta fara?
Rai a ɓace ya ce "To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ƙarshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki."
Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman saƙe-saƙen neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar ɗin da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaɗin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. Haɗuwarta da Baba Maje gobe ba ƙaramar tarzoma zai tayar ba.
"Ki tashi ki fice min daga office nace."
Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta miƙe za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP ɗin tsoro da shakku akanta.
Wurin ƙawarta konace babbar ƴar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment ɗin na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banɗakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi.
Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arziƙi bata yiwa ciwon dake babban yatsan Widad na ƙafa wanda taji a wurin faɗan ɗazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba.
"Bani wayarki in kira Uncle B"
"Kuna can aka zo inspection É—in bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga É—akin nan tafi ashirin."
Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata "banza, me yasa ko a pant baki ɓoye ba?"
"Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching ɗinmu da ɗai-ɗai." Widad ta amsa tana mai ɓoye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata.
Plan É—inta na farko ya faÉ—i tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faÉ—awa sugar daddy É—in nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta É—auka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can.
***
A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ƙaninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ƴaƴansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya.
"Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arziƙi ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne."
Bai manta yadda ya murguÉ—a baki bayan wucewar Alh. Hayatu ba. Ya doka cinya harda tofar da yawu.
"Aniyarka ta bika. Sa idawa, ana ruwa kuna ƙirgawa." Ya nuna ƙafarsa "wannan sayyara da Allah Ya bani babu inda ba za ta shiga ba sha Allahu."
Ga ire iren ranakun sun zo. Ina ma ana mayar da hannun agogo baya. Da ya juya lokaci ya canja komai banda auren Jinjin. Matar da ta rufa masa asiri ta kuma bashi Æ´aÆ´a mafi soyuwa a gare shi.
Gaisawa su ka yi da ƙanin nasa da girmamawa sannan ya faɗa masa halin da yake ciki a kunyace.
"Wallahi Yaya Habibu ka ganni a asibiti wani maƙocina ne babu lafiya. Daga shi sai matarsa ga yara ƙananu ta taho dasu. Basu da kowa a nan sai mu maƙota. Yanzu haka yayansa dake Zaria yana hanya. Tun asuba nake nan."
"Ahhh, yi zamanka Abdulƙadir. Bari kawai naje."
"Ka daina ɓoye kanka daga rayuwar yaran nan. Yau in dukkaninmu babu sai kai kaɗai shikenan sai ace zuri'armu basu da uba saboda abin da ya wuce?"
Yayi maganar ne saboda ya saba ji daga yaransa cewa ƴaƴan yayan nasa suna kunyar alaƙarsu da shi. Bai ga laifinsu ba Fisabilillah. Amma kuma Allah da Ya haɗa alaƙar Shi Ya san yadda zai tafiyar da al'amura. Tayasu ɓoye kansa ba dabara bace tunda duk lalacewa da uba ake ado.
Abba bai sake neman kowa ba ya tafi makarantar. Anyi sa'a yau shadda ya sanya ruwan madara, riga da wando harda hula. Da ya shiga makarantar bayan tafiyar minti arba'in tafiyarsa ya fara ƙoƙarin gyarawa. Sannan da zai tambayi masu gadi ofishin principal ya daddage ya kumbura murya. Amma kunne da idanu masu lafiya babu yadda za ayi su kasa fahimtar me ake son ɓoye musu. Basu dai nuna a fuska ba guda ya nuna masa hanyar office ɗin. A can gefe inda ake ajiye motoci ya ga wata kamar ta Baba Maje. Amma da yake baya tare da nutsuwa bai tsaya ƙare mata kallo ba.