Sashe 41
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta." Ya haɗe rai "Habibu, na baka wata uku ka kashe auren nan. Cire zuri'arka daga jikina shi ne kaɗai abin da zai sa na dawo da Taj gidana. In har da gaske ka damu da shi ba za ka bari rayuwarsa ta ƙare a bin gidan ƴan uwa idan yana son ganawa da mahaifiyarsa ba."
Duk dauriya sai da yaji ƙwalla na neman zubo masa.
"Me yasa ka yarda aka yi auren?"
"Saboda banga alamun idan naƙi zai haƙura ba. Ka riga kayi tasirin da maganarka tafi tawa a wajensa. Zai iya yin komai domin fitar da kai kunya a yadda ya zo min."
Gumi sosai Abba ya dinga yi. Allah Ya sani yafi jin Yaya akan Hamdi. Wannan tsananin farincikin da ta shiga idan ya koma baƙinciki kamar ba za ta iya ɗauka ba. Mutane da yawa za su yi musu dariya. Wadda za ta fi yi mata ciwo kuwa ta ƴan uwanta da su ka haɗa uba ce da ta mahaifin nata da har yanzu yake aibata halittarta da aurenta da đan daudu.
Ya sake kallon Alhaji sai dai babu wata fuska ta yin magana. Magana ɗaya Alhajin ya ƙara yi masa kafin ya koma ciki.
"Ina fata za ka nuna dattako ka riƙe maganar nan tsakaninmu. Dabarar kashe auren tana hannunka. Ni dai kawai nan da wata uku magana ta ƙare."
"In sha Allahu."
Jikinsa rawa ya dinga yi shi yasa ya kasa komawa motar har sai da Taj ya fito. Kafin ya ƙaraso Abba ya yi composing kansa.
"Yau dai na shanyaka da yawa. Muje kada dare ya ƙara yi."
Kasa haƙuri yayi ya tambaye shi "Babu matsala ko Abba? Me ya ce maka?"
"Ban sanka da haka ba Taj. Tattaunawa ce dai ta yaushe gamo da kuma rashin jindaɗinsa da bamu tuntuɓe shi da maganar auren ba sai a makare."
Kallon rashin yarda Taj ya yi masa. Sai dai Abban ya toshe duk wata ƙofar da zai fahimci matsalar. Sun kama hanya za su koma motar Taj yaji Kamal na kiransa. Da ya juya sai yaga Inna tare da Kamal ɗin.
Fuskarsa ta haskaka da wani irin annuri. Ya ce da Abba "Innata ce."
Kamal juyawa ya yi bai biyota ba. Ta ƙarasa kusa da gate ɗin. Idanunta cike da ƙwalla. Taj kuwa tuni ya yi laushi don ya kwana biyu sai dai su gaisa a waya.
"Baki kwanta ba?"
"Ina fa. Ina ta fakon shigowar Alhaji ne idan kun gama." Sai kuma tayi murmushi "ango ka sha ƙamshi."
Dariya ya yi ya rungumo kafaÉ—arta. Ba shiri ta ruÉ—e tana fama ture shi gami da waigawa don kada a gansu.
"Ga Abba...surukinki."
Abinka da sabo. Ƙasa ya yi zai gaisheta.
"Subhanallahi. Haba don Allah. Tashi mu gaisa. Ai mun zama đaya kuma."
Duk da bata so amma a mutumce su ka gaishe da juna. Yana ta bata girma.
"Da farko zan fara da baka haƙuri don nayi imanin ko me Alhaji ya faɗa maka ba mai daɗi bane. Sannan don Allah kada ka wahalar da kanka wajen yiwa ƴata komai. Tunda ka iya bawa yaron nan ƴarka in sha Allahu ba zan bari ta kuka da komai ba. Nagode da karamcinka a garemu."
"Ikon Allah. Hajiya ai nine da godiya da Taj bai ƙyamaci zuri'ata ba."
"Wanda ya baka ƴa ai ya gama maka komai." Ta faɗi tana murmushi "idan babu damuwa ina son ya kawo mana ita cikin sati mai zuwa. Zan karɓi numbar mamanta mu yi magana kafin na zo. Ka san Alhajin naku sai da lallaɓawa."
Murmushi ya yi shi ma "kada ki damu. Hamdi ƴarki ce kuma ikonki. Ina ƙara godiya."
Taj ma godiyar ya yi mata. Abba ya dubi uwa da É—an su ka bashi tausayi. Me yafi wannan ciwo ace uwa tana son ganin É—anta amma sai dai ta saci hanya ta fito kamar mai laifi? Dole zai san yadda ya yi da Yaya da Hamdi a raba auren cikin lumana.
***
Har ƙofar gida Taj ya kai Abba. Su ka yi sallama ta girmamawa. Taj yana ta sake tambayarsa ko babu matsala game da ziyarar da su ka kaiwa Alhaji. Shi kuma ya tabbatar masa babu komai.
"Gobe in sha Allahu zan tafi Abuja. Idan komai ya tafi yadda nake so ba zan wuce kwana biyu ba in sha Allahu."
"Kada ka damu. Happy Taj zai tafi kamar kana nan da yardar Allah."
"Ba manufata ba kenan" Taj ya faɗi yana sosa ƙeya "dama akan ..."
Gira Abba ya É—age gira "matarka ko? In turo ta ku yi sallama ne?"
Da sauri Taj ya koma mota yana ta dariya shi ma Abban ita yake yi. Da gangan dama ya yi tsokanar don kawai ya kawar da damuwar da yake gani a tattare da shi tun a gidansu.
Hamdi na jin shigowar Abba ta leƙo yi masa sannu da zuwa. Ya kalleta ya kalli Yaya da ita ma fitowar tayi da sauri.
"Suruka da matar Taj jiran me kuke yi min ne?"
"Jin inda magana ta kwana mana." Cewar Yaya.
Ita kuwa Hamdi wayancewa tayi ta gudu. ÆŠakinsu ta koma amma akwai mutane. Sai ta zaga bayan gidan amma bata yi nisa ba. Ta zauna akan wani bulo ko tsoro bata ji ta kira Taj.
Murmushi ya yi da call ɗin nata ya shigo. Ko tada motar bai yi ba don ya tsaya duba wani saƙo a waya. Ya bari sai da ta gama ringing sannan ya kirata.
"Za mu iya magana yanzu?" Ta furta a hankali bayan ta kuma gaishe shi.
"Yes."
Raba kanta tayi da dogon tunani ta faÉ—i abin da ya kamata duk da ba shi bane ranta yake so.
"Dama cewa nayi tunda Ya Sajida tayi aure namu ba dole bane ko? Kada ka takura kanka saboda gidanmu."
Kamar bai fahimceta ba ya ce "Ban gane ba. Wani abin ne ya faru?"
"Uhmmmm. Dama wai ko za ka sakeni" tayi saurin ƙarawa da "tunda ba sona kake ba. In aka ce dole ka zauna dani za a shiga haƙƙinka. Kaga kuma hakan bai dace ba. Ace mun takura maka ta wannan hanyar bayan duk irin taimakon da kake yi mana."
Wannan yarinya da abin dariya take ya ayyana a zuci. Ji yadda take zuba zance kamar wadda ake karantowa.
Ita kuma kasa jurewa shirun nasa tayi ta ce "Baka ce komai ba."
"To me zan ce? Naga kin gama yanke hukunci ke kaÉ—ai."
Haƙuri tayi saurin bashi. Sam bata so ta ɓata masa rai kada ya yi amfani da hakan a kanta.
"Wai dama tunda ba so ka ke ba..."
"Ni yaushe mu ka yi maganar nan dake har nace bana so?"
Gabanta ne ya faɗi. Kada fa yaƙi amincewa.
"Rannan É—in nannnn. Ka tuna? Da nayi maka rashin kunya ka ce ai ba sona kake baaa." Ta marairaice masa.
"Anya kuwa nine? Ban tuna ba Hamdi." Ya danne dariyar da yake son yi.
"Allah kuwa ba ƙarya nake ba."
Muryarta yaji ta fara rawa.
"Yanzu dai so kike a raba auren?"
"Eh."
"Amma bai yi wuri ba? Kada sunanki ya ɓaci a gari."
"Kaga bamu zauna tare ba. Ko mun rabu babu mai cewa don nayi wani abu ne. Za ma a fahimta sosai."
"Tun yaushe ki ka fara wannan tunanin?"
Hamdi ta fara murnar jin muryarsa a sake.
"Tun yamma. Wallahi har ciwon kai da zazzaɓi sai da su ka kamani saboda neman mafita...au...saboda nema maka mafita. Bana son mutum ya takura saboda ni."
'Zan yi maganinki'
Lokaci ya duba a wayarsa. Tara da arba'in da biyu.
"Yaya jikin naki? In ba a rufe muku gida ba ki É—an fito mana."
Sai kuma taji faÉ—uwar gaba "takardar za ka bani?"
"Ina jiranki" kawai ya ce.
Da sanɗa ta fito tayi sa'a ƙofar soronsu mai ƙara idan an turata a buɗe take har yanzu. Ƙofar gidan ta buɗe tana sako ƙafa su ka kusa karo da Taj. Baya tayi za ta faɗi ya yi saurin riƙo kafaɗunta. Ita da shi duka wani sabon al'amari ya baƙuncesu lokaci guda. Sai da ta daidaita tsayuwarta ya ce,
"Sannu."
Ta amsa da ka. Yawun bakinta ne a bushe. Tana tare da fargabar ko har ta saku. Bata yi aune ba taji hannun Taj a goshinta.
"Mene ne?"
"Zazzaɓin nake son ji. Da alama akwai saura. Zo mu je asibiti."
"Na'am?" Ta waro masa idanunta.
Wayarsa ya É—ago "bari na kira Abba na faÉ—a masa za mu fita."
"Dani É—in?" Ta ce a gigice. Idanunta sun soma raina fata.
"Idan dare ya ƙara yi kafin mu dawo sai su rufe gidan kawai. Sai mu wuce gida mu kwana."
Hanjin cikinta ya wani cure waje guda don tsoro "Wai da ni?"
"Kada ki damu. Zai fahimta. Mata ta ce so babu wani abu" ya bata amsa kai tsaye.
"Don Allah kayi haƙuri."
"Ban yi wasa da ciwon wanda bashi da kusanci dani ba ballantana kuma naki."
"Na warke tun da rana."
Taj ya ƙanƙance ido "ki ka ce kuma da yamma."
Da sauri ta ce "Eh, da yamman nake nufi. Kafin rana tayi sanyi."
"Hamdiyya kenan. In tambayeki mana."
"Ina ji."
"Kina so na?"
Tsareta yayi da kallo. Ta sunkuyar da kai.
"Kada ki cuci kanki. Da amsarki zan yi amfani."
"Ba za ka ji haushi ba?"
Taj ya yi murmushi "ko kusa."
"Zan fi so mu rabu."
"Ban yi miki ba kenan?"
Yau acting kamar daraktan kannywood ya bata training, ta marairaice masa.
"A'a, ba haka nake nufi ba. Naga kamar bamu dace ba. Ka fi ƙarfin ƴar talakawa iri na."
"Zan sanar da Abba duk yadda mu ka yi...."
"Wane Abban? Nawa?" Ta É—aga murya fiye da yadda ta soma magana saboda tsoro.
"Kinsan ina girmama shi sosai. Ba zan yi komai ba tare da shawartarsa ba."
Ganin zai ɓallo mata ruwa ba shiri ta ce "to a bar zancen nan don Allah."
"Kin fasa karɓar takardar?"
Ta sha kunu "na fasa."
"Za mu je asibitin?" Ya kanne mata ido.
MurguÉ—a masa baki tayi "na ma zama abar tsokana ko?"
Ya rasa me yasa komai tayi yake burge shi. Wannan tsiwar ma da ba don dare ba da zai yi ta zurma ta ne tana yi masa.
"Gobe zan yi tafiya. Ki min addu'a don Allah."